An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 02 April 2016 04:23

Abdullahiyan: Iran Za Ta Ci Gaba Da Taimako Da Kuma Goyon Bayan Palastinawa

Abdullahiyan: Iran Za Ta Ci Gaba Da Taimako Da Kuma Goyon Bayan Palastinawa
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan lamurran kasashen Larabawa da na Afirka Amir Husain Abdullahiyan ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da ba ta taimako da kuma goyon bayan da ta ke ba wa al'ummar Palastinu da ake zalunta, yana mai cewa Iran tana alfahari da hakan.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta daga birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda yayin da yake bayyana matsalar Palastinun a matsayin babbar matsalar duniyar Musulunci ya bayyana cewar: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da ba ta taimako da kuma goyon bayan da ta ke ba wa al'ummar Palastinu da ake zalunta.

Amir Husain Abdullahiyan ya kara da cewa: Goyon bayan al'ummar Palastinu, shi ne babban lamarin da ke gaban duniyar musulmi, a saboda haka bai kamata matsalar ta'addanci da ke fuskantar yankin Gabasa ta tsakiya ya sanya duniyar Musulmi ta mance da batun Palastinu da Qudus ba.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: Haramtacciyar kasar Isra'ila dai ita ce babbar barazanar da yankin Gabas ta tsakiya ke fuskanta, don haka ya ce boren Intifada na uku da al'ummar Palastinu suka kaddamar wani mayar da martani ne na Palastinawa a kokarinsu na neman hakki da kuma dawo da kasarsu da yahudawan suka mamaye.

Add comment


Security code
Refresh