An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 13 February 2015 05:03

Mutanen Venezuela Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati

Mutanen Venezuela Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati
Rahotanni daga kasar Venezuela sun bayyana cewar dubun dubatan mutanen kasar ne suka gudanar da wata zanga-zanga a babban birnin kasar, Caracas, don nuna goyon bayansu ga gwamnatin kasar.

 

 

Rahotannin sun ce masu zanga-zangar wadanda suke dauke da hotunan shugaban kasar Nicolas Maduro sun ce sun fito ne don nuna goyon bayansu gare shi da kuma gwamnatinsa daga abin da suka kira irin makirce-makircen da ake kulla wa gwamnatin da nufin ganin bayanta.

 

Gwamnatin Venezuelan dai tana zargin wasu ‘yan kasuwa da wasu ‘yan siyasa a kasar da aiwatar da siyasar wasu kasashe ciki kuwa har da Amurka na yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasar ta Venezuela da nufin sanya mutane su yi wa gwamnatin bore.

 

Cikin ‘yan watannin baya-bayan nan an sami koma baya cikin tattalin arzikin kasar ta Venezuela sakamakon faduwar farashin man fetur da kuma sauran ayyukan zagon kasa da gwamnatin take fuskanta, sai dai kuma har ya zuwa yanzu mafi yawan al’ummar kasar suna goyon bayan gwamnatin shugaba Nicolas Maduron.

Add comment


Security code
Refresh