An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 20 February 2016 04:32

Ko Kun San Na (341) 5 Ga Watan Esfan Shhara ta 1394 Hijira Shamsia.

Ko Kun San Na (341) 5 Ga Watan Esfan Shhara ta 1394 Hijira Shamsia.
Yau Laraba 5 ga Watan Esfan Shekara ta 1394 Hiira Shamsia. Wacce Ta Yi Dai dai da 15 Jamada-Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce ta yi dai dai da 24 Febrerun Shekara ta 2916 Miladia.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1399 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15 ga watan Jamada-Ula shekara ta 38 Hijira Kamaria. Aka haifi Imam Aliyu bin Husain (a) wanda aka fi saninsa da Zainul-Abideen a garin Madina. Har'ila yau ana masa lakabi da sajjat don yawan sujadansa. Ima zainul Abidin (a) yana tare da mahaifinsa Imam Husain (a) a karbala, inda a gaban idansa sojojin Yazid dan Muawia suka yanka iyalan gidan manzaon All...(s) aka kuma dora kawunan kan masu ana tawo da suka garuruwa. Imam (a) ya kasance bai da lafiya a lokacin yaki don haka ya kasa taimakawa mahaifinsa a lokacin yakin. Ya rayu shekaru 35 bayan inda a lokacin ya tarbiyantar da musulmi da dama ya kuma baza halaye masu kyau na kakansa manzon All...(s). Littafin sahifatussajjadia yana kunshe da addu'oinsa masu matukar muhimmanci ga muminai. Daga karshe Hisham bin Abdulmalik daya daga cikin sarakunan bani Umayya ya kashe shi yana dan shekara 57 a duniya. Muna taya al-ummar musulmi musamman mabiya iyalan gidan manzon All...(s) murnar tauraro na 4 daga cikin iyalan gidan manzon All. (s).

02- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1399 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15 ga watan Jamada-Ula shekara ta 38 Hijira Kamaria. Mohammad bin Abubakar daya daga cikin sahabban Amirul muminina Aliyu bin Abi Taliba (a) kuma walinsa a kasar Masar ya yi shahada. Bayan da Imam Ali (a) ya karbi ragamat jagorancin al-ummar manzon Al...(s) ya nada Mohammad dan Abubakar a matsayin walinsa a kasar Masar. Amma mu'awiya dan abi sufyan ya aika da rundurun mayaka karkashin jagorancin Amru bin Ass. zuwa kasar Masar inda suka sami nasara a kan mayakan Mohammad suka kuma kamashi da ransa . amma suka konashi har mutuwa. Imam Ali (a) ya ji zafin kisan Mohammad ya kuma roki All.. ya yi masa rahama.

03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 67 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24 Febrerun shekara ta 1949 Miladia. Aka kawo karshen yaki na farko tsakanin Haramtacciyar kasar Israela da kasashen Larabawa. Bayan da yahudawan sahyonia suka shelanta kafuwar Haramtacciyar kasar Israela a cikin watan mayun shekara ta 1948 Miladia , yaki ya barke tsakanin ta da kasashen larabawa. Amma a karshen yakin yahudawan sun sami nasara kan larabawan don irin tallafin makamai na zamani da take samu daga kasashen yamma. Sannan a lokacin yaki ta mamaye wasu kasashen Larabawa wadanda suka hada da Masar da kuma kudancin Lebanon. Daga karshe a rana irin ta yau kasar Masar ta rattaba hannu kan takardun sulhu da yahudawan karkashin shiga tsakanin na Majalisar dinkin duniya a wani tsibiri da ake kira Tsibirin Rudas a tsakiyar tekun Aegean kusa da kasar Turkia. A cikin yerjejeniyar dai yankin Gaza na kasar Palasdinu ya koma karkashin ikon kasar Masar.

 

Add comment


Security code
Refresh