An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 21 March 2016 09:54

Firayi Ministan Benin Lionel Zinhou Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Kasar

Firayi Ministan Benin Lionel Zinhou Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Kasar
Rahotanni daga kasar Jamhuriyar Benin sun bayyana cewar firayi ministan kasar kuma dan takaran jam’iyya mai mulkin a kasar Lionel Zinhou ya amince da shan kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar firayi minista Zinhou ya bayyana amincewa da shan kayen ne cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na internet inda ya ce tuni ya kirayi abokin takarar tasa kuma hamshakin dan kasuwa Patrice Tallon don taya shi murnar nasarar da ya samu da kuma yi masa fatan alheri.

Sakamakon farko farko dai sun nuna cewa Mr. Tallon yana da kashi 64.8 cikin dari na kuri'un da aka kada alhali firayi minista Zinhou yana da kashi 35.2 cikin dari na kuri'un da aka kada din.

A zagaye na farko da aka gudanar dai firayi minista Zinsou, wanda yake samun goyon bayan shugaban kasar mai barin gado Thomas Boni Yayi shi ne ya ke kan gaba to amma sakamakon rashin samun kuri'un da ake bukata hakan ne ya kai su zuwa ga zagaye na biyu.

Add comment


Security code
Refresh