An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 16 January 2016 08:12

(01-30) -Sharivar-1394 Hijira Shamsiyya

(01-30) -Sharivar-1394 Hijira Shamsiyya
Yau Lahadi 01-Sharivar-1394H.sH=08-Zulkada-1436H.K.=23-Augusta-2015M.

Yau Lahadi 01-Sharivar-1394H.sH=08-Zulkada-1436H.K.=23-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1051 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Zulkida-385H.K. Aliyu bin Umar wanda aka fi saninsa da suna Daru-Qudni, wanda ya kasance malami mai ruwaito hadisai ya rasu. Daru-qudni ya fara karatu tun yana karami, sannan ya zagaya zuwa kasashe daban daban don neman Karin ilmi. Daru Qudni ya yi karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa. Daru- qudni sun kware a cikin ilmomi wadanda suka hada da tafsiri, Fiqhu, tsara wakoki da kuma adabin larabaci. Daga cikin littafan day a rubuta akwai «السنن» «سنن دارقطنی» وda «المختلف و المؤتلف» ..

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-sharivar-1377H.SH. Wasu yan ta’adda marasa basira sun bindige Sayyeed Asadullah Larijani wani malami mai jihadi da azzaluman sarakunan kasar Iran suka kaishi ga shahada.

An haifi Asadullah a shekara ta 1314 a nan Tehran. Ya fara karatun Primari a nan Tehran. Daga baya ya shiga karatu a makarantun addini wadanda ake kira hauza, anan ne ya shiga cikin masu goyon bayan Imam Khomani(q) kan gwagwarmaya da yake yi da sarakunan kasar Iran. Bayan samun nasara Alkalin alkalai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Dr Hussain Beheshti ya nada sheikh Abdulla a matsayin mai shigar da kara na fara a ma’aikatar shari’at kasar. Daga baya ya zama shugaban gidajen yarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran . Yana bisa wannan aikin ne munafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kashe shi a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 01 – ga watan sharivar ranar da aka ware a nan iran don tunawa da Husain Binn Abdullah wanda akewa lakabi da Abu Ali Sina, ibn Sina, kokuma sheikh Arra’eesh. An haife shi a garin Balkh na yankin Khurasan anan Iran a shekara 03-Safar-370H.K. Ya fara karatu tun yana karami, yana matashi ya zama babban malami. Abu Ali Sina yak ware a cikin ilmomi masu yawa, wadanda suka hada da likitanci, farsafa da kuma taurari. Ya sami nasara warkar da dan sarki Mansur Samoni wanda ake kira Amir Nooh, daga nan sarkin ya bashi damar shiga dakin ajiye littafansa. Anan ne Abu Ali ya karanci littafaida bai isa ya samesu ba sai a wurin. Wannan ya daga matsayin ilminsa har sai da ya zama babu wadanda za’a kwantantashi da shi a zamaninsa. Abu Ali ya rubuta littafai da dama a fanoni da dama daga cikinsu akwai Kanun kan likatanci. Ya rasu a garin Hamedan a nan kasar Iran inda kabarinsa yake a halin yanzu yana dan shekara 58 a duniya.

==========================================================

Yau Litinin 02-Sharivar-1394H.sH=09-Zulkada-1436H.K.=24-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1042 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Zulkida-394H.K. aka haifi Nasir Khusru daya daga cikin fitattun marubutan wakoki a nan Iran a garin Balkh dake kasar Afganistan a halin yanzu. Ya soma karatu tun yana karami. Da farko ya shiga harkokin siyasa, amma bayan ya sami sauyin tunani sai ya kama hanyar karatu, inda ya zagaya kasashen gabas yammacin Asia da dama, ya kuma sami karatu a fannonin ilmi masu yawa. Mafi muhimmanci daga cikin littafan da Nasir Khusru ya rubuta shi ne “Safar Nome” inda ya kawo tarihi da sifar wasu kasashen Asia ta yamma da ya zagaya, wannan littafin yana da muhimmanci a wajen malaman sanin kasashe ko mutane. Hakim Nasir Khusru ya rasu yana dan shekara 87 a duniya a shekara ta 481H.K.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 86 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Augusta-1929M. Aka fara wani bori wanda ake kira borin “katangar Nadba” a kasar Palasdinu, a lokacinda turawan ingila yan mulkin mallaka suke kokarin mamaye kasar. Katangar Nadba dai wanda yake yamma da masallacin alaqsa, yana da muhimmanci ga musulmi don a nan ne manzon Al..(s) ya yi miraji zuwa sama a daren da ya yi isra da miraj. Kafin palasdinawa su fara wannan borin dai yahudawan sahyoniyya wadanda turawan ingila suka fara dawo da su Palasdinu sun fara keta hurumin wurin, wanda ya kai ga musulmin kasar suka bayyana fushinsu kan hakan. Turawan da kuma yahudawan sun yiwa musulman falasdinu kisan kiyashi wanda ya kai daruruwa a duk fadain kasar sannan sun kama wasu 800 suka gurfanar da su a wata kotu ta musamman inda suka jefa da dama daga cikinsu cikin kurkuku.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-shahrivar-1357H.SH. Hujjatul Islam Sayyeed Ali Andarzagu daya daya cikin malaman addini masu gwagwarmaya da gwamnatin sarki sha yakai ga shahada a hannnun jami’an tsaron sarkin. Sayyeed Ali ya fara gwagwarmaya ne tun yana dan shekara 18 tare da shaheed Nuwwab safawi. Yana daga cikin wadanda suka halaka Priministan kasar Iran Husain Ali Mansur, wanda ya samar da dokar capitalasion wacce ta bawa Amurkawa ba zauna iran kariya na gurfana a gaban kotu a iran bisa duk laifin da suka aikata. Har’ila yau shine ya kori Imam Khomaini (q) daga kasar Iran. Tun bayan kisan ne jami’an tsaron sarkin suke nemansa, amma basu same shi ba sai bayan shekaru 13, inda suka kashe shi a wani musayar wuta da shi a wata unguwa a nan Tehran.

==========================================================================.

Yau Talata 03-shahrivar-1394H.SH=10-Zulkida-1436H.K.=25-Augustan-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 920 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-August-1095M. Aka fara jerin yake yaken da ake kira “salibiyya” a kasar Palasdinu. Yake yaken wadanda kiristoci daga kasashen turai suka fara yana da nufin mamayar birnin Qudus da kuma daga baya sauran kasashen musulmi. Bayan shekaru 4 da fara yakin kiristoci wadanda suke dauke da alamun Cross a riguna da tutocinsu sun sami nasarar mamayar birnin Qudus a shekara ta 1099M, kuma birnin ya ci gaba da kasancewa cikin ikonsu har zuwa shekara 1187, a lokacinda sarkin masar na lokacin Salahuddeen Ayyubi ya sake dawo da shi karkashin ikon musulmi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 148 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Augudtan-1867M. Nichael Faraday, wani nasanin ilmin kimiyyar lissafi da na sinadarai dan kasar Ingila nya rasu. An haifi Faraday a shekara 1791M a binin London. Faraday bai da ilmi mai yawa a bangaren da yayi bincike a kansu, amma yana da kwazo wajen bincike, inda ya gano dokokin dabi’a wadanda suka shafi, kwararar wutan lantarki da kuma amfani da igiyar maganadisu don samar da kafi wanda ke jujjuya ingina. Banda haka Faraday ya gano wasu lamura a cikin kimiyyar sinadirai kuma masu muhimmanci, wadan nan abubuwan sun hada da abinda ake kira electrolises.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 74 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Sharivar-1320H.SH. A dai dai lokacinda ake cikin yakin duniya na biyu, sojojin kasashen Ingila da tarayyar Soviet sun mamaye kasar Iran. Bayan da kasashen da suka yi kawance a yakin, wato Ingila, Faransa, Tarayyar Soviet da kuma Amurka suka fahinci cewa sojojin Nazi suna samun nasara a yakin da suke yi da sojojin Tarayyar Soviet, wadan nan kasashe suka yanke shawarar mamayar kasar Iran don isar ta taimako ga tarayyar Soviet. A cikin kwanaki 20 da fara mamayar sojojin Kasashen Britania daga kudancin Iran, sannan na tarayyar Soviet daga gabaci da yammacin Iran sun hadu a birnin Tehran babban birnin kasar. Inda suka tube sarki Rida Pahalawi suka tilasta masa gudun hijira zuwa kasar Afrika ta kudu sannan suka dora dansa Muhammad Riza.

