An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 14 March 2010 10:52

Ba Za'a Bai Wa 'Yan Adawa Damar Shiga Gwamnati Ba A Mauritaniya.

Shugaban kasar Mauritaniya Muhammad Ould Abdul'Aziz ya ce ba zai bai wa 'yan adawar kasar wani mukami a cikin gwamnatinsa ba kamar dai yadda wasu 'yan kasar suka ukaci a yi. Muhammad Ould Abdoul'Aziz ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jagorantar wani taron gangami na magoya bayansa a garin Nouakchot fadar mulkin kasar a jiya asabar.Shugaba Abdoul Aziz ya bukaci 'yan adawar da su amince da shi a matsayin zababben shugaba, sannan kuma su dukufa wajen gudanar da ayyukan adawa irin na gida kasa a maimakon kokarin shirya wa gwamnatinsa zagon kasa. Shugaban kasar ta Mauritaniya ya ce har kullum kofarsa a bude take domin tattaunawa da masu adawa da shi, to amma ya kawar da yiyuwar bai wa 'yan adawar wasu madafan iko a cikin gwamnatinsa.Shi dai Muhammad Ould Abdoul Aziz an zabe shi ne a matsayin shugaban kasar Mauritaniya a ranar 18 ga watan yulin shekarar da ta gabata, sakamakon da 'yan adawar suka yi watsi da shi tare kuma da yin zargin cewa an tafka magudi.
More in this category: « f Ma'aikatanmu »

Add comment


Security code
Refresh