An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 04 February 2015 12:19

Wasu 'Yan Majalisar Amurka Za Su Kaurace Wa Jawabin Netanyahu

Wasu 'Yan Majalisar Amurka Za Su Kaurace Wa Jawabin Netanyahu
Wani adadi mai yawa na ‘yan majalisar Amurka sun yi barazanar kauracewa jawabin da aka shirya firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu zai yi a majalisar a mako mai zuwa kan kasar Iran don nuna rashin amincewarsu da ziyarar tasa.

 

 

Rahotanni daga Amurkan sun ce wasu ‘yan majalisar musamman ‘yan jam’iyyar Democrats sun yi barazanar kauracewa jawabin da aka tsara Netanyahun zai yi a ranar 3 ga watan Maris mai kamawa.

 

A watan da ya wuce ne kakakin majalisar wakilan Amurkan John Boehner ya gayyacin Netanyahun da ya gabatar da jawabi a gaban majalisar kan batun sake sanya wa Iran takunkumi lamarin da fadar White House ta Amurkan ta nuna rashin amincewarta tana mai cewa hakan yana iya cutar da tattaunawar da ta ke yi da Iran kan shirin nukiliyanta.

 

Shugaban Amurkan Barack Obama ya ce ba zai gana da Netanyahun ba a yayin wannan ziyarar tasa don nuna fushinsa da ziyarar.

Add comment


Security code
Refresh