An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 03 February 2016 13:14

Ko Kunsan (325) 19 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria

Ko Kunsan (325) 19 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria
Yau Litinin 19 ga watan Bahman shekara ta 1394 hijira kamaria wacce tayi dai dai da 28 Rabi'uthani shekara ta 1437 hijira kamariyya har'ila yau wacce tayi dai dai da 8 ga watan Febreru shekara ta 2016 Miladia.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 799 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28 ga watan Rabi'uthani shekara ta 638 hijira kamaria. Sheikh Abubakar Muhyuddeen Mohammad wanda ya fi shahara da ibnul Arabi, malami babban ya rasu a birnin Damascus na kasar Syria. An haifi Ibnul-arabi a kasar Andulos wato Espania a halin yanzu. Kuma a can ya fara karatu. Bayan kammala karatu ya zagaya kasashen musulmi da dama don bincike da kara sanin tarigi. Daga cikin kasashe da garuruwan da ibnul Arabi ya ziyarta akwai Tunis Makka bagdaza da kuma Halab . Daga karshe ya koma birnin Damascus na kasar syria da zama. Ibnul Arabi ya rubuta littafai da dama wadanda wasu malamai sun lisaftasu a kan fiye da 500 daga daga cikinsu shi Tafsirin al-qu'ani na «تفسیر کبیر». Mafi muhimmanci daga cikin littafan da ibnul-arabi ya rubuta shi ne «فصوص الحکم» inda ya bayyana ra'ayinsa kan ilmin irfani da ikidu a takaice.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 8 ga watan Febrerun shekara 1963 Miladia. Colonel Abdussalam Arif ya jagorancin wani juyin mulki a kasar Iraqi wanda ya kifarda gwamnatin Abdulkarim Kasim, bayan kishe shi ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Iraqi. Wani abin lura shi ne Abdulkarim ma juyin mulki ne ya yi wa Sarkin kasar Iraqi na karshe wato Faisal a shekara ta 1958 miladia. Amma daga karshen shima abdussalam Arif ya rusu a wani hatsarin jirgin sama wanda ake shakkan kaninsa wanda ya gajeshi Abdurrahman Arif ne ya shirya masa a shekara 1966 miladiyya.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19 ga watan Bahman shekara ta 1357 hijira kamaria mutanen kasar Iran a duk fadin kasar sun fito zanga zangar nuna goyon bayan ga gwamnatin rikon kwaryan da Imam Khomaini (q) ya kafa. Sannan a rannan ne sojojin sama na Iran gaba dayansu suka zo mazaunin Imam Khomai ne da ke kudancin Tehran suka bayyana goyon bayansu ga jagorancinsa. Imam Khomaini (q) ya yaba masu ya kuma bukaci goyon bayansu don gudanar da kasar karkashin laimar addinin musulunci. Ragowar jami'an gwamnatin sarki sha, daga rannan sun debe kauna daga samun nasara a kan Imam da masu goyon bayansa. Ranar 19 ga watan Bahman na ko wace shekara ita ce ranar sojojin sama a nan JMI don tunawa da wancan ranar.

Add comment


Security code
Refresh