An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 10 April 2008 12:49

Tarihin Gidan Radio

An bude Sashin Hausa na Gidan Radion Jamhuriyar Musulunci ta Ira ne a ranar 4 ga watan Janairun shekara ta 1995, koda ya ke 'yan watanni kafin wannan ranar dama an soma 'yan shirye-shirye na gwaji. Da farko dai Sashin Hausa na Radio Iran ya fara watsa shirye-shiryensa ne na tsawon minti talatin (3) tare da ma'aikata biyar (5), bayan shekaru hudu (4) kuma ya koma awa daya tare da ma'aikata tara (9). To amma a halin yanzu saboda karuwar yawan masu saurare da kuma yawan neman da suke yi yasa muka kara awa guda, ya zama gaba daya muna watsa shirye-shiryen mu na tsawon awanni biyu (2)ne, awa daya da safe awa daya kuma da dare, tare da yawan ma'aikata goma sha biyu da 'yan rahotanni goma (10) daga kasashen Nigeria, Nijar da Ghana.A lokacin da Sashin Hausan ya fara watsa shirye-shiryensa yana da karancin yawan masu saurare saboda matsalolin da radiyon ya samu na rashin isar sauti zuwa ga masu saurare, amma cikin ikon Allah tare da kokarin da injiniyoyinmu suke ta yi, ya sa sautin kuma a halin yanzun muna samun wasikun masu saurare daga mafi yawan kasashen yammacin Afirka da hausawan da suke kasashen Libya, Saudiyya, Masar da dai sauransu.Haka nan kuma don kara matsowa kusa da masu saurarenmu da kuma 'yan'uwanmu hausawa da ke nahiyar Afirka muna nan muna shirye-shiryen amfani da tashoshin radiyo na FM wadanda za su rika sanya shirye-shiryenmu kai tsaye ta yadda kowa da kowa zai iya kama mu ba tare da wahala ba. Wannan yana tafe cikin yardar Allah nan gaba kadan. DALILIN BUDE GIDAN RADIYON1- Yada addinin Musulunci ga mutanen nahiyar Afirka.2- Ba da sahihin labaran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kasashen Musulmi da na Musulmin nahiyar Afirka.3- Wayar da kan jama'a game da dasisosin mulkin mallaka.4- Yada ilmin Musulunci.5- Ba da labaran ci gaban Musulmin nahiyar Afirka6- Bayani game da akidar Musulunci ga Kiristocin da sauran mabiya sauran addinai na nahiyar Afirka da kuma sauran jama'a.

Add comment


Security code
Refresh