An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 05:23

Kwamitin Tsaron MDD Ya Tsawaita Wa'adin Takunkumi Kan Kasar Sudan Ta Kudu

Kwamitin Tsaron MDD Ya Tsawaita Wa'adin Takunkumi Kan Kasar Sudan Ta Kudu
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kara tsawaita wa'adin takunkumin da ya kakaba kan kasar Sudan ta Kudu sakamakon yakin basasan da ya bulla a kasar tun a karshen shekara ta 2013.

A zaman da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar a jiya Laraba ya sanar da cewa; Har yanzu kasar Sudan ta Kudu tana fama da matsalolin tashe-tashen hankula tare da zama barazana ga tsaro da zaman lafiyan kasashen da suke makobtaka da ita gami kasashen yankin baki daya.

Dukkanin mambobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya 15 sun kada kuri'ar amincewa da tsawaita wa'adin takunkumin da aka kakaba kan kasar da Sudan ta Kudu zuwa farkon watan Yunin wannan shekara ta 2016.

Takunkumin dai ta takaita ne kan bangarorin da suke jagorantar yakin basasa a Sudan ta Kudu, inda aka haramta musu gudanar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje tare da hana su amfani da dukiyoyinsu da suke bankunan kasashen waje, kuma takunkumin ya fara aiki ne tun a watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2015.

Add comment


Security code
Refresh