*****************************************************.

Yau Laraba 04-shahrivar-1394H.SH=11-Zulkida-1436H.K.=26-Augustan-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1288 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Zulkida-148H.K. Aka haifi Imam Aliyu bin Musa (a) wanda akewa lakabi da Imam Rida a garin Madina. Aliyu bin Musa (a) shi ne limami mai tsarki na 8 daga cikin limamai 12 daga cikin iyalan gidan manzon Al…(s). Ya gaji mahaifinsa Imam Musa (a) a shekara ta 183. A lokacinda Sarki Mamoon dan Haruna Rasheed daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya fahinci cewa Imam Rida (a) ne kadai barazana ga mulkinsa, sai ya ce wai ya bashi sarki mai jiran gadon sarautarsa, ya kuma tilasta masa kaura daga Madina zuwa maru mazaunan sarautarsa. Sai dai zaman Imam Rida (a) a Maru ya kara daukaka shi, ya kuma zama fitila wacce ta haskaka zukatan mutanen yankin kan matsayin iyalan gidan manzon Al…(a) a cikin al-ummarsa. Daga karshe Sarki Ma’amoon ya kasa hakuri da irin daukakar da Imam yake kara samu a duk ranar Al..sai ya kasheshi a shekara ta 203 H.K. a halin yanzu habbarensa yana birnin Mashad na kasar Iran inda miliyoyin masoya iyalan gadin manzon Al.. daga duk fadin duniya suke ziyartarsa. Muna taya al-ummar musulmi murnain ranar haihuwar tauraro na 8 daga cikin iyalan gidan manzon Al..(s).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1100 da suka gabata a rana irin ta uai wato 11-Zulkida-336M. Aka haifi Muhammad bin Muhammad wanda ake wa lakabi da sheikh Al-Mufid a birnin Bagdaza na kasar Iraqi. Sheikh al-mufid ya tashi a cikin gida ta malanta don haka ya tashi a cikin karatu. Bayan ya kamala kararu ya soma karantarwa, da kuma munazara da mutane kan ilmin da addinai. anan ya fahintar da mutane da dama addininsu da kgay . Sheilh al-mufid ya rubuta littafai sun kai 200 amma mafi muhimmanci daga cikinsu suke «الارشاد»، «الارکان» و «اصول الفقه»

Manya manyan malamai kamar su Sheikh Tusi, Sayyedd Murtada da sayyeed radi duk sun yi karatu a wajensa.

**Masu saurarko kun san cewa shekaru 119 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Augusta-1896M. Sojojin daular usmaniyyya alokacin sun fara wani kisan kiyashi na kabilar armeniyawa a yankin Armenia. Dalilan da sarakunan daular usmaniya suka bayar da kisan kiyashin shi ne wai armeniyawan sun tainakwa kabilar girka wadanda suke kokarin ballewa daga daular ta usmaniyya. Kisan kiyashin wanda mafi yawa ya shafi mata da yara ne ya dauki kwanaki biyar cur sojojin daular usmania suna aiwatar da shi.

============================================================================.

Yau Alhamis-05-Shahrivar-1394H.SH=12-Zulkida-1436H.K.=27-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau 27-August-1745M. Reynold Alleyne Nicholson wani baturen Ingila masanin kasashen musulmi ya rasu.

An haifi Nicholson a shekara ta 1968 a kasar Ingila. Bayan ya kammala karatunsa a jami’ar Cambrage ya fara karantarwa a jami’ar a matsayin malamin adabi. Nicholson, ya koyi harshen farasanci ya kuma karanta littafai Maulawi da wasu malaman na tsawon shekaru 25, sannan ya tarjama littafansu da dama zuwa harshen turanci. Littafan da ya tarjama dai sun hada da

. «تصحیح تذکره الاولیاء» da «تاریخ ادبیات عرب».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Sharivar-1357H.SH. An sake maida tarihin hijirar All..ta shamsiyya wanda gwamnatin sarki sha ta maida shi zuwa na nadin saratar daya daga cikin tsoffin sarakunan iran kafin Musulunci. Afarkon shekara ta 1355 ne sarkin ya bukaci majalisar mutanen kasar Iran su maida tarihin kasar zuwa lokacin nadin sarautar Sarki Kaurash na daular hakhamnishawa. Amma imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a lokacin da kuma mutanen kasar Musulmin sun nuna rashin amincewarsu da hakan da tsanani. Wannan ya tilsatawa sarkin dawowa, bayan kimanin shekara biyu sauya tarihin , sake maida shi kamar yadda yake a da wato zuwa hijirar manzon Al..(s) shamsiyya.

**Masu sauraro ko kun san cewa , yau ce 05-Shahrivar ranar da aka ware don girmama babban malami kuma masanin ilmin likitanci Muhammad Zakariyya Razi. An haidi zakariyya razi a garin Rai kusa da nan birnin Tehran, ya fara aikin kira tun yana matashi, amma bayanda ya sami matsala da idanunsa sanasiyyar hayaki, ya bar aikin bayan ya sake samun lafiyar idanunsa. Daga nan ne zakariyya Razi ya fara karatun likitanci da kuma wasu ilmomin. A cikin yan shekaru kadan ya zama korerren likita wanda babu kamarsa a duniyar musulmi. Kafin ya rasu ya rubuta littafai a fannoni da dama, wadanda yawansu ya kai 184. Daga cikin ci gaban da ya samar a fannin kimiyyar sinadoyar akwai ruwan Sulfuric acid.

========================================================================

Yau Jumma’a-06-Shahrivar-1394H.SH=13-Zulkida-1436H.K.=28-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 58 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Augudta-1957M. Wani masanin a kasar Rasha yak era ya kuma cilla makamin linzmi mai keta nahiyoyi. Watanni 4 bayan haka , wato a ranar 2-Octoba-1957M ya cilla tauraron dan adam na farko . Sannan ya bayyana cewa a cikin kasa da shekaru 3 zasu aike da mutum zuwa doron wata.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Shahrivar-1363H.SH. Allamah Khalidi daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya rasu. An haifi Allah Khalidi a karshen karni na 13 H.SH a kauyen Olmoni na lardin Marovan. bayan kammala karatunsa na sharar fage ya koma kasar Iraqi da zama inda ya kara fadada karatunsa a gaban mana manyan malamai na lokacin. Amma a shekara ta 1335 ya dawo kasar Iran da zama inda ya ci gaba da karantarwa a garin Nee. Allah Khalidi ya ci gaba da karantarwa har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Augusta-1993M. Shugaban kungiyar kwatar yencin Palasdinawa Yasar Arafat da kuma Priministan HKI Ishak Rabin sun rattaba hanni kan wata yerjejeniyar sulhu da kuma dakatar da bude wuta a gaban shugaban kasar Amurka na lokacin Bill Clinton. A cikin yerjejeniyar dai a karon farko bayan kafuwar HKI PLO ta amince da sanuwar HKI a yayinda Rabin yay i alkawalin mika ikon wasu sassa na yankunan Palasdinawa da ta mamaye ga Palasdinawa. An samu rashin yarda da kuma tuhuma da ha’inci a cikin mabiya bangarorin biyu. Inda palasduna suna ganin Arafat yay i ha’inci, a yayinda wasu yahudawa suke ganin Rabin yay i ha’inci. Amma duk da haka HKI bata ciki alkawarinta ba , don ta ci gaba da kai hare hare da mamayar karin yankunan Palasdinawa.

============================================================================.

Yau Asabar 07-Shahrivar-1394H.SH=14-Zulkida-1436H.K.=29-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Augusta-1949M. Tarayyar Soviet , a boye ta gwada makaminta na Nukliya na farko. Wannan ya sanya aka samu daidaito mai ban tsaro takanin kasashen Amurka da ita tarayyar Soviet. Don sanadiyyar wannan gwajin kasashen biyu suka fara haharan juna ko wace kasa tana jin tsorim kada dayar tayi amfani da makamin nuklia a kanta. Wannan halin a kalmomin yan siyasa shi ne yakin cacan baki. Wannan halin ya ci gaba a duniya har zuwa faduwa tarayyar soviet a shekara 1991. Sai dai duk da haka tsoron amfani da makaman nucliya a kan mutane bai kauba a duniya. Don kasashe irin su Amurka da HKI suna barazanar amfani da nuclea kan wasu kasashen da basa dasawa da su a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-shahrivar-1331H.SH. Aya. Sayyeed Muhammad Taqi Khunsari daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An haifi Aya. Khunsari a shekara ta 1267H.SH a garin Khunsar a nan tsakiyar kasar Iran. Ya tashi da fara karatu a mahaifarsa. Daga karshe ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatun. Aya. Khunsari ya shiga hannun turawan ingila a lokacinda suka so mamayar kasar Iraqi a shekara 1920. Bayan haka sun tilasta masa gudun hijira zuwa kasar Philipine na tsawon shekaru hudu daga nan ya dawo iran ya ci gaba da karantarwa da kuma gwagwarmaya da sarakunan kasar Iran. da kuma turawan da suke aiki tare da su.

***Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-shahrivar-1369H.SH. Aya. Uzma Sayyeed Shihabuddeen Mar’ashi Najafi daya daga cikin fitattu malaman addini ya rasu yana dan shekara 96 a duniya.

Aya Najafi ya kammala karatunsa ne a gaban manya manyan malamai na zamaninsa a biranen Kazimiyya da kuma Nafa. Bayan haka Aya. Ha’iri yazdi ya bukace shi ya dawo Qum da zama. Anan qum bayan karantarwa da kuma rubuc e rubuce ya samarda wani dakin ajiye littafai wanda babu irinsa a nan kusa. Dakin kittafan yana da littafi kimani 300,000 . Banda haka Aya. Najafi yana daga cikin nmalaman addinin da suka fi bada goyon bayan ga Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

==========================================================================.

