An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 20 January 2016 17:26

Ko Kun San (1-30)- Azaar shekara ta 1394 Hijira Shamsiyya

Ko Kun San (1-30)- Azaar shekara ta 1394 Hijira Shamsiyya
Yau Lahadi 01-Azaar-1394H.SH=10-Safar-1437H.K.=22-Nuwamba-2015M.

Yau Lahadi 01-Azaar-1394H.SH=10-Safar-1437H.K.=22-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 72 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Nuwamba-1943M. Kasar Lebanon ta sami encin kanta a dai dai lokacinda ake cikin yakin duniya na biyu. A shekara 1918 M bayan wargajewar Daular Usmania turawan Faransa suka mamaye kasar Lebanon, sannan a shekara 1923M majalisar hada kan kasashen duniya na lokacin ta tabbatarwa kasar Faransa iko a kan kasar Lebanon. Hakan ya zama masomin tashe tashen hankula a kasar ta Lebanon . Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacin samun encin kai a shekara 1943M.

Kasar Lebanon dai tana da fadin kasa kilomita murabbaee 10,400 kacal, sannan tana iyaka da tekun medeterenian daga yamma sai kuma kasar Palasdinu da aka mamaye daga kudancin kasar . Tana iyaka da kasar Syria ta gabas da arewa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Nuwamba-1963M. John F Kennedy shugaban kasar Amurka na lokacin ya mutu a wani harin da aka kai masa a lokacinda yake ziyarar aiki a jihar Dalas. An haifi Kennedy a shekara 1917M, bayan kammala karatu Kennedy ya shiga siyasa ya kuma zama dan majalisar wakilai na Amurka har sau ukku sannan ya zama senator sau guda. Wani abin jan hankali a cikin kisan Kennedy shi ne, wanda aka ce ya kasashe shi wato Lee Harvey Oswald, yam utu yan kwanaki a hannun wani mai suna Jeek Roby, sannan aka ce shi Roby ma ya mutu a kurkuku sanadiyyar cutar kansa. Da haka ne aka yi rufa rufa kan wanda ya kashe Kennedy.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 44 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Nuwamba-1971M. Gwamnatin kasar Britania ta kauda kwashe sojojinta daga yankin tekun Farisa. Bayan da mafi yawan kasashen da turawan ingila sukewa mulkin mallaka sun sami encin kai, gwamnatin ta yi rauni don haka ta yanke shawarar ficewa daga kasashen da dama a yankin Asia. Kasashe wadanda suka hada da yankin mashigar ruwa ta Swiz a kasar Masar, Tekun Amman, Singapore Malasia da wasu wurare da dama. A cikin wannan halin ne turawan britania suka fitar da kasar Bahrain daga hannun iran bayan da ta kasance wani yanki na kasar Iran kafin ta mamaye ta.

===========================================================

Yau Litinin 02-Azaar-1394H.SH=11-Safar-1437H.K.=23-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 100 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Azaar-1294H.SH. Aka kafa komitin kare kara a birnin Qum a dai dai lokacinda ake cikin yakin duniya na daya. Bayan da sojojin Rasha suka mamaye wani yanki na kasar Iran suka kuma kama hanyar Tehran an wargaza majalisar kasa dake birnin Tehran. Sannan wasu yan majalisar wadanda suka hada da manya manyan malaman addini da kuma yan kasuwa suka koma garin Qom inda suka kafa komitin kare kasa don fuskantar sojojin Rasha da Britania. Amma bayan da sojojin Rasha suka mamaye garin Sawata da ke nan kusa da Tehran sai sojojin Rasha suka kama hanyar Qum daga nan ne Komitin kare kasa ta bar qom zuwa kashan daga kashan zuwa Kirmonsha. A kirmon sha suka kafa gwamnatin rikon kwarya suka kuma fara yakar Rasha bayan da suka mamaye Qum da Kashan. Sai dai bayan wani Lokaci Komitin ya kasa Jurewa ya koma garin Musil na kasar Iraqi daga Musil suka wuce Istambula, inda suka zauna har aka kare yakin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Azaar-1378H.SH. Dr Mohammad Hassan Lutfee Tabrizi masanin ilmin falsafa ya rasu a nan Iran. An haife Dr Lutfee a shekara 1298 H.SH ya yi karatun jami’a a nan Tehran. Inda ya sami shaidar digiri na farko da na biyu sannan ya je kasar Jamus insa ya sami shaidar digiri na ukku a fannin Falsafa. Daga nan Dr Lutfee ya fara aikin tarjaman littafai na aflaton zuwa harsuna turanci Jamusanci da farisanci. Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci ya dawo Iran inda ya ci gaba da ayyukansa na tarjaman littafan falsafa. Dr Lutfee ya rasu yana dan shekara 80 a duniya a shekara 1378H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 936 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Safar-501H.K. Jaafar bin Hussain bin Ahmad malamin Fikihu , hadisi da kuma karatun alqur’ani wanda aka fi saninsa da Siraj ya rasu. An haifi Siraj a shekara ta 419H.K. sannan ya yi karatun addini a wurare daban daban wadanda suka hada da masar Sham. Sheikh Siraj ya rubuta wakoki da dama a wadan nan fannoni. Littafin «نظام المناسک» na daga cikin manya manyan littafan da sheikh Jaafar ya barman.

===========================================================

Yau Talata 03-Azaar-1394H.SH=12-Safar-1437H.K.=24-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 383 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Nuwamba-1831M. Wani masanin ilmin kimiyyar lissafa dan kasar Ingila mai suna Michael Faraday ya gano wutan lantarki. Wannan aiki na faraday dai ya zama babban mataki na ci gaban ilmin kimiyyar lissafi a duniya. An haife faraday a shekara 1791M ya farko ya fara zama a wani shagon littafai ne inda ya yi nazarin littafai da dama. Sanna daga baya ya sami abokin aiki wanda suka fara gwaje gwaje da shi. Banda wutan lantarki dai faraday ya gano wasu ilmomi wadanda suka maida iska ya zama ruwa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato Aya. Sayyeed Mahdi Ruhani daga daga cikin manya manyan malaman a nan Iran ya rasu. An haifi Aya. Ruhani a birnin Qum a shekarata 1303H.K. Aya. Ruhani yana dan shekara 19 ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya share shekaru 8 yana karatu a gaban manya manyna malamai na lokacin. Bayan ya dawo Iran ya ci gaba da karantarwa . Aya. Ruhani yana goyon bayan Imam Khomain (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tun farkon bayyanarsa a shekara ta 1341H.SH. Aya. Ruhani ya rbuta littafai wadanda suka hada da

«بحوث مع اهل السنة والسلفیة» و «تاریخ فرق و مذاهب اسلامی»

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Nuwamba-2013M. Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashe biyar masu kujerun din din din a majalisar dinkin duniya game da kasar Jamus sun rattaba hannu kan yerjejeniyar farko kan shirin nukliyar kasar. Wannan yerjejeniyar dai ta share fagen tattaunawan na bagarorin biyu kan yadda zasu warware takaddar shirin nukliyar kasar Iran wanda kasashen yamma da HKI suke zirginta ta ba ta zaman lafiya bace, indan an tabbatar da hakkan sannan za’a dauke mata dukkan takunkuman aka dora mata. Bayan shekaru da tattaunawa dai bangarorin biyu sun cimma yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata tafiyar da shirin nata da nuklia da zaman lafiya da kuma cire mata dukkan takunkuman da aka dora mata dangane da hakan a cikin watan yuli n shekara ta 2015M.

===========================================================

Yau Laraba 04-Azaar-1394H.SH=13-Safar-1437H.K.=25-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1134 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Safar-303H.K. Abu Abdurrahman Ahmad bin Shu’aibu Annisaaee, wanda aka fi saninsa da شیخ الاسلام daya daga cikin fitattun malaman hadisi ya rasu. An haifi Nisaaee a yankin Khurasan na nan kasar Iran a shekara ta 220H.K. Kuma tun yana matashi ya je kasar Masar don karatu. Bayann kammala karatu Nisaaee ya je sham inda ya rera wakoki na yabon iyalan gidan manzon Al..(s). Amma wadanda basa son hakan sun cutar da shi. Daga ya koma makka da zama. Nisaaee ya rubuta littafai da dama mafi muhimmanci daga cikinsu sun hada da «خصایص امیرالمومنین علی» (ع) da kuma «سنن نسائی» wanda ya tara hadisan manzon All.. (s) a ciki.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 65 da suka gabata a ran airin ta yau wato 14-Azaar-1329H.Sh. Komitin man fetur na majalisar kasar Iran ta lokacin ta ki amincewa da bukatar maida kamfanin haka da sarrafa man Petur nan kasashen Iran da Britania ya zama na Iran kadai. Kafin haka dai tun lokacinda aka gano man fetur a kudancin kasar Iran turawan Ingila suka da nauyin kula da kamfinan haka da sarrafan man na kasar Iran. Amma bayan kin da wannan komitin ya yi sai Aya Kashani ya jagorancin magoya bayan malaman addinin suka gwagwarmaya da turawa da yan barandarsu a cikin gida da kum Dar Musaddik wanda ya jagoranci yan bokon kasar wajen takurawa gwamnati da kuma majalisar kasar amince da bukadar maida kamfanin ya zama na kasar. Daga karshe dai hakan ya tabbata a ranar 29-Esfan-1329H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 50 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-nuwamban-1965M. General Mobuto Seseseko ya jagoranci wani juyin mulkia kasar Za’ir, juyin mulkin da aka zubar da jini mia yawa a kasar. Mobuta yana daga cikin wadanda suka samarwa kasar Encin kai a hannun turawan beljika. Bayan samun encin kai a shekara 1960M Mobuto ya zama Priminster kasar Sai kuma shi ne ya jagorance kashe Patrick Lumumba wani dan kishin kasar mai gwagwarmaya da turawa yan mulkin malla. A shekara ta 1965 Mutubo ya yiwa shugaban kasa juyin mulki sanna ya nada kansa shugaban kasa. A shekara 1971 ya sauya sunan kasar daga Za’ir zuwa Congo. An fara tashe tashen hankula da rashin yarda da gwamnmatinsa a shekara 1990M. Bayan shekaru kimani bakwai yan tawaye sun isa daba da birnin kinsasa, don haka bayan shekaru 37 kan kujerara shugaban kasa a ranar 16-Mayu-1997. Mobuto ya arce daga kasarsa inda bai sake dawowa ba har ya mutu.

