An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 10:23

Gwamnatin DR Congo Ta Yi Suka Kan Bayanin Kwamitin Tsaron MDD Kan Kasarta

Gwamnatin DR Congo Ta Yi Suka Kan Bayanin Kwamitin Tsaron MDD Kan Kasarta
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya zargi kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da kokarin kunna wutan rikici a kasarsa ta hanyar tunzura wasu al'ummar kasar.

A taron manema labarai da ya gudanar a jiya Juma'a: Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Raymond Tshibanda ya bayyana cewa; Bayanin da Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar na baya-bayan nan kan batun gudanar da zabuka a kasar lamari ne da ke matsayin tunzura al'umma da zai kai ga kunna wutan rikici da rashin zaman lafiya a kasar.

Tshibanda ya kara da cewa: Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba ta da wata mummunar manufa dangane da sanarwar da ta fitar cewa: Akwai yiyuwar jinkirta gudanar da zaben shugaban kasa saboda matsalar rashin kudade da samun tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa.

A bayanin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a makon da ya gabata ya jaddada wajabcin ganin mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun dauki matakin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Nubamban wannan shekara ta 2016 kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Add comment


Security code
Refresh