Yau Lahadi 08-Shahrivar-1394H.SH=15-Zulkida-1436H.K.=30-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau 08-Shahrivar wacce a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran aka ware don yaki da ta’addanci. An wari wannan rana da wannan suna ne don abin yan ta’adda suka yi na kai hari da kashe shugaban kasar Iran na lokacin Dr Ali Rajai, da kuma Priministansa Sheikh Mohammad Javad Bohunar. Shekararu 34 da suka gabata ne munafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran , masu samun goyon bayan kasashen yamma har’ila yau wadanda suke riya cewa suna son tsarin Denocdiya sun dana bom a ofishin Priminista Bohunar suka kaisy ga shafa. Kafin haka Shahida Dr Ali Rajai ya kasance malami ne a jami’a ne kuma mai gwagwarmaya da azzaluman sarakunan Iran , inda ya sha wahala a hannunsu, har zuwa nasara. Bayan haka ya zama ministan ilmi sannan dan majalisa, sannan Priminister daga karshe aka zab shi shugaban kasa. Anan ne ya zabi sheikh Jawad Bohunar wadanda suka dade suna gwagwarmaya tare. Bai dade da kama aikin shugaban kasa ba munafukai suka tada bom a ofishin Priminister wanda ya kaisu ga shahada .Bayan shahadarsu Imam Khomaini (q) yana fada dangane da su cewa, martabansu shi ne, suna tare da mutane…

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 144 da suka gabata a rana irin ta ayau 30-Augusta-1871M. Aka haifi Emest Rutherford wanda aka fi saninsa na aban ilmin kimiyar lissafi da atom dan kasar Britania. Bayan ya kammala karatunsa a mahaifarsa New Zealand ya shiga Jami’ar Cambrage. Kafin shekara 1919 ya zama malamin ilmin physics ko kimiyyar lissafi a jami’ar. Binciken da Emest Rutherford ya yi a wannan fagen ya zama harsashen ci gaban ilmi so sai, kuma don irin kwazonsa a wanan fagen ya karbi kyautar Nobel. Mafi muhimmanci a cikin ayyukan Rutherford shi ne gano tsarin ginin kwayar atom da kuma hasken da ake kira radioactive. Rutherford ya rasu a shekara ta 1937 yana dan shekara 66 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 108 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-shahrivar-1286H.SH. Kasashen Rasha da Britania suka rattaba hannu kan yerjejeniyar raba kasar Iran a tsakaninsu. Wannan ya faru ne a lokacin sarki Muhammad Ali Sha Kajaar. Yerjejeniyar ta mallakawar kasar Rasha arewa da kuma wani sashe na yammacin Iran, sannan Britania kuma kudancin kasar, har’ila ya ta bar tsakiyar kasar a sake ba wani da cikinsu da zai shiga. Wani abin ban takaici da wannan yerjejeniyar shi ne wadan nan mulkin mallakan basu ma shawarci sarki Muhd Ali ba don rauninsa. Sai dai duk tare da rashin amincewa da wannan yerjejeniyar wanda majalisar dokokin kasar Iran taye, kasashen biyu sun mamaye wadan nan yankuna da karfin makamai. Wannan halin ya ci gaba har zuwa juyiyin juya halin kasar Rasha a shekara 1917 wanda ya kawo yanayin nda mutanen kasar Iran suka tilastawa kasashen biyu ficewa daga kasarsu.

========================================================

Yau Litinin 09-Shahrivar-1394H.SH=16-Zulkida-1436H.K.=31-Augusta-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 58 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Augusta-1957M. Kasar Malasia ta sami encin kanta daga hannun turawan Ingila. Kafin haka dai Musulunci ya shiga kasar Malasia tun karni na 13M. sannan turawan Potigal suka fara takar kasar a karni na 16M. Sai kuma a cikin karni 18 turawan Holanda suka mamaye kasar, sannan daga baya, a wata yerjejeniya tsakaninsu da turawan Ingila, Malasia ta koma karkashin mallakar turawan Ingila a yayinda Indonasia ta koma karkashin mallakar Holand. Wannan halin ya ci gaba har zuwa samun encin kai a rana irin ta yau. Malasia tana da fadin kasa kilomita murabbaee dubu 330 kuma tana makobtaka da kasashen Tailand da kuma Indonasia.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Augusta-1978M. Jagoran al-umma shia kuma malamin addini dan siyasa a kasar Lebanon Imam Musa Sadar ya yi batan ba zata a kasar Libya a lokacinda yake ziyarar kasar bisa gayyatar shugaban kasar Libya na lokacin Mu’ammar Kazzafi. An haifi Imam Musa a birnin Qum na kasar Iran, kuma a can da kuma kasar Iraqi ya kammala karatunsa sannan koma kasar Lebanon da zama, inda ya same yan shia a lokacin cikin mummunan hali ta ko ina. Sai ya kama majalisar malaman shi ne wacce tare da kokarinsa gwamnatin kasar Lebanon ta amince da samuwarta. sannan ya kama kungiyar bada agaji ta “Mahrumin” wacce ta taimaka wajen kyautatta yanayin tattalinn arzikin musulman kasar. Har’ila yau Imam Musa sadar yana goyon bayan al-ummar Palasdinu a gwagwarmayan da suke yi da HKI. Duk wani kokaro da aka yin a gano yadda aka yi da Imam Musa a kasar Libya , haka bai cimma ruwa ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 10 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Augusta-2005M. Kimani mutanen kasar Iraqi, mabiya mazhabar shia 1000 guda ne suka rasu sanadiyyar tattakesu da wasu suka yi da kuma faduwar wasunsu daga saman gadar da ratsa kan kogin Dijala a birnin Bagdaza. Mabiya mazahabar shia kimani miliyon guda ne suke makokin shahadar Imam Musal Kazim (a) limami na 7 daga cikin limamai 12 , sai suka ji tashin boma bomai a wasu wurare daga nan wadanda suka kan gadan suka tsorata suka yi ta tattaka juna suka kuma ture wasu suka fada cikin ruwan gogin suka mutu. A lokacin dai Amurka da Britania suna mamaye da kasar ta Iraqi.

============================================================================.

Yau Talata 10-shahrivar-1394H.SH=17-Zulkida-1436H.K=01-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1257 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Zulkida-179H.K. Sarki Haruna Rasheed daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilastawa Imam Musa bin Jaafar (a) yin hijira daga Madina zuwa birnin Bagdaza mazaunin mulkinsa. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa Imam Musa (a) ya shiga birnin Bagdaza a ranar 07-Zulkida -179H.K. daga nan kuma sai sarkin ya bada shi ajiya a gidan kurkukun Isa dan Jaafar hakimin Basra , amma sai Isa ya rubutawa sarkin wasika inda a cikinta yake neman sarki Haruna Rashees ya dauke shi zuwa wani kurkukun don shi ba zai iya tsare shia don ganin rashin dacewar haka ga wanda bai yi wani laifi ba. Daga nan ne sarki Haruna ya bukaci a canza masa mazauni. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekaru 15 inda ya umurci wazirinsa Fadle bin Rabee ya kashe Imam (a). A sannan ne Fadle bin Rabee bukaci Sindy bin Shaaheq mai tsaron gidan yarin da ake tsari da Imam Musa (a) ya aiwatar da umurnin Sarkin. Shaahiq ya aiwatar da wannan umurnin ne tare da kula na Yahyah Barmaky shugaban fadawar sarki Harun shima.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 841 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Satumba-1174M. Aka fara ginin hasumiyya ko dogon gin mai suna Pisa a birnin Pisa na kasar Italia. Manufar gina wannan hasumiyya shi ne dora wani katoton agogo a kansa. Hasimiyyar dai tana da tsawon mit 55, amma ginin ya dan karkata a tsawon mita 5 daga doron kasa wannan ya sa ake kiransa karkataccen Hasumiyyar pisa. Masana gine gine daga kasashen duniya da dama ne aka kawo don gyara wanna kuskuren. Sun kuma sami nasarar gyararsa da kuma kammala ginin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 81 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-zulkida-1355H.H. Aya. Abdulkarin Ha’iri Yazdi, babban malamin addini kuma marjaee ya rasu a nan Iran. An haifi Aya. Yazdi a garin Yazd na nan tsakiyar Iran. Ya fara karatu a mahaifarsa. Daga baya ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na wancan lokacin. Bayan kammala karatunsa a dawo nan kasar Iran inda a shekara ta 1340H.K. ya kafa makarantar hauza ta ilmantar da dalimai ya kuma ci gaba da karantarwa. Mafi muhimmanci daga cikin dalibansa dai sun hada da Imam Ruhullah Al-khumaini (q) wanda ya assasa JMI. Banda haka Aya. Ha’iri yazdi ya rubuta littafai wadanda suka hada da کتاب الرضا»، «کتاب الصلاه» و «کتاب المواریث».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 50 da suka gabata a ran airin ta yau wato 10- Shahrivar-1344H.SH aka kafa komiti na farko wanda zai fara aikin duba yiyuwan kasar Iran ta amfanu da makamashin nuclear. Wannan komitin ne dai ya sayi wata na’ura ta farko na bincike kan amfani da makamashin nuklia a kasar Iran daga kasar Amurka aka kuma kafata a nan birnin Tehran.

