An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 11 February 2015 05:37

Ana Ci Gaba Da Kara Samun Wagegiyar Baraka A Tsakanin Netanyahu Da Obama

Ana Ci Gaba Da Kara Samun Wagegiyar Baraka A Tsakanin Netanyahu Da Obama
Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa akwai sabani babba a tsakaninsa da shugaban kasar Amurka Barack Obama dangane da shirin Iran na makamashin nukiliya.

 

A cikin wani bayaninsa wanda ofishinsa ya fitar a jiya, Netanyahu ya bayyana cewa akwai sabanin mahanga tsakaninsa da Amurka da sauran kasashen yammacin turai da suke gudanar da tattaunawa kan shirin Iran na makamashin nukiliya, domin suna son su cimma matsaya tare da Iran da za ta halastawa Iran yin amfani da fasahar nukiliya, yayin da Isra'ila ke kallon hakan a matsayin babban hadari ga samuwarta.

 

A ranar 3 ga watan gobe Benjamin Netanyahu zai gabatar da wani jawabi a gaban majalisar dokokin Amurka dangane da shirin Iran na nukiliya, bayan da 'yan majalisar daga jam'iyyar Repulican suka aike masa da goron gayyata kan hakan, yayin da shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya nuna rashin gamsuwarsa da wannan mataki, inda ya sha alwashin cewa ba zai gana da Netanyahu ba a wannan ziyara, yayin da wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Amurka daga bangaren jam'iyyar Democrat mai mulki, suka sha alwashin kin halartar zaman majalisar a wannan ranar.

 

 

 

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh