An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 25 November 2015 13:20

Jagoran Juyin Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Gana Da Firayi Ministan Algeriya

Jagoran Juyin Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Gana Da Firayi Ministan Algeriya
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya gana da Firayi ministan harkokin wajen kasar Algeriya Abdulmalik Salal.

 

A yayin ganawar jagoran juyin juya halin muslunci ya jinjina wa gwamnati da kuma al’ummar kasar Algeriya, dangane da yadda suke tsayawa kan manufofinsu ba tare da zama ‘yan amshin shata ga kasashen yammacin turai ba, wanda kuma kasar Algeriya na daya daga cikin kasashen arewacin Afirka da ake buga misali da su wajen gwagwarmaya domin kin amincewa da mulkin makkala.

Jagoran ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a kafa kwamiti domin gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tsakanin Iran da Algeriya da za su shafi bangare tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Shi ma a nasa bangare Firayi ministan kasar Algeriya Abdulmalik Salal ya bayyana matukar gamsuwarsa dangane da yadda ganawar takasance inda ya ce ta yi armashi matuka.

Add comment


Security code
Refresh