Ayyukan wannan na’ura ta makamshin nukliya dais hi ne yin magunguna da bincike kan cututtuka masu sarkakiya. Na’urar tana daga karfin megawatt 5 kuma kasar Amurka da wasu kasashen Turai ne suke samar da makamashin da ake bukata don amfanin na’urar. Banda haka wannan komin ya cimma yerjejeniya da wasu kamfanin makamacin nuclear guda biyu a kasashen turai na gina cibiyar saman da wutan lantarki na farko a garin Bushar na bakin ruwa a kudancin kasar Iran. Sai dai duk haka, bayan samun nasarar juyin juya halim muslunci a kasar Iran a shekara 1979M wadan nan kasashe sun juya wa kasar baya sun kuma ki cika alkawarin da suka yi na gina wadan nan wurare. Wannan halin ya cika gaba har zuwa lokacinda iraniyawa kansu suka dauki nauyin samarwa kasu mafita da kansu inda a lokacin mulkin shugaba Ahmadi Najad kasar ta sami fasahar sarrafa makamacin Nuklia har zuwa kashi 20.

**************************************

Yau Laraba 11-shahrivar-1394H.SH=18-Zulkida-1436H.K=02-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Septemba-1945M. Kasar Japan ta mika kai ga kasashen kawance a yakin duniya na biyu. Japan ta mika kai ga wadan nan kasashe ne bayan da Amurka tayi ruwan boma boman Nuklia kan biranen Hiroshima da kuma Nagasaki na kasar a cikin watan Augusta na wancan shekarar. Sannan hakan ya faru ne watannun 4 da mika kai da kasar Jamus ta yi ga wadan nan kasashe. A bisa yerjejeniyar Postadam na kasar Jamus wadan nan kasashe sun mamaye kasar Japan sun kuma dora General mark Ortoor wani komandan sojojin Amurka a matsayin shugaban kasar Japan har zuwa shekara 1951 a lokacinda kasar Japan ta rattaba hannu kan wata yerjejejniyar sulhu da zaman lafiya da kasashe 49 a duniya sannan aka mika mata encin kanta.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Zulkida-1373H.K. Aya. Sheikh Muhammad Husain Kashifulgida , daya daga cikin manya manyan malaman addini a kasar Iraqi ya rasu. An jaife shi a kasar Iraqi ya kuma tashi da karatu a gidan iyayensa. Sannan ya shiga karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa. Aya. Kashiful gida, ya tashi da fahintar gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin, don haka yana daga cikin malaman da suka yi gwagwarmaya da mamayar turawan Ingila kasar Iraqi. Banda karantarwa Aya. Kashifulgida ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai diwanin wakokinsa da kuma «الفردوس الاعلی»، «الآیات البینات» و «السیاست الحسینیه».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a ran airin ta yau wato 19-Shahrivar-1341H.SH. An yi wata girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 7.2 a garin- Bu’ine Zahra- da ke arewa maso yammacin kasar iran. Girgizar kasar dai ta auku ne cikin tsakiyar dare, kuma ta shafi kauyuka kimani 120 a yankin. Mutane kimani dubu 20 ne suka rasa rayukansu a yayinda wasu dubbai suka ji rauni banda haka girgizan kasar ta daidaita daruruwan gidaje da kasa.

Yankin -Bu’ine Zahrah- dai ya saba da irin wadan nan girgizan kasa a baya , don a shekara ta 1381 ma an yi irin wannan girgizan kasar wanda ya kai ga mutuwar mutane 300.

======================

Yau Alhamis 12-shahrivar-1394H.SH=19-Zulkida-1436H.K=03-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 357 da suka gabata a rana irin ta yau wato a rana irin ta yau wato 03-Satumba-1658M. Olover Cromwell shugaban kasar Ingila na farko kuma na karshe ya rasu. Cromwell ya shiga majalisar dokokin kasar Ingila ne a shekara ta 1940. Sannan a lokacin akwai sabani mai tsanani tsakanin majalisar da sarki Charles na farko. Daga nan sai Cromwell ya tattara mayaka ya shiga yakar sarkin da suna majalisar dokokin kasar bayan samun nasara a cikin watannin 6, ya kama sarkin ya kashe. Sai ya kauda tsarin sarauta ya kuma nada kansa shugaban kasar. Shugabancinsa bai kai shekaru 10 ba sai yamuta dansa mai suna Richard ya gajeshi a ranar 3-Satumba-1658, amma aka sake komawa yakin basasa a tsakanin yankunan whiles , Scotland da Ingila. Bayan watannin 8. Richard ya sauka sai Cherles na 2 ya nada kansa sarki ya maida tsarin saraunta a kasar Ingila.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 100 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Sharivar-1294H.SH. Ra’ees-Ali Delworee shugaba masu gwagwarmaya da mamayar turawan ingila a kudancin kasar Iran yay i shahada. A dai dai lokacinda ake yakin duniya na daya, kasashen Rasha da Ingila suka farwa kasar Iran da yaki. Inda turawan Ingila suka bullo ta kudu sai kuma Rasha ta bullo ta arewa. Daga gabas Ra’ees Ali yay i amfani da fatawar jihadin kariya wanda malaman addini na lokacin suka bayan ya tattara mutanen yankin Bushar ya hana turawan shiga kasar Iran har na tsawon shekaru 8. Sannan suka kashe shi a ran airin ta yau.

**Masu sauraro ko kun sa cewa shekaru 97 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Satumba-1918M. Birnin Damuscas fadar mulkin kasar Syria ya fada karkashin turawan ingila yan mulkin mallaka. Kafin haka dai dama turawa sun dade suna dakon faduwar daular Usmaniyya wacce take iko da kasashen musulmi da dama. Don haka bayan faduwarta sun yi watandar yankunan a tsakaninsu, inda kasar Syria ta fada cikin rabon kasar Faransa, amma a rana irin ta yau sojojin ingila suka mamaye birnin Damuscas suka shimfada ikonsu a cikinsa. Dai dai daga karshe a dole ta mikawa faransa kasar kamar yadda suka tsara a can bayan.

====================================================================.

Yau jumma’a 13-shahrivar-1394H.SH=20-Zulkida-1436H.K.=04-Septemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 13 ga watan shahrivar ranar girmama Abu Raihan Muhammad bin Ahmad Khawarizmi biruni, daya daga cikin fitattun malaman addini da wasu fannonin ilmi a zamaninsa. An haifi Abu Raihan a garin Birun da ke cikin kasar Uzbekistan a halin yanzu a shekara ta 362 H.K. ya sarrafa shekaru 25 na farko a rayuwarsa yana karatu a garin Khawarizmi daga baya ya koma Buhara da zama inda sarakunan Samoniyawa daga nan ya je kasar India inda ya hada da malamai da dama ya kuma amfana da su. Abu raihan ya rubuta littafai a fannonin ilmi daban daban wadanda suka kai 160. Ya hada zamani da abu Ali Sina inda suka yi musayar wasiku da shi kan ilmi. Daga karshe Abu raihan ya rasu a garin Gazni na kasar Afganisatan a halin yanzu a shekara 440 H.K. yana dan shekara 78 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 133 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Satumba-1882M. Adison wani injinia dan kasar Amurka yak ire ingin bada wutan lantarki na farko a duniya. Edison ya kirkiro inji mai bada wutan lantarki wanda yake da karfin doki 300 kuma da shi ne ya bada wutan lantarki wanda ya haskaka wani sashe na birnn Newyork a kasar Amurka. Har’ila yau Edison ne ya kirkiro bull na wutan lantarki a shekara ta 1879M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Shahrivar-1357H.SH. An gudanar da zanga zanga wanda ya tara miliyoyin mutanen kasar Iran a karon farko a birnin Tehran. Zanga zanga wanda aka faro ta a masallacin idi bayan sallar idin azumi, masu zanga zanga suna dauke katoton hoton Imam Khomanini (q) wanda ya assasa JMI suna rera taken muna son enci muna son jumhuriyya Islamiyya. Bayan haka an gudanar da zangzanga zanga makamancinsa a ranar 18 ga watan wanda shima ya tara miliyoyin mutane. Daga nana har zuwa nasara juyin musulunci a cikin watan Bahman na wancan shekarar.

