An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 02 February 2016 10:49

Ko kun san (323) 17 ga watan Bahman Shekta ta 1394 hijira shamsiyya

Ko kun san (323) 17 ga watan Bahman Shekta ta 1394 hijira shamsiyya
Yau Asabar 17 ga watan Bahman shekara ta 1394 hijira kamariya wacce tayi dai dai 26 ga watan Rabi'uthani shekara ta 1437 hijira kamariyya har'ila yau wacce ta yi dai dai da 6 ga watan Febrerun shekara ta 2016 Miladiyya

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17 ga watan Bahman shekara ta 1357 hijira shamsiyya. Bayan da aka kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar Iran tare da umurnin Imam Khomaini (q) mutane kasar a duk fadin kasar sun fito zanga zangar nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya sannan suka bukaci Shapoor Bakhtiyar Priministan gwamnatin Sha ya wargaza gwamnatinsa. Banda haka a rannanin wani jami'in tsaron kasar Amurka mai suna General Haizor ya bar kasar Iran bayan ya kasa hana faduwar gwamnatin shapoor Bakhtiyar. Jami'an wanda ya share fiye da wata guda a birnin Tehran yana bada shawarori da dabarbaru na murkushe magoya bayan Imam Khomiani (q) daga cikin har da shirin juyin mulki duk basu amfana ba, daga karshe ya yanke shawarar fice daga kasar kafin kaduwar gwamnatin sarkin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 919 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26 ga watan Rabi'uthani shekara ta 518 hijira kamariyya. Hassan Sabbah wanda ya kafa daular shi'a Isma'iliyya a kasar Iran ya rasu. An haifi Hassan Sabbah a birnin Qum a shekara ta 445 hijira Qamariyya. Ya fara karatun addini a birnin Rai na nan kusa da birnin Tehran na yanzu. Bayan wani lokaci ya tasirantu da ikidar shi'a Ismaliyya wadanda suka amince da limaman 6 masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s) da kuma Isma'ila dan Imam Sadik (a). Sabbah ya je kasar Masar inda Isma'ilawa suke da daula ya yi karatu har ya zama babban malami. Sannan ya dawo Iran ya jagoranci kafa daular Isma'ilaya daga garin Alamut wanda ke kusa da birninQaiwin a nan Iran. Hassan ya sami magoya baya ya kuma yada ikidar Isma'ilyya a kasar Iran ya kuma kafa daularsu ta farko a bab Ira.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 94 da suka gabata a rana irin ta yau wato 6 ga watan Febreru shekara ta 1922 Miladia manya manyan kasashen duniya wadanda suka hada da Amurka, Faransa, Britania da kuma Italia sun rattaba hannu kan wata yerjejeniya ta hana amfani da makaman kare dangi a yaki a birnin Washington na kasar Amrka. Yerjejeniyar wacce aka fi saninta da yerjejeniyar kasashe biyar ta haramta amfani da makaman iskar guba da sinadarai masu da isakar gas masu kashewa a yaki. Sai kuma a shekara 1925 Miladia wasu karin kasashe da dama a duniya sun sanya hannu a kan wannan yerjejeniyar a cikin watan yuli na wancan shekara. Sai dai wannan bai hana wadan nan kasashe amfani da irin wadan nan makaman da aka haramta ba. musamman a yakin Vetnam da kuma yakin shekaru 8 wanda Iraqi ta dorawa Jumhuriyar musulunci ta Iran.

Add comment


Security code
Refresh