An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 05:11

Kwamadan IRGC Na Iran: Iran Ba Za Ta Taba Bari A Rarraba Wata Kasar Musulmi Ba

Kwamadan IRGC Na Iran: Iran Ba Za Ta Taba Bari A Rarraba Wata Kasar Musulmi Ba
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin kasar Siriya a fadar da take yi da 'yan ta'adda yana mai jan kunnen cewa Iran ba za ta taba bari a raba wata kasar musulmi ba.

Manjo Janar Jafari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musuluncin inda ya ce ko shakka babu Iran za ta ci gaba da goyon bayan tabbatuwar gwamnatin Siriya da kuma fadar da take yi da 'yan ta'adda bugu da kari kan ci gaba da zaman kasar guda, kamar yadda ba za ta taba bari a rarraba wata kasar Musulmi ba, yana mai cewa raba kasashen musulmin wata siyasa ce ta Turawan Ingila da kuma yahudawan sahyoniya wanda Iran ba za ta taba amincewa da shi da kuma raunana musulmi ba.

Haka nan kuma yayin da ya koma siyasa da kuma matakan da wasu kasashen larabawan Tekun Fasha suke dauka kuwa kan wasu kasashen yankin musamman Yemen da Labanon, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya ce: Dakarun kare juyin juya halin Musuluncin a shirye suke wajen mayar da martani ga neman tsokana da wuce gona da irin gwamnatoci irin su Saudiyya da Bahrain da makamantansu, wadanda aka bar su a baya a fagen siyasar zamani, abin da kawai dakarun suke jira shi ne a ba su umurni.

Har ila yau Manjo Janar Jafari ya sake jaddada aniyar Iran ta ci gaba da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya masu fada da haramtacciyar kasar Isra'ila irin su kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa, kamar yadda kuma ya sake jaddada aniyar dakarun nasa na ci gaba da karfafa makamai masu linzamin da suke da su, duk kuwa da ci gaba da ihu bayan harin da gwamnatocin Amurka da wasu na Turai suke yi.

Add comment


Security code
Refresh