An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 26 January 2016 09:47

MDD Ta Bukaci A Sanya Wa Sudan Ta Kudu Takunkumin Sayen Makamai

MDD Ta Bukaci A Sanya Wa Sudan Ta Kudu Takunkumin Sayen Makamai
Kwamitin sanya ido na Majalisar Dinkin Duniya kan takunkumin da aka sanya wa kasar Sudan ta kudu ya bukaci kwamitin tsaron Majalisar da ya sanya takunkumin sayen makamai a kan kasar don hada ci gaba da kazamtar yakin basasan da ke faruwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar kwamitin sanya idon ya bayyana hakan ne cikin rahotonsa na shekara-shekara da yake fitarwa inda ya ce har ya zuwa yanzu shugaban kasar Sudan ta Kudun Salva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar suna ci gaba da jagorantar bangarorinsu, don haka su ne kai tsaye suke da alhalin ci gaba da zubar da jinin da ke faruwa a kasar, wanda hakan ya sanya sun cancanci a sanya musu takunkumi.

Tun da jimawa dai wasu kasashen kwamitin tsaron suka so a sanya wa Sudan ta kudun takunkumin sayar mata da makami, to sai dai kuma kasashen Rasha wacce take da hakkin hawa kujerar naki da kuma kasar Angola sun ki amincewa da hakan, suna masu cewa suna tsoron takunkumin zai zamanto a kan bangare guda ne kawai.

Har ila yau kwamitin ya bukaci a sanya takunkumi a kan wasu manyan masu fadi a ji a kasar Sudan ta kudu wadanda suke da hannu wajen hana ruwa gudu a kasar. Duk da cewa ba a fitar da sunayen mutanen ba, amma kamfanin dillancin labaran Reuters din ya ce akwai sunayen shugaba Kiir da madugun 'yan tawayen Riek Machar a ciki.

Add comment


Security code
Refresh