An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 03 April 2016 17:38

An Sake Bude Filin Jiragen Sama na Brussels

An Sake Bude Filin Jiragen Sama na Brussels
An sake bude filin sauka da tashin jiragen sama na Brussels dake kasar Belgium a yau lahadi bayan rufe shi biyo bayan kazamin harin da aka kai a ranar 22 ga watan Maris daya gabata.

Rahotanni dake fitowa daga kasar sun ce tuni wani jirgin sama ya tashi daga filin jirgin a wannan Lahadi.

kafin hakan kuma an dauki kwararen matakan tsaro, kuma an umarci fasinjoji dasu kasance suna filin jiragen saman sao'i uku kafin jirginsu ya tashi.

Harin wanda kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai shi a filin sauka da tashin jiragen sama dama na cikin jirgin karkashin kasa yayi sanadin mutuwar mutane 32 tare da raunana wanio adadin mai yawa.

Mutane biyu ne dai aka gano suka kai harin kunar bakin waken

Tun a jiya ne shugaban filin jiragen saman Arnaud Feist ya sanar cewa yau lahadi za’a dan fara amfani da filin, inda jiragen saman uku za su tashi.

Add comment


Security code
Refresh