An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 April 2016 10:15

Wasu Bama-Bamai Sun Tashi A Wasu Sassa Daban Daban Na Kasar Rasha

Wasu Bama-Bamai Sun Tashi A Wasu Sassa Daban Daban Na Kasar Rasha
Wasu bama-bamai har guda biyar sun tashi a sassa daban daban na kasar Rasha kuma uku daga cikinsu hare-hare ne na kunan bakin wake.

Majiyar watsa labarai ta Fars ta bada labarin cewa: Wasu jerin bama-bamai har uku sun tarwatse a sassa daban daban na kasar Rasha da suka hada da yankin Stavropol Krai da ke kudancin Rasha kusa da kan iyaka da kasar Georgia a yau Litinin.

Rahotonni sun bayyana cewa; Biyu daga cikin hare-haren sun ritsa ne da ofishin 'yan sanda da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Rasha, kuma wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa hare-haren na yau sun hada har da kunnan bakin wake ciki har da harin da aka kai ofishin 'yan sanda da ke yankin Stavropol Krai da ke yankin kudancin kasar. Sai dai har yanzu babu labarin irin hasarar rayukan da aka yi ko na dukiyoyi.

Add comment


Security code
Refresh