An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 20 March 2015 05:23

Al'ummar Venezuela Sun Shigo Da Wani Shirin Fada Da Makircin Amurka

Al'ummar Venezuela Sun Shigo Da Wani Shirin Fada Da Makircin Amurka
Al’ummar kasar Venezuela sun kaddamar da wani shiri na tara sanya hannun mutane miliyan goma na kasar don nuna goyon bayansu ga shugaban kasar da kuma yin Allah wadai da kulle-kulle da matsin lambar da Amurka take yi wa kasar.

 

 

Shi dai wannan shiri wanda magoya bayan shugaban kasar Nicolas Maduro suka kirkiro shi ya biyo bayan wata sabuwar siyasa ce da gwamnatin Amurka ta shigo da shi bayan da shugaban kasar Barack Obama ya sanya hannu kan wata doka a ranar 9 ga watan Maris din nan inda aka bayyana kasar Venezuelan a matsayin babbar barazana ga tsaron kasar Amurka.

 

A bisa wannan dokar ce Amurka ta dora takunkumi da rufe asusun ajiya da kaddarorin wasu jami’an kasar Venezuelan da suka hada da tsohon shugaban dakarun kare kasa Antonio Benavides, shugaban hukumar leken asiri Gustavo Gozales da kuma sufeto janar na ‘yan sandan Venezuelan Manuel Perez da kuma hana su shiga Amurka.

 

Shugabannin kasashe daban-daban na Latin Amurkan sun yi Allah wadai da wannan matsaya ta Amurka.

Add comment


Security code
Refresh