An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 31 March 2016 03:39

Sojojin Yamen Sun Halaka Sojojin Saudiyya Da 'Yan Korensu 378 A Cikin 'Yan Kwanaki Kadan

Sojojin Yamen Sun Halaka Sojojin Saudiyya Da 'Yan Korensu 378 A Cikin 'Yan Kwanaki Kadan
Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun yi nasarar halaka sojojin mamayar Saudiyya da 'yan korensu 378 a cikin 'yan kwanakin nan a Tsibirin Midi da ke lardin Hajjah a arewa maso yammacin kasar Yamen.

Majiyar rundunar sojin Yamen a jiya Laraba ta watsa rahoton cewa; A kokarin da rundunar sojin masarautar Saudiyya da sojojin haya na kasashen Larabawa da suke goyon bayan mamayar Saudiyya kan kasar Yamen suka yi na karbe iko da Tsibirin Midi da ke lardin Hajjah a shiyar arewa maso yammacin Yamen, sun fuskanci mai da martani daga sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa- kai na kasar lamarin da ya kai ga kashe sojojin Saudiyya da 'yan korensu na kasashen Larabawa 378 cikin har da kwamandan runduna ta 209 na sojin saman Saudiyya.

Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun yi nasarar fatattakan sojojin na Saudiyya da na 'yan korensu daga Tsibirin na Midi tare da tarwatsa makamai da motocin yaki baya ga kwasar ganimar na'urori da sojojin na Saudiyya suka yi watsi da su a kokarin tsira da rayuwarsu.

Add comment


Security code
Refresh