An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 18:19

Yan Gudun Hijiran Palasdinawa Da Suke Kasar Lebanon Sun Bukaci Tallafin M.D.D

Yan Gudun Hijiran Palasdinawa Da Suke Kasar Lebanon Sun Bukaci Tallafin M.D.D
Yan gudun hijiran Palasdinawa da suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira da ke kasar Lebanon sun bukaci tallafin Majalisar Dinkin Duniya domin warware musu wasu daga cikin matsalolinsu.

Majiyar 'yan gudun hijirar Palasdinawa da suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira da ke kasar Lebanon ta gabatar da bukatu ga ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, inda majiyar ta bayyana cewa a lokacin ziyarar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon sun gabatar masa da tarin korafe-korafensu musamman matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya.

Majiyar 'yan gudun hijiran ta Palasdinawa ta bayyana cewa daga cikin irin matsalolin da suke fuskanta akwai rashin kayayyakin kiwon lafiya kuma Ban Ki-Moon ya dauki alkawarin ganin Majalisar Dinkin Duniya ta hanzarta aiko da gudumawa a wannan bangaren.

A halin yanzu haka dai akwai 'yan gudun hijirar Palasdinawa fiye da 400,000 da suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira da ke cikin kasar ta Lebanon.

Add comment


Security code
Refresh