An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 16:25

ICC Ta Yi Watsi Da Shari'ar William Ruto

ICC Ta Yi Watsi Da Shari'ar William Ruto
Kotun hukuntan mayan laifuka ta duniya ta yi watsi da shari'ar da take yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto dangane da tuhumar laifukan yaki da ake yi masa.

Lauyoyin kotun ta ICC / CPI sun yi watsi da shari'ar ne kasancewar mai gabatar da kara ta kotun, Fatou Bensouda bata gabatar da isasun shaidu ba, domin ci gaba da shari'a.

Hakan ne yasa mafi yawan alkalan suka amunce da yin watsi da shari'a, aman a cewar kotun ana iya daukaka kara kan wannan matakin nan gaba gaban kotun ko kuma gaban wata kotun kasa.

Ana dai tuhumar Ruto tare da wani dan jaridan kasar, Joshua Sang da zargin hannu a kisan mutane sama da 1,300 a rikicin bayan zaben da aka fafata tsakanin shugaba Mwai Kibakida Raila Odinga a watan Desamba 2007.

Kotun dai ta yi watsi da irin wannan tuhumar da aka yi wa shugaban kasar ta Kenya, Uhuru Kenyatta, a 2014.

Add comment


Security code
Refresh