An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 17:36

Afirka Ta Kudu : Majalisa Ta Yi Watsi Da Tsige Jacob Zuma

Afirka Ta Kudu : Majalisa Ta Yi Watsi Da Tsige Jacob Zuma
Majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu tayi watsi da yunkurin tsige shugaban kasar Jacob Zuba.

Jam'iyyar ANC mai mulki tayi amfani da rinjaye da take dashi a wannan majalisa inda tayi watsi da wannan bukatar da ke bukatar amuncewa da kashi 2/3 na 'yan majalisun dokokin.

'Yan majalisu 143 ne suka kada kuri'a amuncewa da tsige shugaban, yayin da 233 suka ki amuncewa da hakan, kamar yadda mataimakin shugaban majalisar Lechesa Tsenoli ya sanar.

Babbar jam'iyyar adawa ce a wannan kasa ta (DA) ce ta shigar da wannan kudiri gaban majalisar dokoki bayan da babbar kotun kasar ta same shi da laifin taka kundin tsarin mulki wajen amfani da kudin talakawa domin fadada gidansa.

Kotun dai ta umurci Zuma ya mayar da wani kaso na Dala miliyan 16 da ya yi amfani dasu wajen ayyukan fadada katafaren gidan na sa cikin kwanaki 45 masu zuwa.

Add comment


Security code
Refresh