An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 15 April 2008 17:59

Ma'aikatanmu

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

A halin da ake ciki dai Sashin Hausa na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana da ma'aikata guda goma shauku (13),goma daga cikinsu daga nahiyarmu ta Afirka (Nijeriya da Nijar) sai kuma uku daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wato mai dauka mana shirye-shirye da kuma masu kula da masu saurare biyu.

Don haka ga sunayensu da kuma takaitaccen bayani kan kowane guda daga cikinsu:

Tidjani Malam Lawali Damagaramdai an haife shi ne abirnin Zinderna jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, kuma ya kama aiki ne da wannan gidan radio a shekara ta 1999. A halin yanzu shi ne Shugaban wannanSashe na Hausa na Gidan Radion Iran, kuma shi ke gabatar da shirin 'Hannunka Mai Sanda'da shirin na musammanbugu da kari kan sa ido kan dukkannin ayyukan da ake gudanarwa a sashen kuma shi ne babban Editan shirye-shiryen.

Abdullahi Salihu: an haife shi ne a birnin Katsina, Jahar Katsina a Tarayyar Nijeriya.Ya fara aiki da Sashen Hausa Na Muryar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a cikin shekara ta 2003.Yana gabatar da Labaran Duniya da sharhin bayansu da yin Hirarraki,da kuma gabatar da shirin Don masu Saurare da Mu Koyi Harshen Farisanci.Bugu da kari yana sanya labarai da sharhinsu da da shirin da ya ke gabatarwa a shafinmu na Internet. Daga karshe Edita ne na Shirye-shiryen da muke gabatarwa.

Mujtaba Adam:An an haife shi ne a birnin Kano na Tarayyar Nijeria,kuma ya kama aiki ne da Sashen Haysa na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1998.Yana gabatar da "Labaran Duniya" da kuma "Sharhin Bayan Labarai'.Sai kuma shirin v'Mu Leka Mu Gani'.Haka nan kuma yana karanta "jaridu"Bugu da kari yana tuntubar masu aiko mana da rahoto da kuma gabata da hirarrakin da muke yi da mutane. Daga karshe shi Edita ne na shirye-shiryen da muke gabatarwa.

Muhammad Awwal Bauchi: An haife shi ne a garin Bauchi na Tarayyar Nijeria,kuma ya kama aiki ne da Sashen Hausa na Uryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1998.Shi ne yake gabatar da shirye-shiryen 'Iran A Mako', da kumaq 'Matambayi Ba Ya Bata' ba ya ga labaran duniya da kuma sharhinsu yana tuntubar masu aiko mana da rahoto da kuma gabatar da hirarrakin da muke yi da mutane. Da sanya labaran duniya da sharhin bayan labarai da shirye-shiryen da yake gabatarwa a shafinmu Internet.

Abdulkarim Ibrahim: An haife shi ne garin shikal na karamar Hukumar Mulkin Filinque na Jahar Tillabery a Jamhuriyar Nijar.Ya fara aiki da sashen Hausa Na Muryar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a matsayin mai aiko da rahoto daga birnin yamai na Jamhuriyar Nijar a cikin shekara ta 2002 A wannan shekara ta 2008 ne ya soma aiki da Muryar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a matsayin cikakken ma'aikaci.Kafin haka ya yi aiki da gidan Radiyo da Telbijin na Tenere da kuma na Duniya dukkansua birnin Yamai na Jamhuriyar Niger.

Umar Abubakar Kumo: An haife shi ne a garin kumo da ke jihar gombea Tarayyar Nijeriya.Ya fara aiki da Sashen Hausa na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara 2007. Bayan ya yi karatu a Jami'ar Al-Mustapha da k birnin Qum a nan kasar Iran inda ya sami digiri a fannin Nazarin Addinin Musulunci;Umar kumo shi ne ya ke gabatar da shirin 'Hakkokin Dan Adam A Mahangar Musulunci' tare da fassara da karanta Labaran Duniya da Sharhin Bayan Labarai.

Sunusi Inuwa Wunti dai an haife shi ne a garin Bauchi na Tarayyar Nijeriya, kuma ya kama aiki ne da wannan gidan radio a shekara ta 2003. Shi ne yake gabatar da shirin 'Tarihin Iyalan Gidan Manzo'. Har ila yau kuma yana karanta 'Labaran Duniya' da kuma 'Karanta Jaridu', bugu da kari kan tuntuban masu aiko mana da rahoto da kuma gabatar da hirarrakin da muke yi da mutane.

