An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 25 February 2015 07:54

Amurka:A Kwai Yuyuwar Sake Kakabawa Kasar Rasha Takunkumi

Amurka:A Kwai Yuyuwar Sake Kakabawa Kasar Rasha Takunkumi
Amurka tayi barazanar sake kakabawa kasar Rasha sabin takunkumi. Saktaren harakokin wajen Amurka Jon Kery ya ce a kwai yiyuwar sake kakabawa Rasha sabin takunkumi a 'yan kwanaki masu zuwa, bayan gudanar da bincike kan yadda yarjejjeniyar tsakaita wuta tsakanin 'yan awaren kasar Ukrene masu samun goyon bayan Rasha da kuma Gwamnatin Ukrene da ta ke samun goyon bayan Amurka da kasashen Turai ta gudana.

 

yayin da yake jawabi a gaban kwamiti mai kula da harakokin waje na Sanatocin Amurka, Kery ya kara da cewa ma'aikatarsa na ci gaba da bincike dangane da yadda yarjejjeniyar Munesk ta gudana, matukar aka gwano shigar Sojin Rasha a rikicin na gabacin Ukren, ba shakka za su sake kakabawa Rashan sabin takunkumi.

 har ila yau Kery ya karyata ikrarin da magabatan Rasha su kayi na cewa babu sojojin su a cikin mayakan 'yan awaren na gabacin kasar ta Ukrene.

Add comment


Security code
Refresh