An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 12 April 2016 10:04

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Bullar Masifar Cuta A Kasar Afrika Ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Bullar Masifar Cuta A Kasar Afrika Ta Tsakiya
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan bullar cututtuka a tsakanin kananan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sakamakon matsalar rashin abinci mai gina jiki da na harkar kiwon lafiya mai inganci a kasar.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana cewa; Matsalar rashin abinci mai gina jiki da bullar cututtuka da suka hada da cutar cizon soro wato maleriya, amai da gudawa, gurbatar yana yi da ke janyo rashin iska mai kyau da sauransu sun fi zama babbar barazana ga kananan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a kan matsalar tashe-tashen hankulan da suke ci gaba da addabar kasar.

Har ila yau Dujarric ya kara yin gargadi kan bullar yawaitar mutuwar kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, yana mai jaddada bukatar Majalisar Dinkin Duniya na samun tallafin kudade dalar Amurka miliyan 531 domin tallafawa jama'ar da suke cikin halin kaka-ni ka yi a Jamhuriyar AFrika ta Tsakiya.

Add comment


Security code
Refresh