===========================================================

Yau Alhamis 05-Azaar-1394H.SH=14-Safar-1437H.K.=26-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun asan cewa shekaru 430 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Safar-1007H.K. Aka haifi Mullah Muhsin Faid Kashani. Daya daga cikin manya manyan malamai addini a nan kasar Iran. Bayan rasuwar mahaifinsa yana dan shekara biyu a duniya Mullah Kashani ya soma karatu a gaban amminsa. Daga baya ya koma birnin Esfahan inda cibiyar daular safawiyawa take, inda kuma manya manyan malamain suka taru, ya je ya kammala karatunsa. Bayan dawowa gida ya fara karantarwa da kuma rubuce rubuce. Daga cikin littafan da ya rubuta akwai. «تفسیر الصافی » ، « مفاتیح الشرایع » ، « الوافی » ، « المُحَجَّة البیضاء » و « النوادر ».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Azaar-1358H.SH. Bayan umurnin da Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayar na hada rundunar mayaka mai dakaru miliyon 20, a rana irin ta yau ce aka kafa rundunar –Basij- ta masu saka kai, wadanda aka dauko daga dukkan bangarori na rayuwa a cikin mutanen kasar.

Basij ta taimaka sosai a yakin shekaru 8 wanda Gwamnatin Iraqi ta Lokacin ta dorawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Har’ila yau bayan yakin ma Basij ta ci gaba da ayyuka a dukkanin bangaren rayuwa na mutanen kasar Iran. Imam Khomai ya sifanta yan basiji a matsayin masu khidima na gaskiya ga All.. da kuma cewa mahada ce ga masu kyawawan halaye da tsaron All….

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 7 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Nuwamba-2008M. Bayan tashin boma bomai a wasu wurare daban daban a birnin Mumbai na yammacin kasar india da kuma fada na tsawon kwanaki ukku tsakanin jami’an tsaro da yan ta’addan da suka tada boma boman suka kuma yi garkuwa da wasu mutane a cikin wasu manya manyan Hotel guda biyu a birnin. Daga karshe an kashe mutane 200 sannan wasu 300 kuma suka ji rauni. Yan ta’addan sun tada boma bomai ne a manya manyan hotel hotel guda biyu da kuma wani tashar jiragen kasa da farko. Sannan suka yi garkuwa da baki yan kasashen waje a cikin manya manyan Hotel Hotel din. Gwamnatin kasar India dai ta ce yan ta’addan sun sami horo ne a cikin kasar Pakistan, amma gwamnatin Pakistan ta musanta hakan.

==========================================================.

Yau Asabar 07-Azaar-1394H.SH=16-Safar-1437H.K.=28-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 44 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Nuwamba-1971M. Kasar Iran ta dawo da ikonta kan wasu tsibirai guda ukku a cikin Tekun farisa bayan da sojojin Turawan Britania suka kawo karshen mamayarsu. Turawan Britania sun mamaye wadan nan tsibirai ne tun shekara 1887M, don kare harkokin kasuwancinta tsakanin kaashen yanken tekun Farisa da tekun Aden zuwa mashigar ruwa ta Hurmuz. Turawan sun dauke sojojin su daga yankuna da dama a Asia da gabas ta tsakiya ne saboda matsalolin tattalin arziki.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Azaar-1359H.SH. Bayan watanni biyu da fara yaki tsakanin Iran da Iraqi sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sami nasarar korar sojojin Iraqi daga tekun farisa. A cikin wani gumurzun sojojin kasashen biyu suka yi a kusa da rijiyoyin harkar man fetur da kasar Iraqi da ke ta Al-bakar sojojin ruwa na iran sun tawatsa jiragen ruwan yakin kasar Iraqi da dama sun kuma lalata rijiyoyin hakar man fetur na kasar Iraqi a cikin ruwa na yankin. Don irin nuna jarunta da kuma nasarar da sojojin ruwa na kasar Iran suka samu a rannan, a nan Iran duk san ranar 7-Azaar ta kewayo a ko wace shekara ana bukukuwan ranar sojojin ruwa a kasar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Azaar-1371H.SH. Bayan da kasashen Turkemanistan, Qazakistan, Uzbekistan, Qazakistan, Tajakistan da kuma Afganistan suka shiga kungiyar raya tattalin arziki ta ECO na yankin adadin kasashen kungiya ya karu zuwa 10. Kasashen Iran Turkiyya da kuma Pakistan ne suka kafa kungiyar tattalin arziki na ECO a shekara 1363H. bayan wargajewar kungiyar RCD na yankin. Kungiyar ECO ce kungiyar raya tattalin arziki mafi girma a kudancin Asia kuma tana da yawan mutane miliyon 350. Har’ila yau kungiyar ta rattaba hannu kan wasu yerjeniyoyi da wasu manya manyan kungiyoyin tattalin arziki a duniya.

========================================================.

Yau Lahadi 08-Azaar-1394H.SH=17-Safar-1437H.K.=29-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Nuwamba-1947M. Babban zauren Majalisar dinkin duniya ta amince ta wani kuduri wanda ya bukaci aka kasashe biyu a lardin kasar Palasdinu. Majalisar dai tana karkashin ikon kasashe masu fada a ji kamar Amurka da kasashen Turai. Yahudawan da kawanda sun yi murda da wannan kudurin, amma Palasdinawa da Musulmi kuma sun ji haushi kan haka. Bayan haka da watanni kasar Britania wacce take mulkin mallaka a kasar ta fidda sojojinta daga kasar Palasdinu a ranar 15-Mayu-1948M, inda sojojin yahudawa suka maye guebinsu a dukkan sansanonin sojojin Britania suka karbi iko da makaman da turawan suka bar masu a cikinsu. Daga nan ne aka fara yaki na farko tsakanin yahudawan da kuma Larabawa da musulmi na farko. Ranar 29-Decemba na ko wace shekara rana ce ta nuna alhina da kuma taya Palasdinuwa bakin ciki da mamayar kasarsu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Azaar-1341H.SH. Majalisar dokokin kasar Iran ta lokacin ta fidda doka wacce ta bukaci samuwar wakilan yankuna da na malamai a cikin majalisar ministocin kasar Iran. Har’ila yau majalisar ta shafe doka wacce ta bukaci ko wani babban ma’aikacin gwamnati ya kasance musulmi ya kuma rantse da Alqur’ani mai girma. Manufar haka dai shi ne fidda hannun malamai da kuma tasirinsu a cikin harkokin mulki. Amma Imam Khomaini (q) wanda assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga baya ya yi jawabi mai zafi inda ya dira a kan sarki da kuma majalisar dokokin kasar ta lokacin. Kuma hakan ya tilastawa sarkin jada baya da kuma sake dawoda dokokin. Wannan shi nasara ta farko wanda Imam Khomani (q) ya samu a kan sarki Sha da yan korensa a shekara 1953M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 5 da suka gabata a ran airin ta yau wato 08-Azaar-1389H.SH. Wasu yan ta’adda masu aiki wa hukumar Mosad ta HKI sai kai hare haren bom kan Dr Majid Shahriyor da kuma Dr Frodon Abbasi masanan ilmin kimiyar makamashin Nuklea a nan birnin Tehran, inda Dr Abbasi ya tsira da raunuka sannan Dr Majid Shariyar kuma yayi shahad. An haifi Shaheed Shariyar a shekara 1345 H.SH a garin Zanjon a nan kasar Iran. Bayan kammala karatunsa a reshen ilmin makamashin nuklia na kimiyar lissafi a jami’ar Amir Kabir a nan Tehran ya fara karantarwa a Jami’ar . sannan bayan da aka bude reshen wannan ilmin a jami’ar Dr Beheshti sai ya koma can da karantawa. Bayan harin da dan kadan ne Jami’an tsaron kasar Iran suka kama maharani suka kuma tabbatar da cewa suna aiki wa HKI ne. Manufar HKI shi ne hana shirin nucliyar kasar Iran ta zaman lafiya ci gaba.

