An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 28 February 2016 03:01

Ko Kun San Na (346) 10 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria.

Ko Kun San Na (346) 10 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria.
Yau Litinin 10 ga watan Esfand Shekara ta 1394 Hijira Kamaria. Wacce a yi dai dai da 20 Ga watan Jamada-Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce ta yi dai dai da 29 Febrerun shekara 2016 Miladia..

01- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 755 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20 -Jamada-ula-682 Hijira kamaria. Aka haifi Mohammad bin HAssan Hilli wanda aka fi saninsa da «فخر المحققین» a garin Hilla na kasar Iraqi. Mohamad Hilli ya tashi a gaban mahaifinsa wanda shi ma babban malami ne, ya yi karatu a gabansa ya kuma kai matsayin mujtahidi tun yana matashi. «فخر المحققین» ya kware a ilmin tafsiri, harshen laranci, Falsafa da kuma ilmin usul. Har'ila yau «فخر المحققین» ya rubuta littafai da dama. daga cikinsu akwai «شرح مبادی الاصول»، «تحصیل النجاة» و «الکافیه».

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10 -Esfand- 1357 Hijira shamshia. Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jumhuriyar musulunci ta Iran ya shiga birnin Qum bayan shekaru 15 da fitarsa daga garin a zamanin sarki sha. bayan waki'ar 15-Khurdodo- 1342 Hijira shamsia. a lokacinda jami'an tsaron sarki sha ya kashe mutanen garin da dama don goyon bayan da suke bawa immam (q). Sun kuma kama shi suka tafi da shi Tehran daga can suka yi waje da shi. A kashen waje dai ya share shekaru da dama a kasashen Turkia da IRaqi. Sannan daga karshe ya koma birnin Paris na kasar Faransa na yan watanni. Bayan haka Imam ya dawo gida inda ya jagoranci kifar da gwamnatin sarki sha da kuma kafa Jumhuriyar musulunci a Iran. Bayan kafa gwamnatin Imam ya koma Qum da zama inda yake sanya ido a kan harkokin gwamnati daga nesa. Amma bayan yan watanni matsalolin da suka shafi gwamnatin musulunci sun tialsta masa ya koma babban birnin kasar Tehran da zama inda yake sanya idi a kan sabuwar jumhriyyar a kusa.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Esfanda-1366H.SH. a dai dai lokacinda ake yaki tsakanin Iran da Iraqi bayan nasarar juyin juya halin musulunci. sojojin sadam Husain na kasar Iraqi a karon farko sun cilla makaman linzami kan gidajen mutane a birnin Tehran inda suka kashe fafaren hula da dama. Tun bayan fara yakin dai ne sojojin Sadam fara kai hare hare kan fararen hula dan rashin samun nasarar da sojojinsa suke yi a fagen daga.A wadan nan hare hare dai mutanen birnin Tehran da dama suka yi shahada. wasu kuma suka ji rauni.

Add comment


Security code
Refresh