An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 18:04

Kaucewa Biyan Haraji Babbar Matsala Ce Ga Duniya, Inji Obama

Kaucewa Biyan Haraji Babbar Matsala Ce Ga Duniya, Inji Obama
Kwanaki biyu bayan tonon asirin Panama, shugaban Amurka barack Obama ya bayana cewa kaucewa biyan hajari babbar matsala ce ga duniya.

Obama wanda ke bayana hakan a wannan Talata ya ce babban kalubale ne ga duniya kaucewa biyan haraji, kuma hakan na bukatar kara hadin gwiwa domin magance wannan matsala.

A cewar Obama bayanan asiri da aka fitar daga Panama wanda ya shafi manyan ‘yan siyasar duniya, da wasu fitattun mutane ya nuna karara yadda kaucewa biyan haraji dama halasta kudaden haramun ke zaman babbar matsala ga duniya.

Rahoton binciken wanda wata cibiya da ke kasar Panama ta fitar, ya dogara ne a kan wasu muhimman bayanai na sirri sama da milyan 11, inda a ciki aka ambaci manyan kamfanoni na kasashen duniya akalla 35, bankuna sama da 500 da shugabannin kasashen duniya ciki har da na Afrika daya shafi halasta kudaden haram da kuma rashawa.

Cikin wadanda ake zargin sun hada da wasu makusantan shugaban Rasha Vladimir Putin da Firaministan Pakistan da Sarki Abdallah na Saudiya da shugaban China, da Firaministan Birtaniya David Cameron, sanan akwai Lionel Messi gwarzon dan wasan kwallon kada na duniya, da dan wasan fim din nan Jakie Chan, koda yake dayewa daga cikin wadanda aka ambata sun musunta zargin.

Wannan kwarmaton na Panama dai ya kasance mafi girma fiye da tonon asirin da Shafin Wikileaks ya yi a can baya.

Add comment


Security code
Refresh