An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 12 April 2016 17:35

Jagora Ya Ja Kunnen Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Ta'addanci Da Wasunsu Suke Yi

Jagora Ya Ja Kunnen Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Ta'addanci Da Wasunsu Suke Yi
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunnen wasu kasashen turai dangane da irin goyon bayan ayyukan ta'addanci da tsaurin ra'ayi da suke yi wanda ya ce a halin yanzu shika ta fara komawa kan mashekiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da firayi ministan kasar Italiya Matteo Renzi wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan birnin Tehran inda ya bayyana cewar: Wasu daga cikin kasashen Turai sun kasance suna goyon bayan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi da amfani da karfi wajen cimma manufofinsu, to amma a halin yanzu wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda sun fara kai hare-hare Turai din.

Ayatullah Khamenei ya bayyana taimakon kudade da kuma makamai da Amurka take ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda a matsayin babbar abin da ke kafar ungulu ga kokarin da ake yi na kawar da ta'addanci a duniya inda ya ce: Akwai karfafan dalilai da suke tabbatar da irin taimakon da Amurka take ba wa kungiyar Da'esh (ISIS) da sauran kungiyoyin ta'addanci. Duk da cewa a halin yanzu ma sun kirkiro abin da suka kira hadin gwiwan fada ta da kungiyar Da'esh, to amma duk da haka wasu cibiyoyin Amurkan suna taimakon kungiyar ta Da'esh ta hanyoyi daban daban.

Jagoran ya bayyana cewar Iran da kasar Italiya za su iya hada kai wajen fada da ta'addanci.

A yau Talata ce firayi ministan kasar Italiyan Matteo Renzi ya kawo ziyarar aiki nan Iran don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma bin sahun yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a kwanakin baya a lokacin da shugaba Ruhani ya kai ziyara kasar Italiya.

Add comment


Security code
Refresh