An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 December 2015 06:33

Jakadan Libiya A UN Ya Ce: Kasashen Turai Zasu Fara Kai Hari Kan Yan Ta'adda A Kasarsa

Jakadan Libiya A UN Ya Ce: Kasashen Turai Zasu Fara Kai Hari Kan Yan Ta'adda A Kasarsa
Jakadan kasar Libiya a Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa; Kasashen yammacin Turai sun amince da bukatar fara kai hare-hare ta sama kan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a kasar Libiya.

 

Jakadan kasar Libiya a Majalisar Dinkin Duniya Ibrahim Aldabashi a jiya Juma'a ya sanar da cewa; Kasashen yammacin Turai sun amince da shawarar daukan matakin kai hare-hare ta sama kan mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a kasar Libiya, kuma kasashen Italiya, Amurka, Birtaniya da Faransa suna daga cikin kasashen da zasu fara kaddamar da hae-haren ta sama.

Aldabashi ya kara da cewa; Matakin yaki da ta'addancin kungiyar Da'ish da rundunar sojin Libiya ta dauka ta kasa mataki ne kayyadadde, amma idan wadannan kasashe hudu na Turai suka fara kaddamar da hare-hare ta sama kan kungiyar ta Da'ish akwai yiyuwar samun damar dakile ayyukan ta'addancin kungiyar ta Da'ish.

Add comment


Security code
Refresh