===========================================================

Yau Litinin 09-Azaar-1394H.SH=18-Safar-1437H.K.=30-Nuwamba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1400 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Safar-37H.K. Bisa wasu ruwayoyi A rana irin ta ya ce Uwaisul Kari daya daga cikin sahabban manzon All…(s) da kuma Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) ya yi shahada. Uwais zo madina don ziyartar manzon Al…(s) amma ya samu cewa ya yi tafiya, amma sai ya kasa jiransa don jinyan da yakewa mahaifiyarsa wacce bata da lafiya. Manzon All..(s) ya sha ambatarsa da Alkhairi. Amma bayan rasuwar manzon All..(s) Uwaisu ya tashi daga garinsu Karn dake kasar Yemen ya shiga cikin dakarun Amirul muminina Aliyun bin Abi talib(a) da suka yaki Ma’awiya dan Abi Sufyan a kasar Siffin na yankin sham. Kuma a nan ya yi shahadi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 131 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Safar-1306H.K. Allamah Mir Hamid Hussain Musawi Hindi daya daga cikin manya manyan malaman mazhbar Ahlul baiti a kasar India ya rasu. An haifi Allamah Hindi a shekara ta 1346 H.K. a kasar ta India kuma a can ya yi karantunsa na addini har ya zama babban malami. Baya kammala karatun ya ci gaba da karantarwa. Da kuma rubuce rubuce daga cikin littafan da ya rubuta «عبَقات الانوار» «اسفار الانوار» و «شمع المجالس» .

**Masu sauraro ko kun san cew ashekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Nuwamba-1988M. Uztaz Abdulbasid Abdussamad sanennen malami kuma makrancin Alqur’ani mai girma ya rasu a kasar Masar. An haife Abdul basid a birnin Alkahiri ya fara karatu tun yana karami sannan yana dan shekara 12 a duniya ya sami kyautar farko kan iya kira’a da kuma fitta sautin alqura’ni mai girma. Bayan haka Uztaz Abdulbasid ya zagaya kasashen duniya da dama inda ya karanta masu alqur’ani mai girma da sautinsa mai shiga zuciya. Da haka kuma wasu mutane da dama a wasu kasasn duniya suka musulunta don jin sautin karatunsa. Abdulbasid ya rasu ya bar mana saututtukansa daban daban na karatun Alqur’ani.

==================================================.

Yau Talata 10-Azaar-1394H.SH=19-Safar-1437H.K.=01-December-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Decemba-1982M. Yau ce ranar cutar AIDS ta duniya. Cutar Aids dai cuta ce wacce ta fara bulla a tsakanin masu luwadi a birnin Newyork na kasar Amurka a shekara ta 1981M. musababin Cutar wani nau’in Virus ne da ake kira HIV sannan yana da saurin yaduwa a cikin jika mutum kuma yakan kashe garkuwan jikan dan adama ne, wanda hakan zai bada dama ga sauran cutukkuka su yi saurin yaduwa a cikin jikin mutum sannan ta kashe shi ba bata lokaci. A shekara ta 1982 aka bawa wannan cutar suna AIDS wato (Acquired immune deficiency syndrome) wato cutar mai karye garkuwan jikin dan adam. Domin wayar da kan mutane a ko ina a duniya, da kuma ilmantar da su kan cutar da kuma rage irin wariyar da ake nuawa wadanda suka kama da ita, majalisar dinkin duniya a shekara 1988 ta ware ranar daya ga watan Decemba na ko wace shekara don cimma wadan nan manufofi. Bayan yadauwar cutar a duniya dai kashi 90% na wadanda suka fi kamuwa ta ita daga kasashe matalauta ne suke.. Cutar Aids bata da magani, amma an samar da magunguna da suke rage kaifinsa ya kuma tsawaita rayuwar wadanda suka kamu da ita.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 83 da suka gabata a rana irin ta yau wato gwamnatin kasar Irann a lokacin ta yi watsi da contragin Darcy ta hakar man fetur a kasar Iran na tsawon shekaru 60 wanda aka kulla da wani bature mai suna William Darcy . Contragin ya fayyace cewa kamfanin ba zata biyan haraji ko kuma kudin fito ba a lokacinda zai fitar ko kuma ya shigar da wani abu abinda ya shafi man fetur a kasar. Wannan Kontaragi ya gudana har na tsawon fiye da shekaru 30 kafin gwamnatin Iran ta lokacin ta yi watsi da shi. Gwamnatin kasar Baritania ta kai karar gwamnatin Iran a kotun kasa da kasa kan hakan. Daga karshe dai an amince a sake rubuta wani sabon kontragi a shekara 1933. Sai dai sabon kontragin ma yana da wasu kura kurai masu cutarwa ga mutanen kasar Iran amma dai ya fi na shekara 1901M. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda Priministan Dr Musaddiq ya jagorancin maida kamfanin William Darcy na kasar Britania ya zama na kasar. Da Haka kuma aka yanke hanni turawan ingila yan mulkin mallaka daga arzikin da Al…a bawa kasar Iran a ranar 29-Esfan-1329H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 77 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Azaar-1317H.SH. Aya. Shaheed sayyeed Hassan Mudarrisi malamin addini dan siyasa mai gwagwarmaya da azzaluman sarakunan Iran ya yi shahada. An haifi Aya. Mudarris a shekara 1246H.SH. a garin Urdistan na tsakiyar kasar Iran ya kuma fara karatun addini a gida sannan ya kammala shi a birnin Najaf na kasar Iraqi a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada da Aya. Mirza Shirazi. Bayan dawowarsa gida ya shiga harkokin siyasa har ma ya zama wakili a majalisar dokokin kasar a nan Tehran. Sau da dama wasu wadanda turawa yan mulkin mallaka suka wanke kwakwalensu sukan ce da shi babu ruwan addini da siyasa. Amma sai Aya. Mudarris yakan basu amsa da cewa (addininmu shi ne siyasarmu, sannan siyasarmu shi ne addinimmu. Sarki Riza Khan ya rasa yadda zai yi da shi Aya. Hassan Mudarris , inda daga karshe ya tilasta masa zama a wani kyauye mai suna Khoshmor a arewa maso gabancin kasar. Sannan har zuwa lokacinda ma’aikatansa suka kashe shi a rana irin ta yau. Ranar shahadar Aya. Mudaris ita ce ranar majalisar dokoki a nan Iran.

========================================================.

Yau Laraba 11-Azaar-1394H.SH=20-Safar-1437H.K.=02-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1376 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Safar-61H.K. Ranar arba’een da shahadar Imam Husain (a) da sahabban masu cika alkawari a ranar 10-Muharram na-61H.K. Ranar 20 ga watan Safar na wancan shekara kamar yadda ya zo a cikin wasu ruwayoyi, wato kwanaki arba’een shahadarsu, iyalan Imam Husain (a) wadanda suka sujojin Yazid suka kama a matsayin bayi suka sake dawowa karbala bayan Yazid ya sallamesu daga kasar Sham. Har’ila yau a rannan ce suka hannu da wani babban sahabin manzon Al..(s) wato Jabir dan Abdullahil Ansari yana shirye shiryen ziyarar Imam Husain (a). Da fatan Al..ya yawaita ladarmu a kan wannan musibar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wata 02-decemban- 1956M. Fudel Castro jagorar masu gwagwarmayan kwatar encin kasar Cuba daga hannun shugaba Batista dan koren kasar Amurka a Cuba ya fara gwagwarmayan kwato kasar. Da Farko Castro tare da mayakansa su kai farmaki kan wani sansanin sojojin kasar a Havana amma sojojin Batista sun maida maratani sun kuma kawo karshen harin sun kuma kama Castro suka jefa a kurkuku. Amma bayan wani lokaci suke kore shi daga kasar. Sai kuma a shekara 1958 Castro ya sake tara wasu mayaka a wannan karon sun sami nasarar mamayar wurare masu muhimmanci a birnin Havana sun kuma tilastawa Batista barin kasar.

A shekara 1976 Castro ya Zama Priministan kasar Cuba sannan daga baya ya zama shugaban kasa. Wannan halin ya ci gaba har ya tsufa ya kasa aiki ya mika shugabancin kasar ga kaninsa Raul Castro a shekara ta 2006.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Decemba-1949M. Majalisar dinkin duniya ta fitar da wani kuduri mai lamba 317(17) wanda ya haramta bautar da dan adam a duniya. Sai dai hakan ya taimaka ne wajen rage bautarwa na kai tsaye. Amma mamayar kasashe da kuma mulkin mallakan da manya manyan kasashen duniya suka yi ko kuma takaida arziki a hannun wasu tsirarun kasashen duniya da tilastawa kasashe karban bashi wani nau’I ne na bautarwa wand aba kai tasaye ba. Wannan halin ya jefa mafi yawan mutanen duniya cikin talauci da wahalhalu iri iri.

