An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 25 November 2015 19:06

Jagora Juyin Juya Hali Ya Fayyace Aniyar Iran Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Al'ummar Palasdinu

Jagora Juyin Juya Hali Ya Fayyace Aniyar Iran Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Al'ummar Palasdinu
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa; Iran zata ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Palasdinu da dukkanin karfinta tare da kare musu hakkoki.

 

A ganawarsa da manyan jami’ai da kwamandojin dakarun sa-kai na Basij a yau Laraba: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khameine’i ya bayyana cewa; Makiya suna kokarin ganin sun shafe sunan al’ummar Palasdinu tare da kawo karshen gwagwarmayarsu amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana nan a kan aniyarta ta ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa da dukkanin karfinta.

Jagoran juyin juya halin na Musuluncin ya kuma jaddada cewa; Kasar Amurka ta bayyana a fili cewa ita ce kan gaba a sahun manyan kasashe masu girman kai a duniya. Jagoran yana mai fayyace cewa; Jami’an Amurka suna tarbar mutum da dukkanin murmushi amma nan take zasu koma suna cin dunduniyarsa.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya fayyace cewa; Matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fili yake kan al’amura da dama da suke faruwa a duniya musamman a yankin gabas ta tsakiya kuma matsayi ne da ya yi daidai da ma’auni na hankali misali kan matsalar Palasdinu, Bahrain, Yamen, Siriya da Iraki.

Add comment


Security code
Refresh