==================================================================

Yau Asabar 14-shahrivar-1394H.SH=21-Zulkida-1436H.K.=05-Septemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Zulkida-1377H.K. Aya. Sayyeed Yunus Ardabili daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An haifeshi a shekara ta 1293 a garin Ardabil a nan Iran ya kammala karatun sharer fage a nan Iran sannan ya kama hanyar kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai a birnin Najaf da karbala. Sai kuma a shekara ta 1346 H.K. ya dawo gida ya fara karantarwa. Daga nan ya je birnin Mashad inda ya shaidi irin kisan da aka yiwa mutane a masallacin gauharshod. A nan ne aka kama shi aka kuma tilasta masa gudun hijira. Daga karshe Aya. Sayyeed Yunus Ardabila ua rasu a nan Tehran yana dan shekara 84 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Shahrivar-1360H.SH. Aya. Ali Kuddusi babban mai gabatar da kara na juyin juya halin musulunci a Iran yay i shahada sanadiyar tashin wani bom wanda munafukai makiya JMI suka tayar a nan Tehran. Aya. Kuddusi ya kammala karatunsa ne a gaban manya manyan malaman hauza na lokacin wadanda suka hada da Aya. Burujadi da kuma Imam Khomaini(q). Sannan sanadiyyar gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin kasar Iran a lokacin ya gudanar da wani bangare na rayuwarsa a gidan yari. Sannan bayan samun nasara juyin musulunci a nan Iran Imam Khomani(q)ya nada shi babban mai gabatar da kara na juyin juya halin musulunci. Yana cikin wannan aikin ne munafukai suka kais hi ga shahada a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Satumba-1993M. Aka bude wani masallaci mafi girma a duniya bayan na Makka da madina a garin Casablanca na kasar Morocco. Masallacin mai suna darul baida yana da fadin gaskiya kuma yana da dakin ajiyar littafai mai girma da makarantar addini . Wani abin lura a cikin wannan masallacin shi ne rufinsa ana budewa a sake rufewa. Sannan an kawata shi da zane zanen musulunci daban daban.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Sharivar-1379H.SH. Aya. Dr Sayyeed Murtada Aya. Zade shirazi ya rasu. An haifeshi a garin Najaf na kasar Iraqi a shekara ta 1307. Bayan kammala karatun hauza ya shiga jami’an Tehran inda yi digiri na farko, sannan ya sami shaidar doktora a harshen larabci a jami’ar alazhar ta kasar Masar. Sannan ya karantar da harshen farisance na wani lokaci a jami’ar. Aya. Shirazi ya rubuta littafai wadanda suka hada da kamus da kuma tarjamar wasu littafan. Daga karshe Aya shirazi ya rasu a shekara 1379 H.SH yana dan shekara 72 a duniya.

=====================================.

Yau Lahadi 15-Shahrivar-1394H.SH=22-Zulkida-1436H.=06-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 50 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Satumba-1965M. bayan tashe tashen hankula na kimani wata guda a kan iyakokin kasashen India da Pakistan sojojin kasar India sun fara kai hare hare a cikin kasar Pakistan, hare haren dai sune masomin yaki na biyu tsakanin India da Pakistan kan mallakar yankin Kashmir. Kasashen sun dau makonni ukku scur suna yakin. Priministan kasar tarayyar Soviet na lokacin ne ya shiga tsakani, inda a ranar 10-Jenerun-1966M kasashen biyu suka amince da shirin tsagaita bude wuta, suka kuma bayyana hanyoyin warware rikicin yankin na Kashmir. Sai dai duk da haka har yanzun ba’a warware rikicin ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 41 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Shahrivar-1353H.SH. Aya. Sayyeed Muhmood Husain Shahrudi babban marja’in shia ya rasu. An haife shi a garin Bistam a arewa maso gabcin kasar Iran. Ya fara karatun addini a mahaifarsa. Sanna ya kammala karatunsa a biranen Mashad na kasar Iran da kuma Najaf na kasar Iraqi. Bayan wani lokaci ya zama marja’I babba na duniayr shia. Aya. Shahrudi ya raya sunna mai kyau na tattaki zuwa karbala bayan mutuwarsa na wani lokaci . Sannan yana da risala kan fikihun hajji da kuma na ijara ko haya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Shahrivar-1357H.SH. A dai dai lokacinda juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya kusan kaiwa ga nasara, sannan zanga zangar mutanen kasar Iran na bukatar kauda sarautar sarki shay a yadu zuwa ko ina a kasar sarkin ya kafa dokar hana zanga zanga. Amma a dai dai lokacin ne Imam Khomani (q) wanda yake birnin Najaf na kasar Iraqi a lokacin ya bada sanarwan cewa mutane su fito zanga zanga har zuwa faduwar sarautar sarin.

=======================================================================.

Yau Litinin 16-Sharivar-1394H.SH=23-Zulkida-1436H.K.=07-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Sharivar-1363H.SH. Aya. Mohammad Baqir Oshtiyani daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu. An haife shi a nan Tehran a shekara 1284H.SH, kuma a nan ya fara karatunsa na sharar faga. Bayan wani lokaci ya gazgaya zuwa birnin Najaf na kasar Iran inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin. Bayan samun darajar Ijtihadi ya dawo nan Tehran inda ya ci gaba karantarwa da kuma rubuce rubuce. Aya. Mohammad Ostiyani ya rubuta littafai da dama daga cikindu akwai

«ارشاد از نظر اسلام»da harshen farisanci da kuma «مالکیت در اسلام»

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 18-07-Satumba-1997M. Tsohon shugaban kasar Congo dan kama karya Moboto Seseseko ya rasu. An haifi Moboto a shekara ta 1930M, yana dan shekara 20 a duniya ya kammala karatunsa ya kuma shiga kungiyar gwagwarmaya don samun encin kasarsa tare da su Patrick Lumumba. Bayan samun encin kai ya zama shugaban sojojin kasar Congo, sannan yana dan shekara 30 ya zama Priministan kasar sai kuma a ranar 25-Nuwamban-1965M Mobuto ya jagoranci juyin mulki wanda ya dorashi kan kujerar shugabancin kasar. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda aka fara tawaye a kasar a farkon gomiya 90 , daga karshe yan tawaye karkashin Lauran Kabila sun kore shi daga kasar a 16-Mayu-1997M. Ya arce zuwa kasar Morocco bayan mulki na tsawon shekaru 32 in ya rayu har mutuwarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Shahrivar-1382H.SH. Aya. Sayyees Husain Budala ya rasu yana dan shekara 96 a duniya. Aya. Budala ya fara karatu a gaban manya manyan malamai ma garin Qum inda ya fara da Aya. Sheikh Kasim Kabir Qum, Aya Ha’iri Yanzi , Aya. Muhammad Riza galpeyagani . Bayan kammala karatu ya fara karantarwa da kuma yada addini. Har’ila tare da hakan ya bude cibiyoyin yada addinin wadanda yake kula da su. A cikin wannan halin ya sarrafa rayuwarsa, har ya koma ga All…a rana irin ta yua.

===============================================

Yau Talata 17-Sharivar-1394H.SH=24-Zulkida-1436H.K.=08-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1236 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Zulkida-200H.K. Imam Aliyu bin Musa Al-riza (a) ya fara tafiyarsa daga madina zuwa Mari cibiyar mulkin sarki Mamoon na daular Abbasiyawa. Sarki Mamoon ya tilasta masa kaura zuwa Maru ya kuma tilasta masa karban matsayin waziri mai jiran gadon sarauta. Manufar sarkin shi ne sanya ido a cikin lamarun Imam Riza (a) da kuma karfafa mulkinsa tare da taimakonsa. Har’ila yau da kuma zubar da mutuncinsa a gaban mutane. Amma Imam Radz (a) yak i amincewa ya shiga cikin harkokin mulki don bai amince da halaccen sarautar ba. Sai dai duk da haka matsayin Imam Riza (a) sai ya daga karuwa a gaban mutane har ya kai ga sarkin ya kasa hakuri ya kashe shi a shekara ta 203H.K.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Shahrivar-1357H.SH. Aka gudanar da zanga zanga mafi girma a nan birnin Tehran na kasar Iran wanda kuma ya fuskanci dirar mikiya daga bangaren jami’an sojojin sarki sha. A lokacin dai sarkin ya kafa do ta baci, don sojojinsa sun yi ta kisan mutane babu kama hannun yaro. Yawan mutanen da suka kashe a ranar jummma’a 17-Shahrivar na wancan shekara sun kai akalla 4000 don haka shi ya sa ake kiran ranar da ranar shahidai. Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a birnin Najaf na kasar Iraqi a lokacin ya aike da sako inda yake cewa..ina ma da ace ina tare da kun a shiga cikin sahun shahidai, wannan ita ce hanyar Amirulmumina na Imam Husain(s) ya ku mutanen Iran ku san cewa ko ba dade ko bahima nasara tana tare da ku.

**Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 08-Satumba, ranar da hukumar UNESCO ta majalisar dinkin duniya ta ware ta bashi suna ranar –yaki da jahilci-Bisa rahoton hukumar UNESCO wasu kasashen duniya basu bada muhimmancin da ya dacewa harkar yaki da jahilci ba, duk da cewa da shi kadai ne kasashe zasu sami ci gaba, jahilci ne yake kawo talauci rashin lafiya da dukkan sharra. Anan Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci, Imam Khomaini (q) ya bada umurnin kafa hukumar yaki da jahilci a shekara 1358H.SH, don ganin addinin Musulunci ya kodaitar da ilmantar da mutane. A karkashin wannan shiri a halin yanzu kasar Iran ta fice daga jerin kasashe masu fama da tsananain jihalci.