=========================================================

Yau Alhamis 12-Azaar-1394H.SH=21-Safar-1437H.K.=03-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Azaar-1358H.SH. Mutanen kasar Iran sun kada kuri’ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda aka gina shi bisa karantawar Musulunci da kuma ilmantarwan manzon All.. (s) da iyalan gidansa masu tsarki(a).

Bayan samun nasarar juyin juya hali, da farko mutanen Iran sun amince da tsarin Musulunci a matsayin tsarin da zai gudanar da rayuwarsu. Sannan bayan da aka rubuta kundin tsarin tsarin mulkin kasar kuma aka sake neman amincewarsu da shi inda kashi 99.5% suka amince da shi.

Kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai yana da Fasali 12 da rassa 175, an kara wasu dokoki an kuma fitar da wasu a shekara 1968 wanda shima ya sami amincewarvmautan.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-decemba- 1984M. Aka yi wani hatsari a camfanin Union Cabide a garin Pupole na kasar India. Wannan shi ne hatsarin iskar gas mafi muni a duniya, inda rashin kulana magatana wannan kamfani mallakin kasar Amurka ya sa iskar gas mai gubu ta tsiyaye cikin dare a lokacinda mutane suke barci suka bazu cikin mutane awanda a kai ga mutane 2500 suka rasu a take a yayin da wasu dubu 10 suka je rauni.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 32 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Decemba-1983M. Don daga daraja da kuma taimakwa guragu da wadanda suke da nakasa a gabban jiinsu , a zamanta na 37 a shekara 1983 babban zauren majalisar dinkin duniya ta tsaida ranar 03-Decemba na ko wace shekara a matsayin ranar guragu da wadanda suka sami nakasa a rayuwarsu. Kididdigar Majalisar a duk fadin duniya ya nuna cewa ana da nakasassu kimani rabin billion a duk fadin duniya. Sannan fiye da kashi 70% daga cikinsu suna rayuwa ne a cikin kasashe masu tasowa ne. Nakasa takan samu ne a wasu lokata don rashin samun abincin mai gina jiki ko kuma da suka dace, har’ila yau da rashin kula da tsabta, ko rashin yin alloran riga kafi da sauransu. A halin yanzu dai kasashe da dama sun fitar da wasu shirye shirye don tallafawa makasassu a rayuwarsu, da kuma hanyoyin da zasu shiga cikin al’umma suma a dama da su. Da wannan dalilin ne aka ware wasannin da guragu, da wuraren zama a motoci jiragen sama da kuma kasa. Da kuma wasu tallafi daban daban a wurare da dama.

===============================================.

Yau Jumma’a 13-Azaar-1394H.SH=22-Safar-1437H.K.=04-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 216 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Decemba-1899M. A karon farko an samar da riga kafin cutar Taipot ko zazzabin taipoit a duniya kuma an fara amfani da shi don kare mutane daga kamuwa da cutar. Da farko wasu masananin ilmin magunguna guda biyu a kasar Faransa ne suka hada riga kafin, amma daya baya wani likita dan kasar Faransa mai suna Havat ya kammala aikinsa ta yadda ana iya amfani da shi a jikin dan adam.

Cutar taipot dai yana jawo zazzabi da tsananin ciwon kai. Idan ba’a yi saurin magance shi ba yana iya kaiwa ga kisa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 4 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Azaar-1390H.SH.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 4 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Azaar-1390H.SH. Kwararun sojojin kasar Iran sun sami nasarar kwace ikon sarrafi wani jirgen leken asirin kasar Amurka mafi sarkakiya wanda hukumar CIA ta mallaka, a lokacinda jirgin ya shiga sararin samaniyar kasar Iran.

Jirgin mai suna RQ-170 wani jirgin lrken asirin ne wanda na’urar rada baya iya gane shi, sannan yana da kayan aiki na sarrafa kansa da kansa musamman idan ya rasa sadarwansa da cibiyarsa da ke cikin kasar Afganisatan.

Kwararrun sojojin kasar Iran sun yi nasara kwace iko da kuma sarrafa jirgin har suka sauko da shi ba tare da ta lalace ba. Daga bayan dai sun nazarci girgin har suka samar da irinsa a cikin shekaru ukku da suka biyu bayan. Masanan kasar Amurka dai sun kidime da suka sami wannan labarin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Decemba-1952M. Shuwagabannin kasashen Amurka , Faransa da kuma Britania sun gudanar da taro a tsibirin Bamuda da ke yankin kudancin nahiyar Amurka. Manufar wannan taron dai she tattauna yadda zasu tunkari tarayyar Soviet kan irin tsarin siyasar da za’a gudanar a kasar Jamus bayan yakin duniya na biyu. Kafin haka dai tarayyar Soviet tana mamaye da gabacin birnin Barlin a yayinda wadan nan kasashe ukku suna mamaye da kudancin birnin. Daga karshe dai rashin fahintar juna tsakanin kasashen ya sa aka gina bongon da ya raba birnin berlin da kuma kasar Jamus zuwa biyu a shekara 1961.

=========================================================

Yau Asabar 14-Azaar-1394H.SH=23-Safar-1437H.K.=05-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa 141 shekaru da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Decemba- 1874M. Kasar Iran ta shiga cikin kungiyar bada agaji ta kasa da kasa wacce ake kiran Red Cross. Kafin haka dai an samar da kungiyar a shekara 1864M sannan Iran ta shiga kungiyar a shekara ta 1874M. A lokacin dai Abdussamad Mumtaz wakilin kasar Iran a faransa ne ya wakilci kasar Iran a taro na ukku ta kasa da kasa na kungiyar ta red cross a birnin Paris. Sai dai duk tare da zame mamba a cikin kungiyar kasar Iran bada aike da ma’aikatanta gadan gadan su shiga cikin ayyukan kungiyar ba don abinda kasashen musulmi suke korafi kansa na alamar wannan kungiyar. Daga karshe dai kasashen musulmi sun yanke shawarar kafa kungiyar red cresen wacce take ayyuka irin na red cross a kasashensu.

**Masu saura 136 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Safar-1301H.K. Sheikh Mohammad Oganajafi Esfahani daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An hafi Oga Najafi a birnin Esfahan sannan bayan kammala karatunsa na sharara fage ya je birnin Najaf na kasar Iraqi in da ya kammala karatu a gaban man ya manyan malamai na lokaci. Bayan dawowarsa iran ya koma birnin sfahan inda ya ci gaba da karantarwa da kuma wa’azi cikin mutane da kuma rubuce rubuce. Littafan «لب الفقه» و «لب الاصول» na daga cikin ayyukan Sheikh Oga Bozorg najafi esfahani.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Decemba-2013M. Nelson Mandela tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu kuma madugun gwagwarmaya da tsarin wariyar launin fata a kasar ya rasu yana dan shekara 95 a duniya. An haifi Mandela a shekara 1918 M . Mandela ya sarrafa ,afi yawan rayuwarsa yan fada da tsarin wariyar launin fata a kasar. Ya kuma share shekaru 27 cikin kurkukun shuwagabannin wariyar na kasarsa. Daga karshe a shekara 1990 aka kawo karshen tsarin wariya a kasar sannan mutanen kasar sun zabe shi a matsayin shugaban kasar Afrika ta kudu a shekara 1994M. Mandale shugaban kasar Afrika ta Kudu na farko bakar fata.

====================================================.

Yau Lahadi 15-Azaar-1394H.SH=24-Safar-1437H.K.=06-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Azaar-1357H.SH. Dr Isa Sadik wanda ya assasa Jami’an Tehran a nan Iran ya rasu. An haife shi a shekara 1273 H.SH a nan Tehran , yana dan shekara 17 a duniya ya kammala karatun sakandiri ya kuma sami shiga wata jami’a a kasar Faransa. Bayan kamar shahadar digiri na farko da na biyu a kasar Faransa Dr Isah ya zarce zuwa kasar Amurka a shekara 1309 H.SH inda ya sami digiri na ukku a fannin falsa. Bayan dawowarsa gida ne gwamnatin Iran ta lokacin da Bukace shi da ya kafa jami’a a nan Tehran. Banda haka Dr Isa Sadiq ya assasa makarabtu kimani 2000 a duk fadin kasar Iran a marhaloli daban daban kama daga jami’a har zuwa makarantun sakandari da kuma wasu rassa na ilmi. Daga karshe bayan shekaru masu yawa da khidima wa harkar ilmi a kasar Dr Isa Sadiq ya rasu a shekara 15-Azaar-1357 H.SH yana dan shekara 84 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Azaar-1359H.SH. Komanda sojojin sama Ahmad Kishwari ya yi shahada . An haifi Kishwari a wani kayure daga arewacin kasar Iran bayan kammala makarantar sakadare ya shiga makarantar horarda mayakan sama na kasar Iran inda ya kammala horon cikin nasara. Da farko Komanda Kishwari ya fara aiki ne da sojojin sama na yankin Ilam a nan kasar Iran. Sannan bayan nasarar juyin juya halin musulunci ya shiga cikin aikin kauda makiya jumhuriyar musulunci ta iran a kudancin kasar sannan bayan da kasar Iraqi ta lokacin da mamaye wasu yankunan kasar Iran ya shiga cikin aikin korarsu daga kadar a cikin daya daga cikin hare haren da aka kaiwa sojojin sadam ne Ahmad Kishawar yana kan hanyar dawowa sai ya hadu da ajalinsa inda ya yi shahada.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau watu 06-Decemba-1992M. Wasu mabiya addinin Hindu masu tsatsauran ra'ayin addini a jihar Otapradesh sun rusa masallacin Babri dake jihar. An gina masallacin Babri ne a shekara ta 1528M a kan wani tudu a lokacin sarautar Zahiruddeen Mohammad babri daya daga cikin sarakunan taimorawa a kasar na India. Amma bayan shekaru kimani 300 wani bature mai suna Nobel ya rubta tarihin yankin inda a ciki da gangan ya kawo cewa an gina an gina masallacin babri ne a kan wurin bautar indiyawa. Tun lokacin ne kuma aka fara zaman tankiya tsakanin musulmi mazauna wannan yankin da kuma mabiyan addinin hindu masu tsatsauran ra'ayi wanda ya kai ga kisan mutane da dama a bangarorin biyu. Sai kuma a shekata 1992 mabi addinin hindun suka rusa masallacin. Rikicin masallacin ya kaiga wata kotu a garin Allahabad ta yanke hukuncin a ranar 30-Satumban-2010 kan cewa 1/3 na masallacin ne mallakar musulmi sauran kuma na mabiya addinin hindu.

