An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 18 February 2016 08:05

Ko Kunsan Na (340) 4 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia

Ko Kunsan Na (340) 4 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia
Yau Talata 4 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia. Wacce ta yi dai dai da 14 ga watan Jamada- Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila Yau wacce ta yi dai dai da 23 ga watan Febrerun Shekara ta 2016 Miladia

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 4 ga watan Esfand shekara ta 1358 Hijira shamsia. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jumhuriyar Musulunci ta Iran ya nada Aya. Dr Mohammad Husain Beheshti a matsayin alkalin alkalai kuma shugaban bangaren sharia na farko a Iran bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar. Imam ya yi wannan dadin ne bayan an rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar, an kuma gudanar da zaben majalisar shoora Ismami, har kuma wakilan majalisar sun fara aiki. Aya. Beheshti na daga cikin fitattun jagororin Jumhuriyar Musulunci ta Iran kafin da bayan samun nasarar juyin juya hali. Kuma yayi aiki don ganin shari'ar musulunci ya tafi kafada da kafada da sabon tsarin gwamnatin musulunci ta kasar da kuma sabuwar majalisar dokoki. Aya. Beheshti ya yi shahada a shekara ta 1360 bayan wani harin ta'addancin da manufai suka kai masa tare da wasu jami'an gwamnatin kasar.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 6 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04 ga watan Esfan shekara ta 1388 hijira shamsia. Abdulmalik Rigi shugaban kungiyar yan ta'adda ta Jundullah, wacce take da cibiya a kasar Pakistan ya shiga hannun jami'an tsaron kasar Iran a wani aiki leken asri mafi sarkakiya da suka shiryamasa. Rigi da mayakansu sun kashe mutane da dama a kan iyakokin kasashen Iran da Pakistan, da dama daga cikinsu jami'an tsaron kan iyaka na kasar Iran ne. Har'ila kungiyar ta Jundullah ta yi kokarin haddasa fitina ta sunnan da shia a yankin sistan bulucinstan na Iran. Jami'an tsaron JMI sun kama rigi ne bayan da suka tilastawa jirgin fasinjan da ke dauke da shi daga Dubai zuwa kasar Qirkiziztan inda an shirya zai gana da wani babban jami'an gwamnatin kasar Amurka, ya sauka a birnin Bandar Abbas na kudancin kasar Iran. Bayan kamashi ne suka kyale jirgin ya ci gaba da tafiyarsa. A bincikrn da aka gudanar kafin a rataya shi a ranar a ranar 30 ga watan Khurdod na shekara ta 1389 hijira shamsia, Riga ya tabbatar da cewa yana samun tallafi daga kasar Amurka da kuma HKI don aikawar ayyukan ta'addanci a kasar Iran.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 217 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23 ga watan Febrerun shekara ta 1799 Miladia. Sarkin kasar Faransa na lokacin Napolio Banoporat, bayan mamayar kasar Masar a rana irin ta yau ya fara yakin mamayar yankin sham wadanda suka hada da kasashen Palasdinu Lebanon da kuma Siria na yansu. A masar dai sojojin Napolio sun kore sojojin Britania yan mulkin mallaka daga kasar sannan suka maye gurbinsu. Amma a yakin da Napolio ya fara a kasar sham wacce take karkashin daular Usmania a lokacin, ya yi ta fafatawa da sojojin daular Usmania wacce take samun tallafin kasashen Rash da Ingila a lokacin. Banda haka rikicin cikin gida ma duk sun hadu sun tilastawa Napolion janyewa daga wadan nan kasashe gaba daya da kuma kawo karshen yakin.

Add comment


Security code
Refresh