An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 23 February 2015 11:16

Amurka:An Kafa Kungiyar ISIS Saboda Ta Tunkari Kungiyar Hizbullah Ta Labnon

Amurka:An Kafa Kungiyar ISIS Saboda Ta Tunkari Kungiyar Hizbullah Ta Labnon
Jami’in tsaron Amurka ya ce manufar kirkiro Kungiyar ta’addanci ta ISIS rusa kungiyar Hizbul..ta kasar Labnon. Janar Wislin Carlin ya ce Gwamnatin washiton da kawayenta sune suka kirkiro Kungiyar ta’addanci ta ISIS na nufin kawo karshen kungiyar gwagwarmaya Hizbul…..ta kasar Labnon.

 

Yayin da yake hira ta tashar Telbijin CNN ta kasar Amurka, Janar Carlin ya ce ba shakka kasar Amurka ce ta kirkiro kungiyar ISIS kuma sun kashe milyoyin dalas ta hanyar tattara matasa masu tsananin kishin Islama a Duniya , inda suka yi amfani da wasu kasashe kawayensu na  larabawa.

Janar Carlin ya kara da cewa kasar Amurka ta kashe kudade masu dinbin yawa wajen horas da ‘yan ta’adda da kuma siya masu makamai tare da turasu kasar Siriya, kuma dukka wannan an yi shine da nufin kawar da kungiyar gwagwarmayar Hizbul…ta kasar Labnon.

Add comment


Security code
Refresh