================================================

Yau Laraba 18-Sharivar-1394H.SH=25-Zulkida-1436H.K.=09-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1426 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Zulkida-10H.K. Manzon Al..(s) ya fara tafiyarsa ta karshe zuwa aikin hajji, wanda kuma ya fi shahara da hajjin ban kwana. Don bayan sa da kadan ne ya bar wannan duniya. A lokacin dai yana tare da sahabbansa kimani dubu 100. Abubuwa mafi muhimmanci da suka fara a lokacin hajjin ban kwana dai sun hada da cewa manzon All…(s) ya nunawa musulmi yadda zasu gudanar da ayyukan ibada na hajji a Musulunci, sannan a karshen sa ya bayyanawa musulmi wanda zai gajeshi a bayansa a ranar 18-Zulhajji, inda tare da umurnin Al…ya nada Aliyu dan Abitalib a matsayin magajinsa khalifansa a bayansa. Yayi haka ne jim kadan bayan kammala aikin hajji a wani wuri da ake kira gadir Khum. Daga rannan zuwa rasuwan sa kwanaki 70 ne kacal.

**Masdu sauraro ko kun san cewa shekaru 39 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Satumba-1976M. Mao Zedong shugaban kasar China ya rasu. An haifi Mao a shekara ta 1893 sannan a shekara ta 1921tare da taimakon wasu abokansa suka kafa jam’iyyar gurguzu ta china. Sai kuma a shekara 1934M Mao ya jagoranci magoya bayan jam’iyyar gurguzu kimani dubu 100 wadanda mafi yawansu manoma ne, ya jagorancesu don nuna rashin amincewarsu da ayyukan sarakunan kasar. Inda suka tattaka daga kudancin kasar zuwa arewacin kasar inda mazaunin hukumar kasar take. Wannan tattakin ya daukisu shekara guda sannan mutane kimani dubu 60 ne suka rasa rayukansu a kan hanyar. Amma duk da haka Mao ya sami nasarar korar sarakunan kasar karkashin jagorancin Chayon ChayChek, ya kuma kafa tsarin gurguzu a china.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Satumba-2001M. Wasu yan kunan bakin wake wadanda suka yi shigan burtu da kayakin yan jaridu sun tarwatsa bom a yayinda suka hira da shugaban mujahidin kasar Afganistan Ahmad Sha Mas’ud sun kama kashe shi.

Kafin haka dai Ahmad Sha Mas’ud yana daga cikin komandojin sojojin mujahidin wadanda suka kore tarayyar Soviet daga kasar Afganistan a shekara 1989M bayan sun share shekaru 10 suna mamaye da kasar. Sannan bayan da Taliban wacce take samun goyon bayan Pakistan da Amurka suka sake kwace kasar Afgnaistan a 1994, Taliban sun kasa samun iko da yankin Pansheer na arewacin kasar wanda Mas’ud yake jagoranta har zuwa lokacinda suka aiki wadannan masu shigan burtu nay an jarida suka kashe shi. Bayan kisan mas’ud da kadan ne Amurka ta kawo karshen mulkin Taliban a Afganistan ta kuma mamaye kasar na tsawo shekaru 10 ita ma.

===========================================================================.

Yau Alhamis 19-Shahrivar-1394M=26-Zulkida-1436H.K.=10-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 61 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Satumba-1954M. Aka yi wata girgizan kasa mai karfi a kudu maso yammacin kasar Algeria. Gargizan kasar dai ba’a taba ganin irinsa a yankin bay a rusa wani gari mai yawan mutane dubu 30 ya daidaita shi da kasa. Banda haka girgizan kasar ta kashe mutane kimani dubu 10 ya kuma maida wasu dubban dadruruwan marasa gidaje. Banda haka girgizan kasar ta jawo asarorin dukiya mai yawa ga yankin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato19-Shahrivar- 1358H.SH. Aya Sayyeed Mahmood Taliqani daya daga cikin manya manyan malaman addini kuma limamin masallacin jumma’a na farko a nan Tehran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci ya rasu sanadiyyar bugun zuciya.

An haifi Aya. Talikani a shekara ta 1384 a garin Talikan a nan kasar Iran. Ya fahinci siyasar kasar Iran da duniya tun yana matashi. An daure shi shekaru 2 sanadiyyar shiga cikin zanga zangar 15-khurdod -1342H.SH. Bayan haka ma ya sha dauri da kora. Daga karshe a lokacin da juyin juya halin Musulunci ya sami nasara ya na daure mujahidin juyin ne suka sako shi daga kurkuku. Daga nan Imam Ya nadashi limanin masallacin jumma’a a Tehran na farko. Kuma an zabe shi cikin majalisar kwararru masu zaben jagora kafin rasuwarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a ran airin ta yau wato 19-Sharivar-1361H.SH. Aya. Diya’uddeen Amuli daya daga cikin manya manyan malaman addinin a nan Iran ya rasu. An haifi Aya. Amuli a shekara ta 1283H.SH a cikin gidan malanta. Yana karami mahaifinsa ya je da shi birnin Najaf na kasar Iraqi. Bayan kammala karatu ya dawo nan gida iran yana karantarwa. A wani lokaci shugaban hauza a nan birnin Qum Aya Burujadi ya sha aikarsa zuwa jami’an al-azhar na kasar Masar da nufin hukumomin jami’an su samar da daman a karantar da mazhabar iyalan gidan manzon Al…(s) a cikin jami’ar amma hakan bai yu ba don duk sanda ya je baya samun hadin kai daga shuwagabannon jami’ar. Daga karshe aka dakatar da zuwan har zuwa rasuwarsa.

=======================

Yau Jumma’a 20-Shahrivar-1394M=27-Zulkida-1436H.K.=11-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 67 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Satumba-1948M. Mohammad Ali Janah wanda ya assasa samuwar kasar Pakistan ya rasu. An haifi Ali Janah a shekara ta 1876M a birnin Karachi na kasar Pakistan. Ali Janah ne ya kafa kungiyar Muslim Leaque wacce ta fara da ayyukan ilmantarwa da kuma khidima wa mutane amma daga baya ta rikide ta zama jam’iyyar siyasa a shekara 1906M. A zaben majalisar dokokin da aka gudanar a kasar India kafin yakin duniya na biyu jam’iyyarsa ta sami nasar a dukkan yankunan da musulmi suka fi yawa a kasar. Sai kuma daga karshen bayan samun encin kan kasar India a shekara 1947M, a dai dai lokacin aka samar da kasar Pakistan mai musulmi zalla, kuma Ali Janah ya zama shugabanta.

**masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Shahrivar-1360H.SH. Aya. Sayyeed Asadullahi Madani, limamin masallacin jumma’a a garin Tabriz a nan kasar Iran ya yi shahada sandiyar harin da munafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kai masa a lokacinda yake bada sallar jumma’a a garin. An haife a shekara ta 1393H.SH. Ya yi karatunsa na addinin a birnin Najafa na nan Qum. Yana goyon bayan Imam Khomaini (q) a yunkurin ranar 15-Khurdod-1342H.SH don haka tun lokacin ya sha dauri a hannun jami’an sarki sha. Bayan nasarar juyin musuluni Imam ya bashi limancin sallar Jumma’a da wakilcinsa a garin Tabriz. Yana cikin wannan aikin ne manafukai suka kashe shi a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Satumban-2001M. Biyu daga cikin Jiragen fasinja guda hudu wadanda aka sace a filin sauka da tsahin jiragen sama na birnin Boston a kasar Amurka, sun Burma a cikin tawagar gine gine na cibiyar kasuwanci ta duniya dake birnin New York suka rusa gina ginen, na ukkunsu kuma ya Burma cikin ginin ma’aikatan tsaron Amurka –Pentagon- da ke birnin Washington wanda shi ma ya lalata wanim bangarensa sai kuma na hudun wanda aka kakkabe shi a sararin samaniyar dajin Pensovenis na kasar ta Amurka. Mutane kimanu 3200 suka mutu a wadan nann hare hare. Shugaban kasar Amurka na lokacin Geoge W Boosh ya zargi usmana bin Ladan shugaban kungiyar Alqaeda da laifin kai hare hare. Da wannan dalilin ne ya mamaye kasar Afgnaistan a cikin watan Octoba na shekarar sannan ya mamaye Iraqi a cikin watan maris na shekara ta 2003M. Da wannan musulmi a duk fadin duniya suka shiga halin kuntatawa a duk inda suke.