Yau Litinin 16-Azaar-1394H.SH=25-Safar-1437H.K.=07-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 74 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Decemban-19411M. Jiragen saman yaki na kasar Japan kimani 200 sun kai farmaki kan sansanin sojojin Amurka da ke PearlHarbor a cikin tekun Pecific. Wannan harin ya auku ne a dai dai lokacinda kasashen biyu suna cikin tattaunawar sulhu a yakin duniya na biyu. Bayan harin Amurka ta shelanta yaki kan kasar Japan ta kuma fara kai mata farmaki a duk yankuunan da dama take mamaye da su a yankin asia. Yankunan sun hada da kasar Indonasia na yanzu da wasu tsibirai da dama a yankin. A karshen yakin dai Amurka ta jefa makaman nuklia kan kasar Japan wanda ya kawo karshen yakin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Azaar-1332H.SH. Daliban jami'an Tehran ukku ne sojoji masu tsaron fadar Sarki Sha suka kashe a lokacinda suke nuna rashin amincewarsu da ziyarar mataimakin shugaban kasar Amurka na lokacin ichard Nikson yake yi a kasar. Nikson ya kawo ziyarar ne watanni ukku da juyin mulkin da hukumar CIA na kasar Amurka ta shiya da kuma aiwatar wanda ya kifar da gwamnatin Priminister Dr Mohammad Musaddi. Bayan kissan daliban da kwana guda sai aka bawa Richerd Nikson digirin girmamawa a cikin jami'ar. Ranar 13-ga watan Azaar na ko wace shekara ran ace ta daliban jami'a a nan Iran.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Satumba-1981M. Hukumar liken asirin HKI Mosad ta kashe Abdul-Wahab Kiyoli daya daga cikin wakilan Palasadinawa a majalisar kwatar encin Palasdinu da ke birnin Beyrut na kasar Lebanon. Kiyoli ya kammala karatunsa na jami'a a birnin London na kasar Britania. Sannan ya sami darajar Doktora a bangaren tarihin Palasdinawa da gwagwarmayansu da turawa da kuma yahudawan Isara'ila.

Dr Kiyoli ne ya fara kafa mujalla ta Palasdinawa mai suna "Entacciyar Palasdinu" sannan ya rubuta wasu littafai wadanda suka hada da

«تاریخ نوین فلسطین»، «جنبش مقاومت فلسطین» و «پژوهش هایی در باره فلسطین»

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru wato 71 da suka gabata 07-Decemba-1944M. kasashen duniya da dama sun rattaba hannu kan dokokin zirga zirga da jiragen sama a duniya. Amma bayan shekaro 48 da rattaba hannun wato a shekara 1992 babban zauren majalisar dinkin duniya ta samar da wani kuduri wanda ya maida ranar 7 ga watan decemba na ko wace shekara a matsayin ranar zirga zirgan jiragen sama na duniya.

===========================================================

Yau Talata 17-Azaar-1394H.SH=26-Safar-1437H.K.=08-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Decemba-1914M. Aka yi yakin Falklanda a wani tsibiri mai suna haka mallakin kasar Agentina. Yakin ya aukune tsakanin sojojin ruwa na turawan Jamus wadanda suke mamaye da tsibirin da kuma na turawan Ingila. Daga katshe dai turawan Ingila sun kwace tsibirin Falklanda daga hannun Turawan Jamusa. Sai kuma a karni na 16 maladiyya an gano arzikin man fetur a tsibirin wanda ya sake hada turawan Ingila da faransa yaki kan mallakarsa. Amma du da cewa kasar Agentina ta sami encin kai turawan Ingila suna mamaye da tsibirin Falkland har yanzun da muke magana.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Decemba-1949M. Shugan kasar China na lokacin Chiang Kai-Shek ya arce daga begin babban birnin kasar bayan da dakarun Mau masu akidar gurguzu suka mamaye shi, ya koma tsibirin Taiwan wanda shima bangare ne na kasar china ya kama gwamnatinsa a can. Amma don irin goyon bayan da Kai-shek yake samu daga kasashen duniya a lokacin tsibirin Taiwan ta belle daga kasar China sannan an bawa kasar Taiwan kujerar China a majalisar dinkin duniya da kuma na komitin tsaro na majalisar. Si kuma a shekara 1971M bayan tattaunawa da kasar China babban zauren majalisar ta abince da gwamnatin gurguzu na kasar china da haka kuma Taiwan ta fice daga majalisar dinkin duniya.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato Husin Makki daya daga cikin marubuta kuma dan siyasa a kasar Iran a lokacakin Priminister Dr Musaddik ya rasu. An haifi Makki a shekara 1290H.SH bayan kammala karatu ya shiga aikin gwamnati, sannan ya kuma yi aikin jarida na wani Lokaci. Amma abinda ya fitar da Dr Husain Makki shi ne littafin "Tarihin Iran a cikin shekaru 20" da ya rubuta. Bayan haka Makki ya zama dan majalisar har sau ukku a majalisar dokokin kasar Iran. Yana daha cikin yan majalisa da suke goyon bayan Priminista Dr Musaddik wajen maida kamfanin man fetur na kasar Iran ya zama na kasa Amma bayan juyin mulkin da aka yi wa Musaddik Dr Makki ya shagalta kansa da rubuce rubece kadai Makki ya rasu a shekara ta 1378 yana dan shekara 88 a duniya.

========================================================.

Yau Laraba 18-Azaar-1394H.SH=27-Safar-1437H.K.=09-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 98 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Decemba-1917M. A cikin yakin duniya na daya sojojin turawan ingila sun mamaye kasar Palasdinu. Kafin haka dai daular Usmaniyya wacce kasar Palasdinu take karkashinta a lokacin tana cikin yaki da turawan. Banda kasar Palasdinu dai kafin karshen yakin turawan sun mamaye wasu kasashen musulmi da dama. Mamayar Palasdinu yana a matsayin shekare fage ne na kafa HKI a shekarun da suka biyo baya. Da farko dai sakataren harkokin wajen Britania ya shelanta shirin kafa HKI a kan kasar Palasdinu, sannan jim kadan a shekara ta 1948 yahudawan suka shelanta kafa kasarsu a kan kasar Palasdinu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a ran airin ta yau wato 18-Azaar-1370H.SH. Babban sakataren majalisar dinkin duniya na lokacin Savio Pres de quela ya fitar da wani rahoto dangane da yakin shekaru 8 da aka yi tsakanin Iran da Iraqi inda a cikin rahoton ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraqi ta lokacin karkashin shugabancin Sadam Husain itace ta fara mamayar kasar Iran sannan yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kada.

Wani abin lura a nan shi ne a lokacinda majalisar ta fidda kudurin tsagaita bude wuta tsakanin kasashen biyu JMI ta ki amincewa da kudurin ne na wani lokaci don tana son kudurin majalisar ta bayyana wanda ya fara yaki da kuma tilasta masa biyan diyya amma majalisar ta ki yin haka sai bayan an kawo karshen yakin da shekaru.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Azaar-1372H.SH. Aya. Uzma Sayyeed Mohammad Riza Galpeyagani daya daga cikin manya manyan malaman addini kuma marja'I na mabiya mazhabar Ahlulbaiti (a) ya rasu a nan Oran. An haifi Aya. Galpeyagani a garin Galpeyagan a nan kasar Iran yay i karatunsa na sharara fage da kuma karshe a gaban manya manyan malamai a birnin Qum wadanda suka hada da Aya. Ha'iri yazdi da kuma Aya. Burujadi. Aya. Galpeya gani yana daga cikin fitattun malamai da suke goyon bayan Imam Khomai (q) kan gwagwarmayan da yay i da gwamnatin sarki sha har zuwa samun nasara. Banda tarbiyantar da dalibai ya rubuta littafai da kuma kuma shi ne ya sallaci gawar Imam Khomaini mai tsarki bayan rasuwarsa.

