An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 23 January 2016 10:42

Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Somaliya

Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Somaliya
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da 'yan kungiyar Al-Shahab suka kai kan wani otel da ke birnin Magadisho fadar mulkin kasar Somaliya a cikin daren Alhamis wayewar garin Juma'a.

A bayanin da kwamitin tsaroin Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Juma'a ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da mayakan kungiyar Al-Shabab suka kai kan wani otel da ke gabar teku a gefen birnin Magadisho fadar mulkin kasar Somaliya da ya yi sanadiyyar lashe rayukan fararen hula.

 

Har ila yau bayanin na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Somaliya da al'ummar kasar musamman iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon harin ko suka jikkata.

 

A cikin daren Alhamis wayewar garin Juma'a ne mayakan kungiyar Al-Shabab suka kai wani harin ta'addanci kan wajen shakatawa na otel din Lido Beach da ke gabar teku a gefen birnin Magadisho na kasar Somaliya, harin da ya yi sanadiyyar lashe rayukan mutane akalla 20 tare da jikkata wasu adadi na daban.

Add comment


Security code
Refresh