An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 05:07

Kasar Amurka Ta Yi Gargadi Kan Kara Yawaitar 'Yan Ta'addan Da'ish A Kasar Libiya

Kasar Amurka Ta Yi Gargadi Kan Kara Yawaitar 'Yan Ta'addan Da'ish A Kasar Libiya
Majiyar rundunar sojin Amurka ta yi gargadi kan kara yawaitar 'yan ta'adda kungiyar Da'ish a cikin kasar Libiya, inda a halin yanzu yawansu ya doshi dubu hudu zuwa dubu shida.

David .M. Rodriguez kwamandan rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afrika ya bayyana cewa; A cikin watanni goma sha biyu zuwa sha bakwai da suka gabata, yawan mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ya nimka har sau biyu a kasar Libiya, inda suka kai kimanin 4000 zuwa 6000.

Kwamandan rundunar sojin na Amurka ya kara da cewa; Mafi yawan 'yan ta'addan kungiyar ta Da'ish sun kafa sansanoninsu ne a garin Sirt mahaifan tsohon hambararren shugaban kasar dan kama karya marigayi Muhammad Gaddafi da kuma garuruwan Darna da Benghazi da ke gabashin kasar, haka nan Sabarata da ke yammacin kasar ta Libiya.

Rodriguez ya fayyace cewa; Babban aikin da ke gaban sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libiya shi ne kokarin samun hadin kan al'ummar kasar sannan shirin tunkarar matsalar ta'addancin kungiyar Da'ish.

Add comment


Security code
Refresh