An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 19 March 2015 18:06

Amnesty International Ta Yi Galgadin Gurbatar Yanayi A Najeriya

Amnesty International Ta Yi Galgadin Gurbatar Yanayi A Najeriya
Kungiyar Afuwa ta duniya ta yi galgadin samun gurbatar yanayi a Najeriya sakamakon dattin Men fetur da kamfanonin Man masu hako Man ke zubarwa. Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa a yau Alkhamis kungiyar Afuwa ta duniya wato Amnesty International ta fitar da rahoto dangane da gurbatar yanayi a Najeriya inda ta ce a shekara ta 2014 da ta gabata sun samu rahoton gurbatar yanayi sakammakon dattin Man fetur da manyan kamfanonin Shell da Eni ke zuburwa har na gurare 553, kuma wannan barazana ce ga lafiyar  milyoyin Al’ummar dake zaune a yankin.

 

Babban daraktan kungiyar Amnesty International ya bayyana cewa kamfanin Eni  ya kasa sosai wajen kula da aiyukan sa a yankin Nijer-delta, shi kuma kamfanin Shell, duk da irin alkawalukan da ya dauka, babu wani abin a zo a gani da yayi domin kare gurabatar yanayi a Najeriyan.

Kungiyar ta ce daga shekara ta 1971 zuwa 2011 gurare 10 kacal aka samu na gurbatar yanayi a kasashen turai.

Tarayyar Najeriya ita ce babbar kasa dake ta fi ko wata kasa fitar da danyan Man fetur a Nahiyar Afirka.

Add comment


Security code
Refresh