An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 21 January 2016 11:46

Kwamitin Tsaron M.D.D Ya Yi Maraba Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Libiya

Kwamitin Tsaron M.D.D Ya Yi Maraba Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Libiya
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da kafa gwamnatin hadin kan kasa a Libiya tare da neman Majalisar Dokokin Kasar da ta hanzarta amincewa da gwamnatin musamman ganin irin halin tsaka mai wuya da kasar ke ciki.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a jiya Laraba ya fitar da sanarwar ta ya murna kan sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da aka kafa a Libiya yana mai jaddada yin kira ga 'yan Majalisun Dokokin Kasar kan hanzarta kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamntin musamman ganin irin kalubalen da ke fuskantar kasar.

Har ila yau dukkanin mambobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya 15 sun jaddada bukatar ganin an aiwatar da dukkanin yarjeniyoyin da aka cimma kan batun samar da gwamnatin kasa da zata hada dukkanin bangarorin al'ummar kasar ta Libiya da nufin warware dambaruwar siyasar kasar.

Add comment


Security code
Refresh