An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 17 January 2015 06:47

Amurka Ta Soki Masu Zanga-Zangar Allah Wadai Da Charlie Hebdo

Amurka Ta Soki Masu Zanga-Zangar Allah Wadai Da Charlie Hebdo
A wani abu da wasu suka fassara shi a matsayin munafunci da kuma goyon bayan bangare guda, gwamnatin Amurka ta yi kakkausar suka ga ci gaba da zanga-zangar da al’ummar musulmi suke yi a kasashe daban-daban na duniya don nuna rashin jin dadinsu ga zanen batanci ga Ma’aikin Allah (s.a.w.a) da jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta yi.

 

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jeffrey Rathke yayi wannan sukar a lokacin da yake magana kan yamutsin da aka yi a yayin irin wadannan zanga-zangogi a kasashen Nijar da Pakistan inda ya ce babu wani dalili da zai sa a nuna tashin hankali saboda wani aiki na jarida ko da kuwa wasu suna ganin hakan a matsayin batanci a gare su.

 

Kakakin ma’aikatar wajen Amurkan ya kara da cewa: muna kiran da a guji tada hankali da kuma girmama doka. Sai dai kuma jami’in na Amurka bai yi komai kashin ishara ko nuna fushi da wannan zane na batanci da ya sosa zukatan miliyoyin al’ummar musulmi ba.

 

Baya ga rikicin da ya barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Nijar, har ila yau a kasar Pakistan ma jami’an tsaron kasar sun raunana wani adadi na masu zanga-zangar a birnin Karachi a lokacin da suke yi kokarin isa ga karamin ofishin jakadancin Faransa da ke birnin.

 

A kasar Senegal da Mauritaniya ma masu zanga-zangar sun kona tutar kasar Faransa, don nuna rashin jin dadinsu da wannan danyen aikin.

Add comment


Security code
Refresh