===========================================.

Yau Alhamis 19-Azaar-1394H.SH=28-Safar-1437H.K.=10-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1426 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Safar-11H.K. Manzon All..(a) manzon Alla..na karshe wanda All..ta'ala sun aiko don isar da sakon karshe ga bil'adama kuma sakon musulunci tare da littafin Al-qur'ani mai girma ya rasu yan dan shekara 63 a duniya. An haifi manzon Al..(s) a shekaru 52 kafin hijiransa daga makka zuwa madina. Yana dan shekara 40 All..ya zabe annabi ya kuma fara saukar masa ya ayoyin alkur'ani. Kafin haka dai an sanshi da gaskiya amince da kuma halaye masu kyau. Bayan shekaru 13 da isar da sako a makka Al.. ta'ala ya umurce shi da yin hijira zuwa madani inda ya kafa daular musulunci ta farko. Kuma kafin rasuwarsa daular ta zama mafi karfi daga cikin daulolin kasashen larabawa. Banda haka manya manyan kasashen duniya na lokacin suna fara jin tsaron tasowar daular musulunci. Manzon Al..(s) ya barwa musulmi da kuma sauran mutanen duniya littafin All..(a) wanda All..ya yi alkawarin kare shi daga gaba da bayansa. Da kuam iyalangidansa wadanda zasu isar da hadisansa da kuma fassara al-qur'ani mai girma. A halin yanzu addinin musulunci yana da mabiya fiye da billion daya da rabi a duniya. Da fatan All..daukaka addinisa, ya kuma bamu cetonsa da na iyalan gidans a ranar kiyama.

***Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1387 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Safar-50H.K. Imam Hassan Almujtaba (a) limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s) kuma jikansa na farko daga diyarsa Fatimatuzzahra yay i shahada. Mahaifinsa shi ne Imam Aliyu dan Abitalib (a) an haife shi a shekara ta 3 bayan hijira a madina. Ya gudanar da shekaru 7 na farko a rayuwarsa tare da kakansa manzon Al…(s). Sannan ya kasance tare da mahaifinsa Imam Ali (a) harzuwa shahadarsa a shekara ta 40H.K. Bayan shahadar mahaifinsa shi ne ya karbi jagorancin Al-ummar kakakansa. Amma don rashin samun magoya baya ya miki ikon daular musulunci ga Mu'awiya dan abi sufan wanda ya kasance walin sham tun lokacin khalifa na biyu. Imam Hassan (a) yayi haka ne don hana zubar da jinin musulmi da kuma kare sahabbansa daga kissa. Sai dai bayan sulhu da kimanin shekaru goma Mua'wiya yay i amfani da matarsa ya kashe his da guba a rana irin ta yau.

***Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Azaar-1363H.SH. Imam khomaini (q) wanda ya assasa JIMI ya kama jajalisar juyinjuya hali kan lamuran al-adu da kuma makarantun kasar. Bayan samun nasarar juyin makarantu sun ci gaba da karatu da littafai irin na kasashen yamma. Amma don sauya tsarin karau a kasar an rufe dukkan makarantun kasar na wani lokacin don samar da sabon tsarin karutu wanda zai dashe da tsarin da kuma karantarwan addinin musulunci. Wannan majalisar ta yi aiki cikin dan karamin lokaci aka bude makaranrtun kasar tare da sabbin tsarin karatu kuma majalisar har yanzun tana aiki don ganin an fitar da dukkan aladun da basu dashe da musulunci ba cikin tsarin karatu da tarbiya na makaramtuin JMI.

===================================================.

Yau Jumma’a 20-Azaar-1394H.SH=29-Safar-1437H.K.=11-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 172 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Satumba-1843M. Aka hifi wani likita dan kasar Jamus mai suna Robert Garge, Robert garge ne ya gano kwayar cutar TB ko taron fuska. Bayan kammala karatun a fannin likitanci Robert Garge ya shiga aiki likitanci gadan gadan, ya kuma fara bincike don gano musabbabin wasu cututtuka wadanda suka hada tarin TB, Cutar barci wanda wani kuda mai suna tsetse ke haddasa shi da kuma cutar Anthrax. Daga karshe a cikin watan Maris na shekara 1882 Garge ya sami nasarar gano kwayar cutar tarin Tv, sannan ya samar da riga kafinsa da kuma maganinsa daga baya.

Dr Robert Garge ya karbi kyautar Nobel a shekara 1910M sai dai shima cutar tarin Tb ne ta kasheshi a ranar 27 ga watan Mayun shekara 1910.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 78 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Satumban-1937M. Kasar Italia ta fice daga majalisar kasashen duniya wacce ake kira “leaque of Nations”. An kafa leaque of Nations ne a shekara 1920 bayan yakin duniya na daya don samar da tsarin zamantakewa a tsakanin kasasheb duniya wanda zai hana tsokana da kuma yake yake. Amma kasancewa manya manyan kasashe a lokacin kamar Amurka ta ki shiga cikin Majalisar, sai ya zamanta wadanda suke ciki ma sukan fita daga majalisar sanda suka ga dama. Kamar yadda ya faru da kasar Japan wacce ta fice daga majalisar a shekara 1933. Sai kuma shekru biyu bayan haka kasar Italia ta farwa kasar Habasha da yaki don mamayarta. Sannan daga karshe ma ta fice daga majalisar a ranar 11-Satumban-1937M. Daga bayan kasashen Jamus da Italia suka hada kai don canza tsarin zamantakewa a duniya gaba daya wanda ya jawo yakin duniya na biyu. Duk wadan nan abubuwan suka faruwa amma Leaque of Nations ta iya yin kome ba. Amma duk da haka majalisar ta wanzu har zawa karshen yakin duniya na biyu sanda aka kafa Majalisar dinkin duniya a shekara 1946 mai cibiya a birnin New York na kasar Amurka wacce ta maye gurbinta.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 69 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Satumban-1946M. Aka kafa hukumar UNICEF karkashin kula na MDD. Aikin hukumar shi ne bada tallafin gaggawa a fagen kasa da kasa ga yara da iyayensu mata. Dukkan membobin majalisar dinkin duniya sun amince da kafuwar Hukumar UNICEF wacce take da cibiya a birnin New York na kasar Amurka. Aikin farko wanda hukumar UNICEF ta fara shi ne bada taimako ga yara wanda suka rasa iyayensi sanadiyyar yakin duniya na biyu. Daya baya hukumar ta fadada ayyukanta zuwa tallafwa yara marasa galihu a ko ina suke a duniya a fagen karatu da tarbiya da sauransu.

========================================================.

Yau Asabar 21-Azaar-1394H.SH=30-Safar-1437H.K.=12-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1436 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Safar-01H.K. Rana guda kafin Hijira Manzaon All..(s) daga Makka zuwa Madina shuwagabannin Quraishawa sun gamu a kan kisan manzon All..(s) a taron da suka yi a darunnawa. Bayan haka suka zabi matashi guda daga dukkan kabilun Quraishawa don aiwatar da wannan aikin. Amma sai All..ta’ala ya umurci manzon All..da Hijira a wannan daren ne ya umurci Aliyu dan abi Talib (a) da ya kwanta a shinfidarsa don mushrikai su zaci cewa yana nan, Alhali ya fita ya kama hanyar Madina. Wannan daren shi ake kira “lailatul Mabit” inda bayan da samarin Quraishwa suka shiga dakin manzon All..sai suka kane cewa Aliyu ne a kwance ya saida ransa don tsirar manzon Al..(s).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1233 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Safar-203H.K. Imam Aliyu Bin Musa (a) wanda akewa lakabi da Imam Rida (a) limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s) ya yi shahada. An haife Imam Rida (a) a madina a shekara 148 H.K. Bayan shahadar Mahaifinsa Imam Musa bin Jaafar (a) ya karbi ragamar jagorancin al-ummar kakansa. A shekara ta 200H.K. Khalifa Ma’amun dan Haruna Rasheed ya tilastawa Imam Rida (a) kaura daga Madina zuwa mazaunin Mulkinsa da ke garin Maru a cikin yankin Khurasan, wanda yake cikin kasar Tajakistan a halin yanzu. Ma’amun ya tilasta masa karban mastayin magajinsa da nufin yi masa makirci. Amma bayan da ya gano cewa Makircin bai yi amfani ba sai ya yanke shawarar kashe shi da guba a karshen watan safar shekara ta 203H.K. Muna taya dukkan musulmi juyayin wannan rashin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Satumban-1963M. Kasar Kenya a gabacin Afrika ta sami encin kanta daga hannun turawan Britania yan mulkin mallaka. A shekara 1920 ne dai Turawan suka kafa ikonsu a cikin kasar Kenya suka kuma fara mulkin wariyar a cikinta. A dai dai lokacinda ne mutanen kasar Kenya bakaken fata suka fara gwagwarmayan samun encin kai. A shekara 1950 rikincin ya zama yakin basasa tsakanin bakake da fararen fata yan mulkin mallaka. A karshen yakin basasar an kafa sabon kundin tsarin mulkin wanda ya daidaita tsakanin farere da bakaken fata a kasar Kenya. Sai kuma a shekara 1961 Aka gudanar da zaben majalisar dokokin wacce bakaken fata suka sami gagarumin rinjaye a cikinsa. Shekara guda bayan haka aka gudanar da zaben shugaban kasa Jimo Kenyata ya zama shugaban kasar Kenya sannan aka kawo karshen mulkin mallaka akasar.

