An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 17:30

Iran Ta Sanar Da Tura Wasu Sojojinta Na Musamman Zuwa Siriya

Iran Ta Sanar Da Tura Wasu Sojojinta Na Musamman Zuwa Siriya
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tura wasu dakarun sojojinta na kasa na musamman zuwa kasar Siriya a ci gaba da taimakon da Iran take ba wa sojojin Siriya a fadar da suke yi da kungiyoyin ta'addancin da aka shigo da su kasar daga kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na Iran din ya jiyo Birgediya Janar Ali Arasteh, babban jami'in tsare-tsare na sojojin kasa na Iran yana fadin cewa a yau Litinin wasu dakarun sojin Iran na musamman daga birget ta 65 na sojojin na Iran sun isa kasar Siriya don taimakawa sojojin Siriya da shawarwari a fadar da suke da 'yan ta'adda a kasar.

Har ila yau Birgediya Janar Arasteh ya kara da cewa a nan gaba ma za a sake tura wata tawaga ta kwararrun sojin na Iran duk dai saboda wannan aiki na taimako da ba da shawarwari ga sojojin kasar Siriya a kokarin da suke yi na 'yantar kasar daga 'yan ta'addan.

Su dai wadannan dakaru na birget ta 65 na sojojin Iran din wasu dakaru ne na musamman da suke da kwarewa a bangori daban-daban na yaki da tattaro bayanan sirri.

Tun dai bayan barkewar yakin basasa a kasar Siriya, Iran bisa bukatar shugaban kasar Siriyan Basshar al-Asad ta ke tura dakarun sojojinta zuwa kasar da nufin taimaka gwamnatin fada da 'yan ta'addan daga kungiyoyi daban-daban da aka shigo da su kasar da nufin kifar da gwamnatin Siriyan.

Add comment


Security code
Refresh