An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 19 March 2015 18:02

Banki Moon Yayi Jawabin Barka Da Salla Sanadiyar Gabatowar Sallar Nooruz

Banki Moon Yayi Jawabin Barka Da Salla Sanadiyar Gabatowar Sallar Nooruz
Babban saktaren Majalisar dinkin duniya Banki Moon ya yi jawabin barka da salla ga Masu magana da yaran Farisanci dangane da gabatawar sallar Noruz. Kamfanin dillancin Labarai na Mihr ya habarta cewa a yau Alkhamis babban saktaren MDD Banki Moon ya yi jawabin barka da salla game da ranar duniya ta Noruz wacce tayi daidai da ranar 21 ga Maris, Banki Moon ya ce sallar Noruz wata babba dama ce ta tattaunawa da fahimtar al’adun al’umar duniya daban-daban tare da mutunta juna.

 

Banki Moon ya kara da cewa sallar Noruz salla ce ta hadin kai da mutunta juna a ciki da wajen Al’umma masu amfani da harshen farisanci, a wadannan ranaiku masu wannan yare suna haduwa guri guda domin kara dankon zumunci da kuma girmama juna a tsakaninsu domin haka ne ya ce zai yi amfani da wannan dama ga Al’ummar yankin su bada hadin kai ga Majalisar dinkin Duniya domin tabbatar da sulhu a wannan shekara ta 2015

Add comment


Security code
Refresh