An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 01 December 2015 12:17

Manufar Wasikar Ayatullah Khamenei Ita Ce Bayyanar Da Hakikanin Musulunci

Manufar Wasikar Ayatullah Khamenei Ita Ce Bayyanar Da Hakikanin Musulunci
Shugaban kwamitin al’adu na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Malam Ahmad Salik ya bayyana cewar manufar wasikar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa matasan Turai a kwanakin baya ita ce gabatar da Musulunci na hakika.

 

 

Ahmad Salik ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labaran hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran a yau din nan Talata, inda ya ce: babban sakon da ke cikin wasikar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya aike wa matasan Turan shi ne gabatar da hakikanin Musulunci ba tare da gurbata shi, don su sami damar yi masa fahimta ta hakika kamar yadda yake.

 

Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin karbuwar da wasikar farko da Jagoran ya aike wa matasan Turan a tsakanin matasan kasashen Turai da Amurka, shugaban kwamitin al’adu na majalisar ta Iran ya bayyana cewar: irin karuwar wayewar kai da aka samu tsakankanin matasa da kuma fahimtar halin da sauran al’ummomin kasashen musulmi musamman al’ummar Palastinu suke ciki na daga cikin sakamako na wannan wasikar da Jagoran ya aike wa matasan a wancan lokacin.

 

A ranar Lahadin da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya aike wa matasan kasashen Turai wata wasika inda ya kiraye su zuwa ga tunani kan irin dalilin abubuwan da suke faruwa a kasashensu na ayyukan ta’addanci da kuma hanyoyin magance su na hakika.

Add comment


Security code
Refresh