=======================================================.

Yau Lahadi 22-Azaar-1394H.SH=01-Rabi’ul-Awwal-1437H.K.=13-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1437 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Rabi’ul –Awwal-Shekara ta farko Manzon Al…(s) ya yi hijira daga Makka zuwa madina bayan shekaro 13 yana kira zuwa ga wannan addinin a Makka. A daren da ta gabace mushrikan makka suka kuduri anniyar kashe shi. Amma Al.. ta’ala ya umrceshi da yin hijira zuwa Madina. Kafin haka ya kulla yerjejeniyar Aqaba ta biyu da mutanen Madina kan zasu kareshi su kuma kare addinin Musulunci da rayukansu da dunkiyoyin su. Bayan isarsa madina ya sami tarbe mai armashi. Ya kuma sami hadin kan mafi yawan mutanen madina wadanda ake kira Ansar wato masu taimakawa. Daga nan ya kafa daular Musulunci. Kafin rasuwarsa a shekara ta 11 bayan hijirarsa Musulunci ya dadu a mafi yawan kasashen Larabawa kuma daular Musulunci ya zama shine daula mafi karfi a yankin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1372 01-Rabi’il-Awwal-65H.K. Mayaka masu neman fansar jinin Imam Husain (a) jikan manzon Al..(s) sun fara gwagwarmaya da sarakunan bani Umayya a birnin Kufa. Imam Husain (a) ya yi shahada ne a ranar 10-Muharram -61H.K. bayan da mutanen Kufa wadanda suka kirashi ya zo ya jagorancesu wajen yakar Yazid dan Mu’awiya amma suke juya suka zama sojojin yazid suka yakeshi suka kashe shi a karbala. Amma bayan shahadarsa wani daha cikin mutanen Kufa mai suna Sulaiman bin Sorad ya hada gagarumin runduna wacce ake kira tawwabin ko masu tuba inda dukkaninsu suka yi shahada wajen neman jinan Imam Husain (a) a karawarsu da sojojin yazid.

=========================================================

Yau Laraba 25-Azaar-1394H.SH=04-Rabi’ul-Awwal-1437H.K.=16-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 251 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Rabi’ul –Awwal-1186H.K. Sheikh Yusuf Bahrani , malamin hadisi, masanin fiqhu kuma mai bincike a cikin karni na 12 hijira kamariyya ya rasu a birnin Karbala na kasar Iraqi. Sheikh Bahrani ya gabatar da rayuwarsa a firkin littafinsa da ake kira « لوء لوء البحرین » inda ya bayyana cewa ya koyi rubutu da karatu a gaban mahaifinsa. Sannan bayan kammala karatu ya je aikin hajji daga nan ya dawo kasar Iran da zama. Anan ne ya rubuta littafai masu muhimmanci wadansa suka hada da « الحدائق الناضره » « انیس المسافر » da kuma . « جلیس الخواطر ». Sheikh ya rubuta littafai wadanda suka kai 32. Kafin rasuwarsa ya koma garin Karbala na kasar Iraqi na zama inda ajali ta same shi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Decemba-1991M. Kasar Qazakistan ta shelenta samun encin kai daga tarayyar Soviet. Kabilar Qazak wadanda suka fi kusa da turkawa ne suka fi yawa a kasar . Sai kuma a farkon karni na 18 miladiyya kasar Rasha ta fara yin tasiri a kasar, da haka kuma bayan juyin juya halin yann gurguzu a kasar Rasha a shekara ta 1920 kasar Qazakistan ta zama daya daga cikin jihohi 15 na tarayyar Soviet. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1991 a lokacinda rauni ya bayyana a fili a tarayyar Soviet, sai mutanen kasar suka kuduri anniyar samun encin kai wanda ya tabbata a rana irin ta yau. Kasar Qazakistan tana da fadin kasa kilomita murabbaee miliyon da dubu 800. Kuma tana makobtaka da kadashen Rasha, China, Uzbekistan, Qarqizistan da kuma Turkamanistan. Mafi yawan mutanen kasar Musulmi ne.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Decemba-1998M. Wata kotun daukaka kara a birnin Paris na kasar faransa ta yanke hukunci dauri da kuma tara kan dan siyasa marubuci musulmi mai suna Prof. Roger Garaudy. Kotun ta samu Garaudy da laifin karyaka “Holocus” wato kisan yahudawa million 6 wanda wai Adolf Hitla na kasar Jamus yayi a cikin yakin duniya na biyu, a cikin wani littafinsa mai suna “Tatsuniyoyin ginshikan siyasar Isra’ila”. Garaudy ya kawo hujjoji masu karfi don tabbatar da ra’ayinsa. Inda daga cikinsu yake cewa yawan yahudawa a dunila a lokacin basu kai haka ba. Ya ce sun kirkiro wannan kariyar ne kawai don duniya ta tausaya masu, ta kuma tallafa masu don samarda da HKI a kasar Palasdimu. Hukuncin da aka yankewa Prof. Garaudy ya tabbatar da cewa encin fadin albarkacin bakin da kasashen yamma suke riyawa, musamman kasar Faransa karaya ce.

========================================================.

Yau Alhamis 26-Azaar-1394H.SH=05-Rabi’ul-Awwal-1437H.K.=17-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Azaar-1370H.SH. Aka dawo da gawan shaheed Tanguyon ministan man fetur na kasar Iran bayan shekaru 11 da shahada a hannun sojojin kasar Iraqi. An haifi Shaheed Tanguyon a shekara 1329H.SH. a nan Tehran bayan kammala karatunsa na jami’a ya shiga cikin masu gwagwarmaya da gwamnatin sarki Sha. Bayannasarar juyin Musulunci a Iran gwamnatin Shaheed rajaee ta nada shi ministan man fetur. A dai dai lokacinda ya kai ziyara a wasu filayen hakar man fetur a kudancin kasar sais hi da wasu ma’aikatansa suka fada hannu sojojin kasar Iraqi. Wanda suka azabta shi har ya kai ga shahada. Sannan ba’a mika gawarsa ba sai bayan shekaru 11 a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Decemba-1992M. Gwamnatin HKI ta kama shuwagabannin kungiyoyin gwagwarmaya da mamayar kasarsu na kungiyar Hamas da kuma jihadul Islami su 415 ta je ta jibgesu a cikin tsananin sanyin hunturu a kudancin kasar Lebanon. Gwamnatin kasar Lebanin ta ki amincewa su shiga kasar ta da haka wadannan Palasdinawa suka zauna cikin sanyi na wasu kwanaki. Wannan tada hankalin kasashen duniya da dama har saida ya kai ga Majalisar dinkin duniya ta samar da wani kuduri mai lamba 977 wanda ya yi All.. wadai da aikin yahudawan. Bayan takurawa na kasashen duniya daga karshe yahudawan sun kyale su suka koma gidajensu a cikin Palasdinu. Amma duk da haka yahudawa sun sake kama wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin inda suke tuhumarsu da kashe wani ba yahude.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Decemban-1998M. Sojojin Amurka da Britania sun soma kai hare hare kan kasar Iraqi bayan sun talastawa sojojin kasar ta Iraqi ficewa daga kasar Kuwaita da ta mamaye. Kafin haka dai Kasashen Amurka da Brirania sun jagoranci samar da kudurori daban daban a komitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan kasar ta Iraqi wadanda suka hada da hana shawagi ko tashin jiragen sama a yankin da kurawan kasar suka zama a arewacin kasar. Da kuma kafa komitin masu binciken iran makaman da kasar Iraqi ta mallaka wanda suka hada da na linzami, guba da kuma nuclia. Mafi yawan hare haren da wadanda kasashen suka kai kan mutanen kasar Iraqi yana cutar da fararen hula ne wadanda suka hada da mata da yara.

=====================================================.

