An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 04:21

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Shari'ar Da Ake Wa Mataimakin Shugaban Kenya Williams Ruto

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Shari'ar Da Ake Wa Mataimakin Shugaban Kenya Williams Ruto
Kotun duniya mai hukunta manyan laifuka (ICC) ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto na hannu cikin tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2007.

A wata sanarwa da kotun ta fitar ta ce kusan dukkanin alkalan kotun sun amince da daukar matakin watsi da tuhumar ake yi wa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto tare da wani dan jarida Joshua arap Sang bisa zarginsu da hannu a kisan gillan da ake zargin an yi wa mutane kimanin 1,200 a rikicin da ya barke bayan zaben shekara ta 2007 da aka gudanar a kasar.

Shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta, wanda shi kansa aka kori karar da aka kai shi gaban kotun bisa wannan zargin a shekara ta 2014, ya bayyana farin cikinsa da wannan hukumcin yana sake jaddada cewar babu wani abin da mataimakin nasa yayi.

Mutanen da rikicin ya cutar da su dai ta bakin lauyansu Wilfred Nderitu, sun bayyana rashin jin dadinsu da wannan hukunci inda ya ce sam ba a yi adalci ba.

Kafin wannan lokacin ma dai babbar mai shigar da kara a kotun Fatima Bensouda ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira katsa landan da ake yi cikin shari'ar.

Add comment


Security code
Refresh