An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 18:11

Brussels: Mohamed Abrini, Ya Tabbatar Cewa Shi Ne ''Mai Malafa''

Brussels: Mohamed Abrini, Ya Tabbatar Cewa Shi Ne ''Mai Malafa''
Rahotanni daga Belgium na cewa mutumin nan mai suna Mohammed Abrini da aka cafke jiya, ya tabbatar da cewa lalle shi ne "Mai Malafa", da ake zargi shi ne mutum na uku da bam dinsa ya ki tashi, a harin Brussels.

Kakakin ofishin shigar da kara na Belgium din ne ya sanar da hakan a wannan Asabar, inda ya ce bayan nunawa mutanen hoto bidiyo da aka dauka ran 22 ga watan jiya, Mohammed Abrini ya amsa cewa lalle shi ne a cikin mutanen da suka kai harin na filin jirgin Zaventem.

Kafin hakan dama hukumomin kasar ta Belgium sun tuhumi mutane hudu ciki har da Mohamed Abrini din, da hada kai da kungiyoyin 'yan ta'ada da kukma kisan ta'adanci.

Mohammed Abrini, dan shekaru 31 wanda dan asalin kasar Belgium din ne gami da Marocco, dama ana tuhumar sa da hannu a hare-hare watan Nuwamba bara da suka yi sanadin mutuwar mutane 130 a biranen Paris da Saint-Denis na kasar faransa.

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh