An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 16:42

Dakarun Iran Sun Yi Watsi Da Tayin John Kerry Na Tattaunawa Kan Makamai Masu Linzami Na Iran

Dakarun Iran Sun Yi Watsi Da Tayin John Kerry Na Tattaunawa Kan Makamai Masu Linzami Na Iran
Mukaddashin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Birgediya Janar Massoud Jazayeri yayi watsi da bukatar sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry na tattaunawa da Iran kan shirin makamanta masu linzami yana mai kiran ma'aikatar harkokin wajen na Iran da su mayar da masa da martani mai karfin gaske.

Janar Jazayeri ya bayyana hakan ne a yau din nan Juma'a a matsayin mayar da martani da kalaman John Kerry na cewa Amurka a shirye take ta sake bude wata tattaunawa da Iran kan shirin makamanta masu linzami inda ya ce: Mun sha fadin cewa, shirin makamai masu linzami na Iran suna daga cikin jajayen layukan da ba za ta taba ketare su ba, wadanda kuma ba za a taba tattaunawa kan su ba. Don kuwa Iran ba ta neman izini ko yardar wani wajen karfafa bangaren kariyar da take da shi.

Mukaddashin babban hafsan hafsoshin na Iran ya kara da cewa dakarun na Iran ba za su taba bari wani ya tsoma musu baki cikin wannan lamarin ba, sannan kuma za su gutsure hannun duk wani wanda yake shirin tsoma baki cikin wannan lamarin.

A saboda haka ne Janar Jazayeri ya kirayi ma'aikatar harkokin wajen na Iran da ta mayar da martani ga wannan kalamai na sakataren harkokin wajen Amurkan.

A jiya Alhamis ne dai sakataren harkokin wajen Amurkan John Kerry, bayan ganawar da yayi da takwarorinsa na kasashen larabawan Tekun Fasha ya bayyana cewar Amurka tana shirye ta zauna kan teburin tattaunawa da Iran kan shirin makamanta masu linzami.

Add comment


Security code
Refresh