An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 17:24

Cibiyar Enterprise Ta Zargi Shugaban Turkiyya Da Hannu A Mara Baya Ga Kungiyar Da'ish

Cibiyar Enterprise Ta Zargi Shugaban Turkiyya Da Hannu A Mara Baya Ga Kungiyar Da'ish
Cibiyar bincike ta Enterprise ta kasar Amurka ta bayyana cewa; Shugaban kasar Turkiyya ba zai taba barin a kawo karshen kungiyar ta'addanci da Da'ish mai kafirta musulmi da suka yi kaurin suna a kasashen Siriya da Iraki ba.

A rahoton da cibiyar bincike ta Enterprise ta kasar Amurka ta fitar yana dauke da cewa; Matukar shugaban kasar Turkiyya yana kan karagar shugabancin Turkiyya ba zai yiyu a kawo karshen ayyukan ta'addancin kasar Siriya ba saboda matakin da kasarsa ta dauka na goyon bayan 'yan ta'adda da suke gudanar da ayyukan ta'addanci a kasashen Siriya eda Iraki.

Rahoton cibiyar ya kara da cewa; Gwamnatin Turkiyya ta bude kan iyakar kasarta ta zame hanyar kutsen 'yan ta'adda zuwa cikin kasar Siriya, inda zuwa yanzu 'yan ta'adda da suka fito daga kasashen duniya daban daban suka samu shiga cikin kasar Siriya ta kan iyakar Turkiyya.

Add comment


Security code
Refresh