=========================================================

Yau Asabar 21-Shahrivar-1394M=28-Zulkida-1436H.K.=12-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1076 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Zulkida-360H.K. Abul-Qasim Tabrani daya daga cikin manya manyan malaman hadisi ya rasu a birnin Esfahan na nan kasar Iran. Tabrani ya shahara da sanin ilmin hadisi don haka ne ma ya dau shekaru 33 cur yana bincike da kuma tattara hadisan manzon Al…(s) daga kasashen musulmi daban daban. Bayan ya kammala yawace yawacen san a neman ilmi ya dawo birnin Esfahan a nan Irn inda ya ci gaba da bada ilmi. Ya kuma rubuta littafai a wannan fannin, wadanda suka hada da «معجم کبیر»، «معجم وسط» و «معجم صغیر».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 29 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-shahrivar-1365H.SH. Hafiz Mohammad Yusuf Sadidi, daya daga cikin malaman koyar da rubutu mai kyau ya rasu abirnin Lahor na kasar Pakistan. An haife shi a shekara ta 1920M . Yana dan shekara 19 a duniya ya fara koyon rubutu a gaban manya manyan malaman rubutu na kasar Pakistan wadanda suka hada da Muhammad Sharif Da kuma Tajuddeen Zarrin. Bayan korewarsa wajen aikin rubutu da zabe Sadidi ya rubuta wani littafi mai suna “Minyor Pakistan” wanda ya kawata shi da rubutunsa mai kyau kuma ya zama abin alfahari wanda aka ajiye a dakin ajiyar kayakin Tarihi na kasar Pakistan. Yana da wasu zane zanen da kuma rubutu masu kyau banda wannan.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 784 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Zulkida-652H.K. As’ad Bin Halawan Damashqi, wani kwararren likita dan kasar dan kasar Syria ya rasu. An haifi As’ad a shekara ta 593 H.K. Bayan kammala makarantar koyon aikin likita a zamaninsa ya zama kwararre kuma mashahurin likita a lokacin. Banda aikin likitanci As’ad yak ware ya kuma yi rubuce rubuce a fannin lissafi, Mandiq da kuma adabin larabci.

=======================================================.

Yau Lahadi 22-Shahrivar-1394M=29-Zulkida-1436H.K.=13-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 95 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Shahrivar-1299H.SH. Sheikh Muhammad Khiyabani daya daga cikin masu gwagwarmaya don samar da kundin tsarin mulki da ake kira Mashrudiyya a kasar Iran ya yi shahada. Bayan nasarar gwagwarmayan mashrudiyya a kasar Iran da kuma tube sarki Ali Kajaar daga kan kujerar sarautar kasar Iran Sheikh Khiyabani ya zama wakilin mutanen Tabriza a sabuwar majalisar kasa da aka kama. Amma bayan da ya gano cewa shishigin da kasashen waje, Kamar Ingila da Rasha suke yi a cikin harkokin mulkin kasar Iran sun hana kasar Samun cikekken encin da ta kamata, musamman amincewa da kudurin na 1919, khayabani ya tsaida shawarar yin tawaye ga sarakunan kasar Iran tare da tainakon mutanen Tabriz. Da haka kuma ya fara wani yunkuri na samarwa Iran cikekken enci amma a rana irin ta yau tare da kha’incin wasu abokansa aka kashe shi aka kuma kawo karshen tawayen na Tabriz.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-satumba-1959M. Jirgin jigilar yan sama jannati na farko mallakin kasar tarayyar Soviet ya sauka a kan doron wata. Jirgin mai suna Lunik2 ya sauka tare da dan sama jannati wanda ya gano cewa wata bata da karfin maganadisu kamar duniyar mu. Don haka babuwa wani karfi wanda yake jan abubuwa zuwa jikin wata. Sai dai a wani gwajin da aka gudanar daga baya ya nuna cewa wata tana da karfin maganadinsun a wasu wurare ne kadai. Kuma ko su din basa da karfi. Bincike ya nuna cewa wata tana da karfin maganadisu kamar na duniya fiye da shekaru miliyon 3 da suka gabata.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Satumba-1993M. Aka rattaba hannu kan yerjejeniyar sulhu tsakanin Palasdinawa da Yahudawan sahyoniyya mai suna yerjejeniyar Gaza –Ariha. A birnin washinton na kasar Amurka. A taron sulhun dai Yasar Arafat ya amince da samuwar HKI sannan yahudawan sun yi alkawarin janyewa daga yankunan larabawa da ta mamaye sannan a kafa kasar Palasdinu daga Gaza zuwa ariha a shekara ta 1999. Sannan za’a fara tattaunawa kan dawowan yan gudun hijira, dakatar da ginawa yahudawa a yankunan laabawa da kuma sakin fursinonin Palasdinu. Sai dai HKI bata cika ko da daya daga cikin alkawulan da ta dauka a wannan yerjejeniyar ba bayan kullata.

====================================================================.

Yau Litinin 23-Shahrivar-1394H.SH=30-Zulkida-1436H.K.=14-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1216 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Zulkida-220H.K. Imam Muhammad Taqee aljawad limani na 9 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All(s) yayi shahada. An haif shi a cikin watan Ramadan na shekara ta 195 H.K. Bayan shahadar mahaifinsa Imam Aliyu bin Musa arrida (a) ya karbi jagorancin al-ummar kakaknsa. A zamininsa ne daular Musulunci take cikin ci gaganta na kole, wajen yawa da kuma yaduwar ilmi daban daban . Don Imam Jawad (a) ya shagaltu da wayar da mutane kan sabbin ilmin da suka shiga al-ummar musulmi daga kasashen girka, Farisa da kuma india, wadanda wasunsu sun sabawa ikidi da al’adar Musulunci. Don sau da dama yak an shirya muhawara da malamai masana kan lamura na wayar da kai. Amma wannan ya sanya an sanshi a ko ina kuma sarakunan Abbasiyawa a lokacin suna ganin yana iya zama barazana da mulkin, wanda ya kai ga sarki Mutasim billah ya sanya aka kashe shi a rana irin ta yau. Muna mika ta’aziyyarmu da dokashin musulmi kan wannan rashin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 625 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Satumba-1389M. Daular Usmania ta sami nasararta ta farko a kokarin da ta yin a fadada ikonta a kasashen turai inda ta mamaye kasar Sabia a yankin Balkan. Duk kokarin da sabiyawa suka yin a kubuta daga hannun daular Usmania sun kasa samun nasara. Wannan halin ya ci gaba har zuwa tsawon karnuka 5, wato zuwa karshen karni na 19 M. a lokacinda sabiyar da hada kai da Rasha suke kori daular Usmania daga yankin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 55 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Satumban-1960M. Aka kafa kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta OPEC tare da sanya hannu na kasashen 5, kasashen dun hada da Iran, Saudia, Kuwait, Iraqi da kuma Venezuela. Kafin haka dai kamfanin kasashen yamma ne suke cin kerensu ba babbaka a fagen haka da saida man a duniya, wadan nan kamfanoni ne suke ayyana farashin man fetur kamar yadda suka ga dama. Amma da shigowar OPEC musamman bayan da wasu kasashen kamar Libya, Nigeria, Gabon, Qatar, Indonasia, Ekwado da kuma hadaddiyar daular larabwa suka shiga kungiyar Opec ta yi tasiri a cikin harkokin nkasuwancin man fetur a duniya. Harma a lokacinda kasashen larabawa suka haramtawa HKI da kasashen yamma sayan mai a wajensu sanadiyar yakin da suke yi da kasar Masar wannan ya sanya farashin mai ya ninninka.

======================================================

Yau Talata 24-Shahrivar-1394H.SH=01-Zulhajji-1436H.K.=15-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1434 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Zulhajji-02H.K. Aka kulla aure mai albarki tsakanin Fatima Azzahra (a) diyar manzon Al..(s) da kuma Aliyu dan Abitalib. Kafin haka dai wasu sahabban manzon Alll(s) sun gabatar da kansu don aurenta, amma manzon Al..(s) yakan cewa masu aure diyata Zahra yana hannun Al..(t). Amma bayan da Imam Aliyu dan abitalib (a) ya gabatar da kansa, manzon All(s) ya nemi yardarta sannan ya kulla aure a tsakaninsi. Rayuwar Fatima da Ali(a) ta zama rayuwar masili ga dukkan al-ummar musulmi don irin tsarkin da suke da shi. Albarkanin wannan auren ne aka haifi manya manyan jagoririn wannan al-umma wato Imam Hassan da Husain (a) da kuma zainab jarumar Karbala.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 850 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Zulhajji-586H.K. Aka haifi Ibn Abil Hadid, babban malamin tarihi kuma mawaki a garin Mada’in na kasar Iraqi. Cikekken sunansa shi ne Abu Hamid Abdulhamid bin Muhammad Mada’ini, amma an fi saninsa Ibn Abilhadid Mutazili. Sharhin littafin Nahjul Balaga wanda ibn abil hadid yay i ya nuna irin yadda yake kaunar Amirul muminina Aliyu dan Abitaliba (a). Littafin yana dauke da sharhin khudobobi, wasiki da kuma kalaman amirulmuminina Aliyu bin Abitalib wanda sayyeed Radi ya tattarasu a cikin Nahjul Balaga. Sharhin nasa yana da mujalladai goma kuma ya zama littafi mai muhummanci ga malaman tarihi tun lokacinda ya rubuta shi. Abul Hadid ya rasu a shekara ta 656H.K. a birnin Bagdaza yana dan shekara 70 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 194 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Satumban-1821M. Kasashen tsakiyar Amurka da dama sun sami encin kansu daga hannun turawan Espania. Tun cikin karshen karni na 15 miladiyya ne turawan Espania suka mamaye kasashen tsakiyar Amurka da dama, amma bayan rikicin cikin gida da ke aukuwa a kasar Ta Espania wadan nan kasashe sun shelanta samun encin kai daga kasar ta Espania a shekara ta 1821M. Kasashen dai sun hada da Nicaragua, Elsalvador, Costorica, Hundurus da kuma Gwatamala. Bayan samun encin kai da shekaru 2 wadanda kasashe sun hadewa kasar Mexico babba . Sai dai zuwa shekara 1829 tarayyar ta wargaje wanda ya kai ga ko wace kasa ta kafa gwamnatin kanta.

