An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 15 March 2015 19:15

Amurka:John Kery Wajibi Ne Mu Tattauna Da Shugaban Siriya Bashard Al-Asad

Amurka:John Kery Wajibi Ne Mu Tattauna Da Shugaban Siriya Bashard Al-Asad
Babban saktaren harakokin wajen Amurka John Kery ya ce wajibi ne su tattauna da Bashar Al-asad shugaban kasar Siriya domin kawo karshen yaki da kasar ta Siriya Tashar telbijin ta Press Tv wacce ke watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto john kery yayin da yake hira da tashar telbijin ta CBS na cewa, wajibi magabatan watsinton su tattuna da shugaban kasar Siriya Bashar Al-asad domin kawo karshen yakin da kasar ta kwashe kusan shekaru 5  tana fama da shi.

 

Firicin baya-bayan nan na shugaban kungiyar leken asirin ta kasar Amurka Jean Bermand na nuni da cewa magabatan na Amurka sun canza matsayarsu ta siyasa dangane da kasar ta Siriya

Mr Jean Bermand shugaban kungiyar CIA ya ce nan gaba za su tattauna dangane da zaman Bashard Al-asad a kan karagar milkin kasar Siriya na tsahon shekaru biyu.

A nasu bangare ‘yan adawar na Siriya ta bakin Basam Almalik sun ce a watan avrilun mai kamawa za gudanar da taro a birnin Alkahirar Masar inda za su tattauna kan batun ci gaba da zaman Al-asad na tsahon shekaru biyu a kan karagar milkin kasar.

Add comment


Security code
Refresh