An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 08:34

Ko Kunsan Na (338) 02 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia

Ko Kunsan Na (338) 02 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia
Yau Lahadi 02 ga watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia. Wacce Ta yi dai dai 12 Jamada -Ula shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce ta yi dai dai da 21 Ga watan Febreru Shekarar 2016 Miladia

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 58 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21 Febrerun shekarata 1958 Miladia. Mutanen kasashen Masar da Siria sun zabi dunkulewar kasashen biyu zuwa kasa mai suna Hadiddiyar jumhuriyar Larabawa, da kuma shugaba Jamal Abdunnasir na kasar Masar a matsayin shugaban sabon kasar na farko, a wani zaben raba gardama da aka gudanar a cikin kasashen biyu a rana irin ta yau. Manufar hadewar kasashen dai shi ne samun karfi wajen fuskantar barazanar da haramtacciyar kasar Israela takewa kasashen Larabawa. Bayan wani lokaci kasar Yemen ma ta dunkule tare da kasashen biyu. Sabuwar kasar dai tana da majalisar hadin guiwa wacce take kula da lamuran harkokin wajen sabuwar kasar. Sai dai saboda sabani, sabowar kasar da hadaddiyar jumhuriyar kasashen larabawa bata shekaru ukku ba sai ta wargaje saboda rashin amincewar da kasar Syria ta yi kan yadda ake gudanar da gwamnatin kasar a shekara ta 1961 Miladia.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 51 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21 ga watan Febrerun shekara 1965 Miladia. Wasu yan bindiga wadanda ba'a tantance ko su waye ne ba sun kashe Malcon X wani musulmi dan kasar Amurka a lokacinda yake jawabi a wani taro. An haife Malcon X a shekara ta 1925 a kasar ta Amurka. Sannan yana matashi ya hadu da wasu musulman da suka kira shi zuwa ga addinin musulunci ya kuma shiga musulunci. Daga bayan Malcon X ya kafa wata kungiya wacce take ganin tare da addinin musulunci zata kwace hakkokin bakaken fata daga hannu fararen fatar kasar wadanda suke nuna masu wariya. Amma gwamnatin Amurka a lokacin ta fahinci irin hatsarin da take tattare da abinda Malcon yake yi don haka a rana irin ta yau ta aike da wasu yan bindiga bakaken fata wadanda suke bindige malcon har lahira.

03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 43 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21 ga watan Febrerun shekara 1973 Miladia. Jiragen yakin Haramtacciyar kasar Israela sun cilla makaman linzami kan wani jirgin fasinja mallakar kasar Libya dauke da fasinjoji 113 ta kuma kashe mutane 108 daga cikinsu bayan faduwarta. Jirgin dai ya taso ne daga Birnin Tripoli babban birnin kasar Libya kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira na kasar masar. Amma sanadiyar bacin yanayi ya bace hanyarsa ya bi ta kan yankin hamadar Sinna wanda a lokacin yake karkashin ikon Haramtacciyar kasar Israela. Duk da cewa yahudawan sun san cewa jirgin na fasinja ne amma suke cilla masa makaman linzami wanda ya tarwatsa shi a sama ya kuma kashe dukkan mutane 113 da ke cikinsa in banda mutane 5 .

Add comment


Security code
Refresh