=================================================================.

Yau Laraba 25-Shahrivar-1394H.SH=02-Zulhajji-1436H.K.=16-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 84 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Satumba-1931M. Turawan Italia yan mulkin mallaka sun rataya Umar Mukhtar shugaban mutanen kasar Libya masu gwagwarmaya ta mamayar turawan na Italia.

An haifi Umar Mukhar a shekara ta 1959M, a shekara ta 1995 ya je kasar Sudan don tallafawa mutanen kasar kan Turawan Ingila da suke kokarin mamayarta, bayan da turawan suka sami nasara a kansu ya dawo kasar Libya. Sai kuma a shekara 1911M turawan Italia suka shiga yaki da sojojin daular Usmania kan mallakar kasar Libya, bayan shan kayen da sojojin daular Usmaniya suka yi Umar Mukhtar ya tattara mutanen kasar Libya don hana turawan mamayar kasarsu. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekaru 21 a lokacinda turawan suka yi amfani da manya manyan makamai suka yiwa Umur da dakarunsa kawanya suka kuma kamashi. Bayan wani lokaci sun rataya shi a gaban mutanensa a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-shahrivar-1357H.SH. Wata girgizar kasa mai karfin ma’aunin Richter 7.7 ta aukawa yankin Tabas da ke arewa maso gabacin kasar Iran kuma yay i sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 25 a garin da kuma gewayensa. Gizrgizar ta auku ne a dai dai lokacinda juyin juya halin Musulunci a nan kasar Iran ya kusan kaiwa ga nasara gwamnatin sarki sha ta so tayi amfani da wannan damar don maida mutane baya kan fada da zaluncinsa. Amma imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a kasar Iraqi a lokacin ya aike da sako inda ya bukaci a taimakawa mutanen Tabas a kuma hankali da farfagandar sarakunan kasar kan wannan batun.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Satumba-1982M. Sojojin HKI tare da yan korensu a kasar Lebanon sun yi kisan kiyashi wa Palasdinawa 3300 yan gudun hijira a sansanoninsu da ke Sabra da Shatila. Kafin haka dai yahudawan sun mamaye kasar Lebanon a cikin watan Yuni na wancan shekarar suka kore dakarun kungiyar PLO na Palasdinawa daga kasar sannan suka yiwa wadan nan sansanonin yan gudun hijira kawanya na wani lokaci, daga baya tare da mayakan Falanja na kiristocin kasar Lebanon suka dauki sa’oee 40 suka kashe Palasdinawa a wadan nan sansanoni. Duk da cewa kisan ya daga hankalin kasashen duniya amma kuma ba wanda yayi ko All..wade da su.

=============================================.

Yau Alhamis 26-Shahrivar-1394H.SH=03-Zulhajji-1436H.K.=17-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 54 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Satumba-1961M. Hukumomin soje a kasar turkiyya sun rataya tsohon Priministan kasar Adnan Mundaris. An haife Mundaris a shekara ta 1899M. Ya yi karatun jami’a a kasar ta Turkiyya ya karbi digiri na farko a fannin sharia. Mundaris ya kafa jam’iyyar democradiyya ta turkiyya a shekara 1946. A shekara ta 1950 jam’iyyarsa ta lashe zabe ya zama Priministan kasar, sannan ya sake zama Priminista a zagaye na biyu bayan jam’iyyarsa ta sake lashe zabe a shekara ta 1954. A karo na ukku ya sake zama Priminista a shekara ta 1957M. amma masu adawa da siyasarsa musamman daliban jami’a sun tada kayan baya wanda ya kai ga juyin mulki a shekara 1960 da kuma gurfanar da shi a gaban kotu wacce ta yanke masa hukuncin kisa aka kuma zartar da shi a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Shahrivar-1959H.SH . Shugaban kasar Iraqi na lokacin Sadam Husain ya yaga takardun yerjejeniyar sulhu ta raba kan iyakokin kasashen Iran da Iraqi a shekara ta 1975M, wacce ake kira yerjejeniyar Algies. Sadam ya dau wannan matakin ne don bawa kansa damar fadawa jaririyar jumhuriyar Musulunci ta Iran. Bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci karkashin jagorancin Imam Khomaini (q) kasashen yamma musamman Amurka sun bi dukkan hanyoyi na kifar da jaririyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran amma sun kasa daga karshe sun ingiza sadam Husain wanda ya mamaye wane bangare na kasar Iran don cimma manufodin wadan nan kasashe. Amma musulman kasar Iran sun kare kasar har zuwa karshen yakin na shekaru 8 a shekara 1988M. ba tare da sun cimma burinsu ba.

==========================================================.

Yau Jumma’a 27-Shahrivar-1394H.SH=04-Zulhajji-1436H.K.=18-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 197 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Satumba-1818M. Kasar Cheele a nahiyar kudancin Amurka ta sami encin kai daga hannun turawan Espania. Turawan sun mamye kasar Cheele ne a shekara ta 1536M. Mutane kasar sun fara gwagwarmayan samun encin kai ne tun shekara ta 1814M. Sai kuma a shekara ta 1817M Madugu gwagwarmaya da turawan Espania a kasar Agentina Khuzeson Martine ya farwa sojojin Espania da suke mamaye da kasashen Peru da kuma Cheele, tare da taimakon masu kishin kasa na kasar Cheele sun sami nasara tilastawa Espaniyawa bada encin kaiwa kasar Cheele a shekara 1818M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 54 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Satumban-1961M. Dag Hammarsk-Jold dan babban sakataren majalisar dinkin duniya na biyu yam utu sanadiyyar faduwar jirdinsa a cikin kasar Congo. An haifi Dag a shekara 1905M a kasar Sweden. Ya karantar a jami’ar stolkhom na wani lokaci sannan ya rike kujerar mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sweden na wani lokaci. A shekara ta 1953 M ya zama babban sakataren MDD na biyu, sannan an sake zabensa a kan wannan mukamin a karo na biyu a shekara 1957M. Dag ya taimakawa wajen mayarwa kasar masar mashigar Swiz sannan ya tura sojojin MDD zuwa congo don dawo da zaman lafiya a can. Sai dai a ranar 18-Satumban shekara ta 1961 yan tawayen kasar ta Congo karkashin jagorancin Musa choombeh sun kakkabo jirginsa wanda ya kai ga mutuwarsa a faduwarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Shahrivar-1367H.SH. Sayyeed Mohammad Husain Bahjat Tabrizi, mawakin juyin juya halin Musulunci a nan Iran, wanda aka fi saninsa Shahriyor ya rasu. An haife shi a shekara ta 1285H.SH a garin Tabriz. Ustaz Shahriyor ya shahara da wakokin yabon Manzon Al…(s) da iyalan gidansa kafin nasara juyin Musulunci a nan Iran . Bayan nasarar juyi kuma Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bashi lambar girmamawa kan wakokinsa na goyon bayan juyin Musulunci. Ustaz shahriyor ya rasu a rana irin ta yau a shekara ta 1367H.SH yana dan shekara 82 a duniya. Ranar rasuwarsa a nan Iran ita ce ranar mawaka.

===============================================================.

Yau Asabar 28-Shahrivar-1394H.SH=05-Zulhajji-1436H.K.=19-Satumba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 57 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Satumban-1958M. Aka kafa gwamnatin entacciyar kasar Algeria ta farko. Kafin haka dai mako gwagwarmayar neman encinwa kasar sun fara yunkurin entar da kasar ne a shekara ta 1954M. Wannan gwagwarmayan ta ci gaba har zuwa lokacinda sojojin turawan Faransa yan mulkin mallaka suka kasa murkushe masu neman encin kasar wanda ya kai ga kafa gwamnatin entaccen kasar Algeria a ranar 19-Satumba-1958M. Amma gwagwarmaya bata kare ba sai a ranar 5-Yunin-1962M a lokacinda Faransa ta tabbatar da samun encin kasar.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Satumban-1979M. Hafizullah Amin ya jagorancin wani juyin mulki a kasar Afganistan wanda ya kai ga zubar da jinni da kuma kisan shugaban kasar na lokacin Noor Mohammad taraki. An haifi Taraki a shekara ta 1913 a garin Gazne na kasar Afganistan, yah au kan kujerar shugabancin kasar ne baya

Add comment


Security code
Refresh