An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 28 March 2016 05:29

Belgium : Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kai 31

Belgium : Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kai 31
Hukumomin kasar Belgium sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren kunar bakin waken da aka kai birnin Brussels ranar Talata data gabata sun kai 31.

A wata sanarwa da kwamitin dake bincike kan lamarin ya fitar jiya Lahadi ya ce kawo yanzu an kai ga tantance gawawakin mutane ashirin da daya.

Sanarwar ta kara da cewa goma sha biyar daga cikin mutanen sun mutu ne a harin kunar bakin waken filin jirgi sama, sanan wasu 13 a harin jirgin karkashin kasa.

Wadanda aka tantancen sun hada da 'yan asalin kasar ta Belgium 16, sauran 12 sun hada dana wasu kasashen ketare takwas da suka hada dana jamus,Amurka,Birtaniya,Sin,Faransa,Italiya,Newsiland da Sweden.

Wannan alkalumandai a cewar masu binciken basu shafi wadanda suka kai harin ba.

Add comment


Security code
Refresh