An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 09:15

Al'ummar Chadi Sun Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Duk Fadin Kasar

Al'ummar Chadi Sun Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Duk Fadin Kasar
A yau Lahadi ne al'ummar Chadi suke gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Idris Deby da wasu 'yan takara goma sha biyu daga jam'iyyun adawar kasar.

Kamfanin dillancin labaran Rauters ya watsa rahoton cewa: Tun a safiyar yau Lahadi ne Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Chadi ta sanar da bude rumfunan zabe a duk fadin kasar domin gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin 'yan takara 13 ciki har da shugaban kasar mai ci Idris Deby da ya kwashe tsawon shekaru 26 a kan karagar shugabancin kasar.

Hukumar zaben ta sanar da cewa: Mutane kimanin miliyan shida ne suka cancanci kada kuri'a a zaben shugaban kasar a yau Lahadi, inda a wannan karo jam'iyyun adawa suka amince da shiga takarar sabanin zaben shekara ta 2011, inda suka kauracewa zaben saboda zargin tafka magudi.

Idris Deby da ya shafe tsawon shekaru 26 a kan karagar shugabancin kasar Chadi tun bayan juyin mulkin da ya yi wa Husaini Habre a shekara ta 1990, a halin yanzu ma shi ake zaton zai lashe zaben shugabancin kasar.

Add comment


Security code
Refresh