Tahir Amin Yoladai an haife shi ne a garinYola na Tarayyar Nijeriya, kuma ya kama aiki ne da wannan gidan radio a shekara ta 2009. Kuma dama ya taba aiki da gidan RadiyonHausatsakanin shekara ta 1999 zuwa 2003.Shi ne yake gabatar da shirin Ko Kusan. Har ila yau kuma yana karanta 'Labaran Duniya' da kuma 'Karanta Jaridu', bugu da kari kan tuntubar masu aiko mana da rahoto da kuma gabatar da hirarrakin da muke yi da mutane.Kuma yana sanya Labarai da sharhinsu da shirinsa na Kokunsa a Shafinmu na Internet.

Muhammad Aminu Ibrahim dai an haife shi ne a garin Kiyawa na jihar Jigawa a Nijeriya, kuma ya kama aiki ne da wannan gidan radio a shekara ta 2003. Shi ne yake gabatar da shirin Kukan Kurciya Jawabi ne da Shirin Fatawowi'. Har ila yau kuma yana karanta 'Labaran Duniya' da kuma 'Karanta Jaridu', bugu da kari kan tuntubar masu aiko mana da rahoto da kuma gabatar da hirarrakin da muke yi da mutane.Da sanya labarai da Sharhinsu da shirye-shiryen da yake gabatarwa a cikin Shafinmu Na Internet.

Halima Yakuba: An haife ta ne a birnin yamai na Jamhuriyar Niger tana da aure da 'Da guda kuma ta zo kasar Iran a shekara ta 2002 inda bayan koyan harshen Farisanci a garin Qazwin ta ci gaba da karatu da harshen Farisanci a Jmi'ar Az-zahra da ke birnin Tehran na Iran.A shekara ta 2005 ne ta fara aiki da gidan Radiyo Hausa na iran inda take fassara jajidun Iran zuwa Hausa da daukar rahotonni da hirarraki da gabatar da shirye-shiryen da muke watsawa.

Malama Tala Sabouri : An haife ta ne a garin shiraz Na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara ta 1975 kuma kammala karatunta na digiri a harshen Hausa a Jami'ar Musulunci ta Azad a birnin Tehran.Bayan haka ta fara aiki da Radiyo Hausa na iran a shekara ta 2001 a matsayin mai fassara daga Hausa zuwa Farisanci kuma a halin yanzu ita ce ke kula da fassara duk wasikar da masu sauraremu suka aiko mana da kuma jera lambobin wayarsu da adreshinsu na E-Mel a cikin kamfuta.Ta kasance mai matukar son harshen Hausa kuma fatarta wata rana ta kai ziyara a kasar Hausa don kara kusantar Hausawa da Al'adunsu.

Malama Najme Quddusiyan : An haife ta ne a birnin Tehran na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara ta 1981.Ta fara aiki da Gidan Radiyon Hausa na Iran a shekara ta 2004 a matsayin mai Fassara daga Hausa zuwa Farisanci kuma a halin yanzu ita ce ke kula da sa sunayen masu sauraremu a cikin kamfuta da adreshinsu,ta kuma aika musu da kyaututtukan da suka sauwaka da Gidan Radiyo ke aikewa masu saurare.Tun tana karama take da zurfin kaunar al'ummar Afrika saboda ta ce tana farin ciki mai yawa da kasancewa a tsakiyar Hausawa tana aiki da su da fatar za ta iya taimakawa ko da dai da kwayar zarra wajen yada addinin musulunci da faranta wa masu sauraren gidan Radiyo Hausa Rai.

Malama Nassim Julaei: An haife ta 1981 a birnin Tehran a Jamhuriyar Musulunci ta iran.Yanzu haka malama Jula'i ta mallaki takardar digirin farko a harshen Hausa a Jami'ar Musulunci ta Azad da ke Tehran.Ta fara aiki da Sashen Hausa na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara ta 2007 a matsayin mai daukar sautin shirye-shirye na sashen.Malama Joulaie tana da sha'awar zane zane kuma ta yi fice a wannan fanni.

Add comment


Security code
Refresh