Yau Jumma’a 27-Azaar-1394H.SH=06-Rabi’ul-Awwal-1437H.K.=18-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 113 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Decemba-1902M. A karon farko a duniya an kafa tashar radio na kasa da kasa a birnin Golasbi na kasar Italia. Wani inginia mai bincike dan kasar ta Italia mai suna Gugliemo Marconi ne ya kafa wannan tashar ta radio da haka kuma aka fara sadarwa ko kuma watsa ga mutane takaninin nahiyar Amurka da turai. A lokacin dai ana amfani da tashar radio ne kawai wajen ayyukan tsaro. Daga bayane aka fara shigar da shirye shirye na shakatawa da kuma ilmantar da mutane.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Decemba-1914M. Turawan Britania yan mullkin mallaka sun mamaye kasar Masar sun kuma maida ita mallakarsu. Kafin haka ta farudai, daular Usmaniyya wacce kafin yakin duniya na diya ita ce ke iko da kasar Masar, amma bayan da ta hada kai da kasashen Jamus da Austria a yankin duniya na diya sai kasar Britania ta yanke shawarar mamayar kasar masar don rage karfin daular Usmania. Sai muatanen kasar Masar basu kyale turawan su ci gaba da mallakarsu , don haka bayan gwagwar maya na kimani shekaru sun tilastawa turawan ficew adaga kasar. A halin yanzu dai kasar masar tana gudanar da tsarin jumhuriya mai cikekken encin kai.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Decemba-1979M. Majalisar dinkin duniya ta amince da dokar kafa hukumar kare hakkin mata don kauda bambancin da kem tsakanin zata da mata a duniya da kuma da kuma yin adalci a tsakaninsu. Amma addinin Musulunci yana ganin akwai bambamci tsakanin mata da maza a nau’in halattarsu don haka don haka akwai abinda ko wane bangare yake iyaka dauka, don haka a mahangar addinar Musulunci hakkin mace koma kuma mutuncinta shine kamar yadda yazo a cikin addinin. Har’ila yau wasu addinai ma suna da iran wannan fahintar. Sai dai duk tare da samar da wannan hukumar kare hakkin mata ta duniya, na fiye shekaru 20 da suka gabata , mata a kasashe daban daban suna fama da matsaloli daban daban wadanda suka hada da cikin mutuncin jincin mata.

=======================================================

Yau Asabar 28-Azaar-1394H.SH=07-Rabi’ul-Awwal-1437H.K.=19-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 228 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Decemba-1787M. Kasar Salio ta fada karkashin mulkin mallakar turawna Ingila yan mulkin mallaka. Wani dan kasar Potigal ne ya gano kasar ta Potigal da farko sannan ya kawo mutanensa wadanda suka fara kama bakaken fatar kasar suna saida su a kasuwannin bayi dake kasshen turai da Amurka. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1961 a lokacinda turawan suka bawa kasar kwarya kwaryan cin gashin kai. Sanna bayan a shekara ta 1971 ta fara gudanar da tsarin jumhuriya a kasar. Kasar Salio tana da fadin kasa kilomita murabbee dub71,740 . kuma tana kan bakin tekun Atlantika daga yammacin Afrika. Sannan tana da makobtaka da kasashen Guinea da kuma Liberia.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 163 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Decemba-1852M. Aka yi haifi Albert Abraham Michelson wani masanin ilmin kimiyyar lissafi yan kasar Amurka. Albert Abraham Michelson shi ne ya gano saurin haske . Masanin ya karbi kyautar nobel ta ilmi a shelara ta 1907M. Da farko Michelson ya shiga makarantar sojojin ruwa ne a kasar Amurka inda ya fita da shahadar ilmin lissafi. Sannan ya shiga bincike a cikin halayen haske . inda ya gano saurin sa.da hanyar gwaje gwajen da ya yi a cikin teku.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Azaar-1369 H.SH. Wata kungiyar yan ta’adda a kasar Pakistan wacce take samun goyon bayan kasashen yamma ta kai hari ta kuma kashe Saadiq Ganji shugaban gidan ajiye kayakin tarihi da ke nan Tehran. Ganji ya je kasar Pakistan ne don samun hadin kai tsakanin kasashen biyu don raya tarihin Musulunci wanda kasashen biyu suka mallaka. Ganji ya share kimani shekaru 4 yana wannan aikin a kasar Pakisatan kafin ya hadu da ajalinsa a hannun wadan nan yan ta’adda a rana irin ta yau.

==========================================.

Yau Lahadi- 29-Azaar-1394H.SH=08-R-Awwal-1437H.K.=20-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1177 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-R-Awwal-260H.K. Limami na 11 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wato Imam Hassan bin Ali wanda ake wa lakabi da al-askari (a) ya yi shahada. An haifi Imam Hassan (a) ne a madina a shekara ta 232. Bayan shahadar mahaifinsa Imam Aliyul Hadi (a) Imam Hassan Al-askari ya karbi ragamar jagorancin al-ummar kakaknsa. Ya kuma yada ilmin addinin Musulunci na asali a tsakanin al-ummar musulmi. Zamanin Imam Hassan al-askari (a) yana cike da fitintunu don sanin cewa shi ne zai haifi limami na karshe , wato Imam Mahdi (a). Don haka sarakun Abbasiyawa sun tsananta masa don ganin cewa sun halaka wannan da idan da zaran ya zo duniya. Amma Al…da ikonsa ya boye haihuwar Imam Mohamda Almahdi (a) wanda Al..ta’ala ya yi alkawarin ciki duniya da adalci bayan cikarta da zalunci. Imam Mahdi (a) yana dan shekara biyar aduniya sarakunan abbasiyawa n alokacin suka kashe mahaifinsa Imam Hassan Alkaria (a). Muna mika ta’aziyyarmu ga dukkan musulmi ga wannan juyayin da kuma rashi.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 80 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Decemba-1935M. Azzuddeen al-qassam shugaban palasdinawa masu gwagwarmaya da mamayar kasar Palasdinu wanda turawan ingila suka yi ya yi shahada. An haifi al-qassam a kasar Palasdinu bayan ya kammala karatun sharar fage a birnin Damascus na kasar Syria ya je jami’an al-azhar inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malaman addini a lokacin wadanda suka hada da sheikh Mohammad Abduh. Bayan dawowarsa gida ya sami cewa turawan ingila sun bada dama wa yahudawan sahyoniyya suna ta kwarara daga kasashen turai zuwa kasar Palasdinu. Don haka a shekara 1930 Sheikh Izzuddeeen al-qassam ya hada runduna ta musulman palasdinawa don yakar turawa Ingila yan mamaya. Amma rana irin ta yau, a wani makircin da turawan suka kulla an kashe sheikh izzuddin al-qassam .

**Masu saurar ko kun san cewa shekaru 65 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Azaar-1394H.SH. Uztaz mohamad Husain Khatam wani kwarerren mai zane dan kasar Iran ya rasu. An haifi Khatam a shekara ta 1262H.K a garin Shiraz daya daga cikin biranen kudancin kasar Iran. Uztaz khatam ya zana abubuwa masu kayatarwa wadanda suka hada da ayoyin al-qurani mai girma da rubutunsa masu kyau. A halin yanzu akwai ayyukansa na rubuta da zane zane masu kayatarwa wadanda suke ajiye a cikin dakunan ajiye kayakin tarihi a ciki da wajen kasar Iran.

===========================================================

Yau Litinin 30-Azaar-1394H.SH=09-R-Awwal-1437H.K.=21-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1177 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-R-Awwal-260H.K. Bayan rasuwar mahaifinsa imam Hassan al-askari (a) Imam Mahadi (a) wato Mohammad bin Hassan (a) ya karbi ragamar jagorancin al-ummar kakakansa manzon Al…(a). Imam (a) ya fara jagorancinsa da gaiba karama inda har zuwa shekara ta 328 H.K. yana da jakadu hudu wadanda suke kai kawo tsakaninsa da mabiyansa. Amma bayan mutuwar jakadansa na hudu ya shiga gaiba babba wacce Al.. kadai ya san ranar bayyanarsa. Amma kamar yadda ya tabbata shi ne cewa zai bayyana a lokacinda duniya take cike da zalunci sai ya bayyana don cikata da adalci. A lokacin gaibarsa malamai masu tsoron Al.. da kuma masanan zamaninsu zasu wakilceshi har zuwa ranar bayyanarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa daren 30 ga watan Azaar a cikin kalandar iraniyawa wacce ake kira hijira shamsiyya ita ce dare mafi tsawo a shekara a rabin arewacin duniya ?. A cikin al-adan Iraniyawa daren tana faraway ne daga faduwar rana a ranar 30 ga watan azaar zuwa huduwar rana a ranar daya ga watan Day. A cikin al-adar Iraniyawa da kabilun yankin tun kafin Musulunci sukan gudanar da bukukuwa don shigowar sanyi da dussan kankara , da kuma fatan samun amfanin gona mai albarka a shekara mai shigowa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Decemba-1988M. Sanadiyar tashin bom a cikin wani jirgin fasinja mallakin kasar Amurka, jirgin ya fadi a kan kauyen lokabi da ke yankin Scortland na kasar Britania. Dukkan fasinjoji 270 da suke cikin jirgin sun rasa rayukansu. Bayan yan kwanaki gwamnatocin Amurka da Britania sun tuhubi mutane biyu yan kasar Libya da sanya bom a cikin jirgin. Don haka ne MMD ta kakabawa kasar Libya takunkuma na sayan danyen manta da na zirga zirgan jiragen sama a shekara 1992, har zuwa lokacinda ta miko wadan nan mutane biyu. Daga karshen Libya ta mika mutanen biyu a shekara 1999 aka gurfanar da su a kotun kasa da kasa da e birnin haque wacce ta sallami dayansa sannan ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga dayan. Banda haka kasar Libya ta biya diyyar dukkan mutanen

Add comment


Security code
Refresh